← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 289

Sashe 118

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *Allah's messenger saw said fear Allah wherever you are* page 44 yaya yusif ne yayi nasarar cafko hannuna cikin nasa yana bani hkr cikin matsanancin tashin hankali. kiyi hkr saleemat ki yarda da kadara.. ki dauka wannan itace kaddararki ,baki isa ki goge kaddarar da Allah ya rubuto miki ba , baki ji abinda shi kansa masoyin naki ya gaya miki ba matsawar matarsa ce ke zai aureki . kiyi hkr dan girman allah kisamu natsuwa ki dawo cikin hankalinki ki dauki dangana kisawa zuciyarki . "idan so cuta ne hakuri magani ne. " ki taimakawa rayuwar yan'uwanki muna matsanancin sonki bama son mu rasaki arayuwa . mahimmanci kassncewarki cikin natsuwa yafiye mana komai dake cikin duniya . kece zuciyarmu salema gbdy soyayyarmu, mu tattara shi ne akanki "ke kadai Allah yabamu mace atsakaninmu idan muka rasaki zamu shiga damuwa da tashin hankali. ki kalli can.... ya nuna min inda mamma take tsaye tana zubda hawaye, duba kiga halin da mahaifiyarmu ke ciki ayanxu datake tsaye agabanki... damuwarki ce ta haifar da hk... duk maganganunsa shiga kunnuwa suke suna fita 1 byn 1. babu mgnrsa daya datayi tasiri cikin kunnuwana balle xuciyata ,sbd hankalina da natsuwata gbdy basa gangar jikina suna ga masoyina taufeek.... so nake nasake daura idanuna akansa ko zan ragewa kaina radadin da nake ji azuciyata akan rasashi da zanyi arayuwa .. amman yaya yusif ya rike hannuna gam ya hanani motsawa daga inda nake . ganin hk yasa nasaki wani irin ihu tare da fixge hannuna cikin nasa . ina kuka.... yasoma kokarin sake kamo hanuna, na goce da sauri muryarta na rawa nace karka sake yunkurin tabani kai ba yayana bane makiyanane gbdynku bakwasona tunda bakwa son farincikina .... kuna kallo an rabani da burin raina.... kuna kallo zan rasa taufeek ..amman kace kuna sona wannan wani irin so ne...? nakarasa gaban mahaifiyata dake tsaye har lokacin tana kuka na riko hannuta mamma kice suje suce taufeek ya dawo zaku bashi ni. kuce masa ya dawo kar ya tafi ya barni nasan ke uwace zaki fi kowa fahimta da fuskantar yadda nake ji azuciyata..... rashin taufeek .. daidai yake da rasa raina . zan mutu kowa ya huta rayuwata bata da wani amfani matsawar babu shi. ...... mamma kiyi wani abu kar na mutu akwai sirrika masu matukar mahimmanci atsakanina da taufeek.... shi din wani bangare ne na rayuwata ...... shine wanda zaifi kowa sanin darajata da kimata idan ya aureni.. narasa abu masu girma da mahimmanci a dalilinsa "matukar bashi na aura ba akwai matsala....duk ma wanda zaku bawa aurena wulakantani kawai zaiyi sbd narasa shi ainihin jigon auren....... na juyo afirgice ina kallon yan'uwana 1byn 1 daga wannan lokacin cikinku duk wanda bai tsaya min na samu cikar burin zuciyata ba zan kafashi cikin tarihi rayuwata sannan kada wanda ya sake cewa yana sona acikinku... gaddafi ne yayi karfin halin karasowa gareni tare da dafa kafadata yakira sunana salema. karkice hk dukkaninmu muna sonki muna son faricikinki sannan muna son aurenki da taufeek kassncewar kina sonshi amman abinda kike bukatar muyi miki yafi karfinmu sbd babu yadda zamuyi da hukuncin mahaifinmu gareki .... shawarata kiyi addua matsawar taufeek mijikin ne duk tsanani duk wuya zaki aureshi" idan km ba mijinki bane duk yadda kika so ki mutu akansa zaki rayu sannan bazaki aureshi ba. ada can bakisan zaki hadu dashi ba Allah ya hadaku dan hk kiyi hkr ki fawalawa Allah komai zamu tayaki da addua. ahankali na saki hannun mamma dake rike cikin nawa. nasoma yin kasa kasa ina wani irin kuka na fitar hankali . na durkushe tare da kamkame jikina guri daya na daura kaina bisa gwiwowina ina wani irin kuka duk wani kuzari da karfin jiki babu shi a tattare dani baya ga tashin hankali ji nake tmkr bani bace. gani nake tmkr mahaifina ya aikata min laifi ne me girma adalilin tarwatsa rayuwata dayake kokarin yi.. ahankali na furta kalmar shikenan tawa takare rasa taufeek daidai yake da rasa raina ..... daidai wannan lokacin mahaifina ya fito harabar gidan inda kowa ke tsaye cirkocirko yakaraso gurin da nake durkushe a kasa ina risgar kuka kmr wace narasa iyayena . yasa hannunsa ya dafa kaina yana kiran sunana mamana... ...na dago da sauri ina kallonsa da jajayen idanuna da suka gama rikidewa xuwa ja. tsoro da matsanancin firgici naga ya bayyana a fuskar babana alokacin dayake kallon kwayar idanuna. " yayinda ni km zuciyata tashiga bugawa da karfi numfashina ya soma barazanar daukewa ina cigaba da kallonsa . "wani irin ubane shi dai bai son farincikin ya'yansa ban taba tunanin mahaifina zai iya hanani abincin ruhina ba. lokacin danake zaune gabansa nayi danasanin kasancewarsa uba gareni domin ya aikata abunda iyaye dayawa bazasu iya yiwa ya'yansu na cikinsu ba ,na dauka ya'ya sune sanyi idanun iyaye a she ba hk bane .... ina cikin wannan tunanin ne muryarsa ta daki dodon kunnena lokacin dayake cewa taso mamana mushiga ciki ya miko min hanunsa. ,alamun nazo kallon tafin hannunsa nake ina tsiyayar hawaye batare da nayi yukunri mikewa tsaye ba,hawayen bakin ciki kawai ke gangaro min bisa kuncina . xuciyata shiga tunanin me yake son fada min km byn yayi nasarar rabani da sanyin idaniyana. " banda uba uba ne alokacin ina jin kmr na canza nawa uban.. "kusan minti goma ina zaune ina kallon tafin hannusa , sannan na mike a zabure ina kallonsa mgn nake son yi masa alokacin amman na kasa furta komai kawai na juya da gudu zan bar gurin ya sake kiran sunana muryarsa na rawa mamana ki tsaya ki saurareni....... na tsaya cak tare da juyowa idanuna akan fuskar mahaifina me zakace min baba ..?atahiri rayuwa ma iyaye kan sadaukar da farincikinsu ne wa ya'yansu domin samun kwanciyar hankalinsu . amman ni na kasa samun wannan farincikin daga gareka . "ina son taufeek tmkr raina.. ina son rayuwa tare dashi amman kayi sanadin yanke wannan soyayya me girma da sadaukarwa . taufeek na sona har yafi sona da bukatata fiyye da wanda kake kokarin hadani dashi . "amman babu komai Baba nagode......nagode ina kaiwa nan na haye matattakala da gudu suka biyo byna suna ihun kiran sunana tare da rige rigen kamoni. ban juyo balle na tsaya har sai dana dangana da dakina nashiga da sauri na rufo kofar tare da murda key . na jingina bayana da jikin kofar ina kuka ina sambatu irir ina kiran sunan taufeek da iyakacin karfina ...... bugun kofar suke da iyakacin karfinsu kowane nakiran sunana da kalar rarrashinsu gareni akan na bude musu kofar su shigo amman naki hk suka gaji da bugu kofar suka hakura . ranar gidanmu dawowa yayi tmkr gidan mutuwa kowa kagani fuskarsa babu annuri yayi jugun tare da zabga uban tagumi har matan yayyena. "mahaifiyata kuwa tunda tashige dakinta ta kulle kainta bata sake yunkurin fitowa ba... ni kuwa duk wannan lokacin ina jingine jikin kofar dakina ina kuka me taba rai .... jikina a matukar sanyaye na daga kafafuna da kyar na nufi gadona na fada ina sake barkewa da wani sabon kukan ina jin yau idan ban sake daura idanuna akan taufeek ba mutuwa zanyi.. ina son na sake ganshi koda kuwa hkn zai zama ganina dashi na karshe arayuwata wayyohhhly Allah babana kana son kashe saleemarka ne da hannunka.. meyasa baxaka gane halin dazan shiga arashin taufeek ba? meyasa bazaka zama jigon tallafawa tilon diyarka ba akan abinda zuciyarta ke matsananci so ba? ina son taufeek tmkr raina ida narashi zanshiga wani hali . sannan zaka iya rasani sanadin hanani aurenshi. meyasa bazaka fahimceni ba babana....... bani na sanyawa kaina son taufeek ba ? hk na dinga sambatu ina kuka ina birgima acikin dakina na dawo tmkr wata mahauciya, mahaifiyata tazo yafi sau goma tana min mgn na bude mata kofa naki . hk yayyena maza babu wanda bai yi iya kokarinsa ba ,har babana da kanshi sai daya zo yagama tsayuwarsa ya tafi. ina kwance lamo a kan makeken gadona tare da runtse idanuna hawaye na tsiyaya byn shudewar awa uku ina kwance kiran sallah ne kawai ke tayar dani. ranar kwana nayi kuka ina neman layin taufeek domin son jin muryarsa da sanin halin dayake ciki ,amman number'sa taki shiga ,abinda ya sake daga min hankalina kenan. na sake shiga rudani da tashin hankali fiyye da wanda nake ciki . "nayi kukan nayi hauka adakina tare da sabatu iri iri , idanuna bude suka kwana dan ko bacci barawo bai yi nasarar daukata ba yadda naga rana hk naga dare . hankalin mahaifina yayi mugun mugun tashi ganin har asuba naki bude kofar dakina. shi kansa ba'ason ranshi zai min auren da bana so ba ayyadda naji sautin muryarsa amman babu yadda ya iya da rayuwarsa domin bazai iya kin aiwatar da kudirin hjy harira ba . dan hk gari nagama wayewa tun da sassafe ya bar Cotonou zuwa xugu. zaune yake gaban hjy harira byn sun gaisa yace daman naxo ne kan zance auren salema da yakub .. nan yashiga koro mata komai dake faruwa tun daga farko da wanda tasani da wanda bata da masaniyarsa har ya dasa aya . tana gama ji komai tace uhm daka kwaso jiki kaxo me kake son ayi ..? daman nace ko za'a bar zance auren inyaso kowannensu ya auri wanda yake ra'ayi. " domin samun zaman lafiya kar azo garin karfafa zumunci,zumunci yazo ya lalace dan.... atsawace ta katse shi da hannuta tayi tsalle ta dire agabansa tana huci tmkr yar bori tare da cewa daga kai uban nata har ita salemar baku isa ba....nace baku isa ba . "ina tabbatar maka wannan auren kamar anyisa angama koda kuwa zata mutu tabar duniya ne byn anyishi . amman wallahi sai yakub jikana ya mallaki salema diyarka matsayin matarsa. sannan ga sako kabawa salemar idan ka koma gida, tasani yadda bata son auren yakub shima yakub bai sonta bai son aurenta nice nan nake son auren km tillas ayisa koda kuwa duk duniyar nan gatan ne . kai gaka me "ya" kawani kwaso jiki kaxo min da zantuttuka banza marasa ma'ana . dan hk nabaka nan da wata 3 kagama duk wani shirinka akan lamarin aure..lokacin yinsa yayi. hk
Chapter 118 · 0% Book details