Sashe 18
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
da batasan ciwon kanta ba, wacce batasan abinda zata fitar daga cikin bakinta ba ina son kisaka aranki ni ne nan zanga bayanki, bakiyi kuka ba tukun, Ki Ta nadi hawayenki. ko zuwa gaba zasuyi miki amfani. da ikon Allah sai ka hadu da maseefa wace tafi wanda nike ciki, sai wani mummunar abu ya sameka da ikon Allah tare da ke Zeey ya katseta yana busa mata iska cikin kunneta, sbd a yanzu ina tabbatar miki duk inda zaki ina biye dake ,matsawar baki bani hadi kai ba ,ke ko aure kikayi bazan barki ba sai adabi rayuwarki, ai tunda kika nuna baki sona, kika hadu da ciwon hawan jini da ulcer zan tabbatar miki ni akil baa min hk babu macen Data isa........ zan zame miki kaska rabi me jini ba dai ke kince karamar k... Tun bai karasa abinda zai fada ba tayi saurin hangin din kiran Tana kuka what I may going do..? Ta tmbyi kanta.. yakamata nasamowa kaina mafuta tun lokaci bai kure min ba. Ta dade zaune ahaka sai dataci kukanta takoshi sannan Ta shirya takira AK byn ya dauka take tmbyrsa abinda zaa girka masa. Ki dafa min any soft food Amman fita zanyi yanzu Ki hanzarta yana gama fadar hk ya kashe wayar. Zeey tana tsaye a kitchen Tana hadawa AK breakfast tajiyo sautin muryarsa yashigo parlour'n ammi suna gaisawa da ammi . yace mata fita zai Yi kan isue karatunsa . ammi ta hade ranta tamau kana tace zauna akwai mgn me mahimmamci da zamuyi kafin fitarka Ta fadi hk Tana nuna masa kujera zama da yatsunta. Jikinsa a sanyaye ya zauna yana fuskantar mahaifiyarsa take km yaki gabansa na faduwa sai Data numfasa tace kana jina? Ak ya jinjina mata kai alamun yana jinta. abdulkabir takirasa sunansa ya sake tattara hankalinsa da natsuwarsa gateta. ammi tacigaba Kabar shirin komawarka kasar Spain ana zaka cigaba da karantunka... Dammmm gabansa ya fadi A dan tsorace bai san sanda yace ammi akan ME byn komai nawa ya kusan kammala. Akan na isa da kai na isa na hanaka Abu km ka hanu. , dan hk matsawar kana son cigaba da karatunka sai dai kayi anan period ....Meyasa ammi zaki min hk? wallahi muddin kika hanani tafiyar nan kin rusa min gabadaya budget dina. Allah yasa duniyarka na rusa ba budget ba ana zaka cigaba ana tausayinka bakajin tausayin kanka . kama sawa ranka cewar nagama rusa komai.. abinda nike so agidan shi zaa Yi ,yau din nan kaje ka tsaida komai kasoma neman gurbi anan cikin Luthe . Kwantar da kai yayi sosai tare da , marairaicewa yayi fuskarsa tausayi yace Dan girman Allah kiyi hakuri kibarni kimin addua. Bafa zan yarda ba abdulkabir idan kai bakason rayuwarka ni tana da mahimanci gareni, idan wani abu ya same yakake son nayi takarasa mgnr kmr zatayi kuka. ..... Ya sake tausasa muryarsa cike da shagwaba yace ammi please karki min hk wlh akwai ab.....bafa zan yarda da tafiyarka wata kasa ba ammi ta sake katseshi tana juyar da kanta gefe. ok kawai ya iya cewa bai sake cewa daita kala ba yana me mikewa tsaye ranshi a matukar bace ya juya takira sunsnsa ya juyo ahankali fuskarsa babu yabo babu falsa breakfast din fa? Fuskasta a daure yace Bana ci ya sake juyawa tasan ranshi ne yabaci shiyasa. itama bata sake cewa dashi komai ba har yabar part din tunda tasamu ya amince zai Yi karatunsa anan ai shikenan.. Burinta yacika. Zeey wace ke kitchen datagama sausaron duk abinda ya faru tsakanin uwa da danta ta fito da sauri Amman ina har yabar part din . Batama kula da ammi ba, hanyar kofar fita ta nufa da hanzarinta ta fito daga bangaren ammi saukowa kasa tayi da sauri sai dai baya kasa fitowa harabar gidan tayi nan ma batagansa ba batamaga alamar motarsa ba . jikinta a matukar sanyaye ta Kalli inda aka tanada domin ajiye motaci.tana kallo. ta dade tsaye agurin tana tunani Aranta. sannan Ta juya ahankali . cikin mutuwar jiki takoma ciki iman wacce dawowarta Kennan daga part din dady tana zaune hannuta rike da plastic cup da spoon tana yuya tea dinta Data hado Ta dan saci kallonta kana tace aunty wai meke damunki tsakanin jiya da yau duk ahargitse nike ganinki ? Zeey Ta juyo inda iman take zaune tana fuskantar iman da kyau tare da yin murmushin yake Kawai tace babu komai sisina na gode da kulawarki gareni. tana takarasa mgnr muryarta cike da rauni ta nemi hanyar part dinsu ammi tace Zainab..... Juyowa tayi da sauri tare dawowa baya kadan ta Kalli ammi wace take daga zaune gefe tace zo nan diyata Ta yafutota da hannu. Zeey takarasa ga ammi .ammi ta kamo hannuwanta duka cikin nata ta zaunar daita gefenta, meke damunki diyata..? Karki boye min Nima tmkr mahaifiyarki ce duk abinda kedamunki kisanar min zan magance miki matsalarki da yarda Allah . Sharr... hawayen dake makale a kwarin idanunta suka samu nasarar zubowa uhmmmmm karki min kuka abinda ke damunki kawai na bukaci sani ba kuka ba. Zeey takasa tsaida hawayenta sannan takasa cewa komai gashi mgn take son Yi Amman tarasa me zata cewa ammi. ciki garenta ... Koko damuwarta na rashin nemanta da AK baiyi ba har yabar gidan..... ko soyayyar tilon danta dake neman haukatata da kokarin tarwatsa zuciyarta ... Tsawon lokaci suna a hk batare da kowannensu yayi yunkurin cewa komai ba . Sai ma Iman dake zaune can gefe tace Allah ammi akwai damuwa atattare da aunty Zeey tun jiya . yau fa da safe har kuka ta dinga yI acikin a bathroom .. Ammi ta tsareta da idanunta tana cewa hk ne zance iman .? Zeey ta girgiza kai sbd rashin sanin abinda zata ce. To meye dalilin kukanki , budar bakinta sai cewa tayi yaya ne naga gabadaya ya canza min ba kmr yadda muke da ba. Dan wanna shine zaki zauna cikin damuwa kmr bakisan hali abdulkabir ba? ai shi din tmkr hawainiya ne km karki sake saka kanki cikin damuwa . idan ya canza miki kema Ki canza masa domin idan yagane kina shiga damuwa akanshi akwai matsala sbd wata rana zaku kasance cikin inuwa daya, Dan hk ki dinga rike mutuncinki amatsayinki na diya mace me daraja. girgiza Kai Zeey tayi alamun taji . sai dai take zance ammi yashiga mata yawo cikin kwalkwaluwarta wata rana, zasu kasance inuwa daya to me hk yake nufi tun batayi zufi ba taji sautin muryar ammi. maza tashi kije Ki shiryo mana abinda kika dafa masa mu muci abinmu tunda shi wancan uban yan fushi yayi zuciya . Ammi abar masa zai dawo yaci. Ko yadawo nasan halin AK bazai ci ba ........ Hk ta mike jikinta a matukar sanyaye taje Ta shirya dining zaune suke gabadayansu har ita kowa nacin abinci Amman ban daita da takasa turawa cikinta komai tunani kawai take Ta yadda zata rabu da damuwarta.... Bayan Sun gama breakfast Zeey tashiga daki takira kawarta bolaji waCe suke kiranta da bj nurse ce Itama sosai ta mugun krewa aharakar abortion sbd asibitin data koyi aiki su aikin da sukeyi Kennan . byn bj ta dauki waya Zeey ta tmbyeta kota tana gida da Yaren yarbanci . Bj Ta bata amsa da mo'wale oremi sh'e kosi? Owa mofe riye fun e'n ko'ko MO bo'o nisi'sin injicewar Zeey tare da katse kiran. Tafi parlour tayiwa ammi sallama rataye da Jakarta Ta zuwa makaranta. ammi tace Allah yatsare a dawo lfy ki kula da kanki. takaraso gurin iman tare Ta ce mata Ni na wuce. iman tace sai kin dawo,yanzu gidan Zai Yi shr babu dadi idan baki nan shiyasa nima nike Allah Allah nazana jam wallahi suka Yi dariya atare ..karki damu ba Dadewa zanyi give 72 mints na dawo sing kawai zanyi.. Na Dai baki? 2 mint suka sake yin dariya sannan ta fito zuwa harabar gidan .. Zeey na barin gidan a madadin ta dauki hanyar yaba tac a'a kai tsaye hanyar bustop ta nufa taje tashiga motar me zuwa agege, cikin 15 ta sauka a daidai oniwaya jection kasancewar daga ikeja zuwa agege babu wani nisa da kafa MA idan mutun Yasa kanshi zai iya zuwa ..wani dan karamin lungu Ta shiga byn Ta wai waiga bataga idon sani ba . sbd kusa da area dinsu ne . Ahankali har Ta isa gidan datake Son zuwa zuciyarta na beating kada wani mugun ido yaganta ......... Mmn sudais SAI KA AURENI DOLE