Sashe 263
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"salemat ina cikina? "ina baby'nah dana barki dashi ? "ina abinda kika haifa min? "tashi muje a yau zan sake dangana kaina ga mahaifinki a karo na biyu domin yabani aurenki dan muddin ina raye kece abokiyar rayuwata bazan iya rayuwa da kowa ce irin mace ba matukar bake bace .. yatashi daga zaunen dayake akan gadon tare da janyo hannuta ya soma tafiya da ita yana mata magana sunyi taku d'aya zuwa biyu kenan sukaji shemah ta buga wani irin salati me karfi tare da fashewa da wani matsananci kuka me k'arfi wani irin tafasa zuciyarta take tamkar ana diga mata ruwan dalma, akirjinta kuma tamkar zai faso waje saboda tsananin tashin hankali.... .. da kishin daya turnuketa, ta dubeshi tana hawaye tace "Mahbub ni kuma ina makomar aurena da kai? "mekake tunani akaina? wani irin kallo Taufeek yake binta dashi me cike da tsantsar mamaki da tashin hanki sannan ya nunata da yatsan hannusa "ke kuma daga ina? "aure fa kikace waye mijin naki anan ? "a ina nasanki da har kike min wasu zantuttuka wand'anda kwakwalwa bazasu iya dauka ba? bansaki ba bansan daga inda kike ba asalima yau ce rana ta farko dana soma ganinki a rayuwata .... cikin rawar murya tace " nasani nasani Mahbub bazaka tuna koni wacece gareka ba sannan bazaka ta'ba sanina ba da matsayina a gurinka ba," tunda kayi lossing memory dinka na tsawon shekaru masu yawa da suka gabata amman kasani ni matarka ce ta suna da igiyoyin aurenka uku rassss suka rataya akaina," sannan muka rayu tsawon shekaru tare ,tsawon shekarun da mukayi rayuwa da kai na kasance ina maka wani irin so da uwa kad'ai takema d'anta, kullun kuma ina maka fatan samun lafiya domin sanin wani abu daya danganceka da danginka "sanadin yayana kasamu garkuwa cigaba da rayuwa a doro duniya yayana shine silar komai daka zama a yaxxu... " yayana yayi wahala da kai daga kasar haihuwarka har zuwa wata kasar daban batare da yasan ko kai waye ba." ya inganta rayuwaka alokacin da kai kanka bakasan halin dakake ciki ba ,amman dan yanzu ka dawo haiyacinka shine zaka manta dani... cikin abinda bai fi second biyu ba gumi ya rufe shi ya dimauce cikin karfin hali irin nashi ya bude baki yana son furta kalma koda guda daya ce gareta amman ya kasa bayaga girgiza kanshi daya dinga yi yana kallonta da Ammi dake tsaye akansu tana kallonsu cike da matsanancin tausayawa dan tasan wani tashin hankalin ke kokarin sake kunowa cikin rayuwar d'an uwata.. .... shemah takaraso inda Ammi ke tsaye tare da kamo hannuta cikin nata tana zubda hawaye "hakika nasan yayana yayi kuskure arayuwarsa, kuskurensa kuwa shine amincewa da yayi ya aura min d'an uwanki alhalin yasan yana cikin dimuwar, da watan wata rana zai iya dawowa haiyacinsa wanda gashi hakan yakasance , a yau abubuwa masu radadi da ciwo suna kokarin dawowa cikin rayuwata ciki kuwa har da ciwon zuwan wannan ranar da mahbub d'ina zai tabbatar min da bai sani ba kosanin aurensa dake kaina ba. Ammi ta rike hannunta sosai cikin nata jikinta na kirrrrma "ki daina kuka haka ni kaina na tabbatar da ke din matarsa ce duba ga yanayinku a lokacin da bai dawo hankalinsa ba "dole nayi kuka saboda nasoma hango karshen zamana dashi duk da bazan so rabuwa da abinda na rayu dashi sama da wasu shekaru ba. "mun rayu tare da mahbub , mahbub mutun ne me fara'a dasanin darajar d'an adam sannan kullun muna tare dashi sai dai idan baya k'asar, komai tare mukeyi matsawar muna guri d'aya bamu tabayin nisa kmr irin yadda muke a yanzu ba, "yau ace mun haihuwa dashi nasan ko yaranmu ya kalla wannan kawai ya isa ya tabbatar masa da matsayina agurinsa. A sanyaye Ammi ta katseta "karkice haka ki ma daina wad'an nan zantuttuka yadda kukayi mu'alamarku kad'ai zai sa ya iya kankarewa ba.. amman zance aurenki dake kansa yana nan har yanzu kina nan amatsayin matarsa .. take yaji zuciyarsa ta tsaya cak gaba d'aya ta daina bugawa na wani lokacin sannan ahankali tacigaba da bugawa da karfi maganganunta ba iya kunnensa kad'ai ya tsaya ba har cikin zuciyarsa yake jin komai yasoma karasowa gareta yana son ta karyata abinda tace yazama karya ne ba gaskiya ba, "wani irin aure kuma? tun kafin yakarasa gareta Ammi ta dakatar dashi ta hanyar cewa "ka tsaya ko kasamu guri ka zauna zance aurenka da ita gaskiya ne tabbas babu k'arya takarasa maganar tana maida idanunta kan shema " zanso naji yadda akayi kuka tsinci d'anuwana da kuma irin taimakon da kukayi masa.. tunda Ammi ta tsai dashi yake aikawa shemah wani irin Kallon me tattare da alajabi yayinda har lokacin hannunsa ke cikin na Umman su'ad wace ke tsaye sai kifkifta idanunwa take da sake zurfafa tunanin rayuwarta da tarin soyayyarsa gareta," bazantar da rayuwata datayi Sanadinsa iyayenta danginta tana wassafa ina ma komai dake faruwa a halin yanzu karya kunnuwanta suke jiyo mata ba gaskiya bane.." Taufeek d'inta bai da auren kowace mace akansa zasuyi rayuwarsu daga ita sai shi.. yadda Salema ke zurfafa tunaninta haka itama shemah ke tunani, sai dai nata tunanin yasha banban da wanda salema take har zuwa sanda ta matso kusa dashi suna fuskantar junansu. "ka daina tantama ko jin mamaki abinda nace ni din nan matarka ce mahbub tacigaba da kallonsa tana zurfafa tunanin gidanta da rayuwar da sukayi ina ma ace wannan abun daya faru tazo ta tafi ne da yanzu duk tsiya suna tare kwance guri daya ko zaune suna hira da mijinta ma'aboci zolaya da kokarin danne fushinsa. take ta fara tariyo rayuwarsu dasukayi a baya da dalilin haduwarsu.... *asalin faruwar lamari* mu asalin yan kasar Nigeria ne kasancewar mahaifinmu haifafen Nigeria ne, mahaifiyarmu ce haifaffiyar k'asar koria gaba da baya. karatu ne ya kawo mahaifinmu engening Nura kasar koria har Allah ya had'ashi da mahaifiyarmu me suna polina, polina ita ce d'iya ta uku gurin iyayenta wanda tunda ga kanta iyayenta suka tsaida haihuwa atsarinsu yara uku sun isheshesu rayuwa. A loakinci polina ce tasoma nunawa mahaifinmu soyayya ta fitar hankali saboda a kallon farkon data soma yi masa taji Allah ya dauki soyayarsa yasaka mata cikin zuciyarta ,ta yadda take jin bazata iya hakura dashi ba , batayi sanya a gwiwa ba gurin sanar masa inda shi kuma yaki amincewa da hakan ,ya nuna mata bazai iya soyayya da itaba saboda addini da aladarsu ba daya ba. "ta bishi tayi magiyar duniya da salon jan hankali amman yaki yarda saboda hudubar mahaifinsa garesa domin kafin yazo kasar koria karatu da kyar mahaifinsa ya yarda har sai dayayi masa alkwarin bazai saurari kowace yarinya ba abinda ya kai shi zaiyi ya dawo kasar . wannan rashin amincewarsa yasa tashiga tashin hankali daga karshe ta yanke shawarar gaya masa ta hak'ura da soyayyar su zama Friend kawai nan ma yaki yarda haka ta dinga yi masa naci, dan wannan alakar abotaka tayi amfani da matantakanta, kafin zuwa wani lokaci soyayya me karfi tashiga tsakaninsu wanda idan d'aya bai ga d'aya ba babu kwanciyar hankali ,bayan wasu lokuta sukayi nasarar yin aure bayan wahalun da suka sha kafin su samu mallakar junansu domin lokacin da mahaifinmu ya zowa iyayensa da batun auren polina kin yarda sukayi daga karshe suka hanashi komawa kasar koria gaba d'aya wanda sanadin haka mahaifiyarmu tabiyosa kasar haihuwarsa inda ta nunawa iyayensa shi take so kuma duk abinda suke so zatayi ko cewa sukayi ta zauna kasar Nigeria matukar zasu amince da aurensu zata muslinta ta zauna da kyar dai da taimakon wasu daga cikin manya a dangi ,da mahaifinmu ya shawo kansu aka muslintar da mahaifiyarmu inda ta amshi sunan muslinci da khadija sukacigaba da rayuwarsu a can a nigeria a wani bangare daga cikin gidan. bayan wani lokacin khadija tasamu ciki tashi kwance babu wuya agurin Allah har Allah ya sauketa lafiya tasamu haihuwar d'a namiji tunda ta haifi yaron, ta hana kowa daga cikin dangin d'aukarsa har mahaifiyar babamu daga babanmu sai ita ke d'aukar baby, duk me son ganin baby sai dai ya iskoshi cikin dan karamin gadonsa ya gansa daga nesa amman bazai ta'ba baby ba,har ranar suna inda yaro yaci sunan kakanmu wato salis tunda polina ta haihu mahaifinmu ya d'auki son duniya ya daurawa polina da danta ganin haka yasa ta dinga bashi shawarar su gudu su bar kasar batare da sanin kowa ba, bayan suna da wasu watanni aka wayi gari eng Nura sun gudu tare da khadija da baby'nsu . d'angi sun shiga tashin hankali matuka daga baya suka rakasu da addua ,komawarsu koria babu dadewa Allah yayiwa Salis rasuwa lokacin yana da wata 6 duniya dan har yasoma takawa,babu rashin lafiya babu komai kwana ne dai ya kare mahaifina yaji mutuwar sosai dan ba'a ta'ba masa mutuwa ba arayuwarsa kowa nashi na nan a raye haka khadija har tafishi shiga tashin hankali sai ta dinga tunani ko dan ta haifeshi a nigeria ne yasa tarashi, tundaga lokacin taci alwashin ita da kasar har abada haka ma duk abinda zata haifa masa bazasu taka kasar ba hatta shi kansa mahaifinmu bazata sake kuskuren barinsa zuwa kasar Nigeria ba ,suka cigaba rayuwarsu cikin so da kauna da kulawa. bayan haihuwar Salis iyayenmu sun dade basu samu haihuwa ba kafin daga baya suka samu haihuwar yayana Habib alokacin mahaifinmu yasamu cigaba sosai akowani bangare na rayuwarsa dan bai tsaya iya aikinsa kadai ba har da harkokin kasuwanci zuwa kasashen duniya yana yi, shekarunsu biyar dasamun haihuwar habib suka sake samu haihuwata kuma har lokacin maihaifiyarmu bata tunanin sake zuwa kasar mahaifinmu sakamakon wannan tsoron d'an kar arabata damu . shi kansa mahaifinmu da taimakon kasuwancisa yake samun damar zuwa kasar haihuwarsa yaga iyayensa batare da saninta ba ,mun taso cikin gata da kulawa iyaye sosai takowane bangare iyayenmu naji damu duk abinda muke so shi mukeyi mahaifinmu ya shahara sosai a kashen duniya dan bayan gwagwarmayar rayuwa data aikin gwanati har ma da rike mukamai nasiyarsa kasar yayi da taimakon mahaifiyarmu. " ina matakin jamia Allah yayiwa iyayenmu rasuwa sakamakon hatsarin mota da sukayi ta hanyar dawowarsu daga office din jakadanci "acewar mutane an kwance musu birkin mota ne . mutuwan ta gigitamu kwarai da gaske muyi