← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 233 OF 289

Sashe 233

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

yi mata sannu kusan minti goma tana suna tsaye akanta suna jera mata sannu sannan ta amsa da kyar ta amsa "tace eiman ina kike samo wannan turaren haka me hawa kai tunda na shaka rasa abinda ke min dadi dan Allah karki kara amfani dashi . eiman tace "ai tuni ma na mikewa kule shi yaje can yakara, jiya ne fa danaje siyayya addal mall din yaya nagansa naji kamshi yayi min dadi shine na d'auka bansa abinda zai jawo ba kenan . ammi takarasa taje cire zanin gadon ta kai cikin washing machine ta dawo ta gyara inda tayi amain ta shimfid'a sabon zani gado ta dawo da su'ad ta zaunar daita tare da sanya mata pillow abayanta. ahankali su'ad taji cikinta yana murdawa still zuciyarta na tashi take kuma miyo ya cika mata baki ta yunkura zata sauko daga kan gadon zaraf taji ammi ta meida ita "ina zaki? tayiwa ammi nuni da bakinta "zauna bari na kawo miki guri ki zuba . eiman naji haka ta juya da sauri "ammi bari naje na d'auko kitchen taje ta d'auko robar ice cream ta dawo ta kawo mata ta zuba miyo ta koma ta kwanta tana sakin numfashin ammi tace "ko asamomiki goro ko wani abu kisa abakinki? ta daga mata kai ala'mun eh still eiman ce ta sake fita ta aiki hannatu. dare yayi kowa yayi bacci amman ita takasa runtsawa sai juyi take akan gado, ko sallar daren datake ma gbdy takasa tashi tayi ,ciwon ciki ya sakata gaba sai murkususu take tana kiran wayyohhhly Allah cikina mutuwa zanyi a zabure ammi tashi daga bacci datake tayi kanta tana mata sannu "sannu ciki kuma? " yanzu yazamuyi ta duba agogo karfe biyu saura minti goma "cikinki ke ciwo? ta sake tmbyrta har ta dauko jakarta datake zuba magunguna ciki ,tasan baza'a rasa na ciwon ciki ko me ta tuna sai kuma ta fasa ta dawo ta rungumeta ajikinta tana shafa kanta zuwa bayanta can kuma tasoma kakarin amai kwana sukayi tana amai da ciwon ciki ,tun cikin daren ammi takira doctor saif aiko karfe biyar a gida tayi masa yakaraso kanta wanda zuwa lokacin tagama galabaita ta fita haiyacinta, ya zuba mata ido sosai kafin daga baya yasoma bata taimakon gaugauwa ya dan jima akanta yana duba lafiyarta sannan yace wa ammi "tana bukatar drip sakamakon aman data kwana tanayi. cikin wasu mintina da basu wuce 20 da aka aki kule ba sai gashi ya dawo dr saif ya daura mata drip yayi mata allurar bacci cikin drip din sannan ya shiga tmbyr yadda ciwon ya faru ammi tashiga yi masa bayani tunda ga shigowar eiman har zuwa yanzu, inda take kan docto ya kulle shifa daman tun sanda akawo asibinsu wajen scanning yaga wani abu kmr gas a saman mahaifarta anya kuwa ba ciki gareta ba ya fadi haka cikin ransa ya jima tsaye a dakin yana kallonta sannan ya dibi jininta ya fita. kai tsaye yana barin gidan hospital ya nufa ya jima cikin office dinsa yana dube dube da aune aunensa gabadaya hankalinsa a matukar tashe yake ya tattara natsuwarsa akan gwajin jinita sabani idan irin haka ya taso bashi ne ke yi ba akwai wad'anda keda alhakin haka. hankalisa yayi mugu mugun tashi ganin da gaske dai abinda yake zargi dai shine yagani amman sam yaki amincewa ransa cewar sakamakonta ne dan haka yanke sha'war azo daita. mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 233 · 0% Book details