Sashe 182
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
cike da matsanancin kaunarsa .. wani tausashen murmushi ya sakar mata yana kashe mata idonsa daya aiko ta zabga masa wata katurar harara tana dauke idanunta akansa taci gaba da aikin ta. " Kai ni kike harara? Yarinyar nan kin gama rainani ko? Tayi mishi banza yakaraso ya zauna kusa daita ya kamo hannuta daya cikin nasa yana massaging ahankali ahankali yana narke mata muryarsa a kasalance yace " Kije ki dauko jakar tsarabarki ko kuma ki hadu da bacin rai ......ta dago fararen idanunta tana dubansa tana yatsina fuska zatayi magana "yace wallahi kiyi abinda nace ko na shuka miki rashin mutunci kin San km zan iya ko? zate hannuta tayi cikin nasa ta mik tsaye da niyyar shigewa cikin dakin ammi sbd bazatayi abinda yake so din ba sai dai yayi abinda zaiyi . Ya kai hannunwansa duka ya fixgota da karfi. "me yasa kika fiye taurin kai? "ina sonki baya nufin zan dauki wulakacin da rashin kunya ba. ta lumshe fararen idanunta tare da dafe goshinta tana layi kmr me shirin sumewa, ya kara matsota sosai ya daga murya, "kina ganin zaki iya ja dani ne? ........luuu yaga tai kasa tana shirin zubewa yayi saurin tarota zuwa faffadan kirjinsa ya rungumeta tsam tare da zaro ido su'ad ...Yakira sunanta a matukar firgice yana sake tarairayota zuwa jikinsa pls hrt beat karki min hk babu abinda zan miki da wasa nake ina mahaukacin mugu mugun sonki bazan so wani abu yasameki a halin yanzu ba gbdy ya rikice ya gigice yasoma waiga waigan neman ruwan da zai yayyafa mata babu komai kusa wanda zai yi amfani dashi gurin dawowa da numfashinta , jikinsa na rawa ya sungumeta yayi bisa kujera three seater ya kwantar daita yayi cikin kitchen da gudu ya bude fridge zai dauko ruwa..... .. tana ganin ya bar gurin tasoma bude idanunta ahankali ahankali har ta budesu duka koda taga wayam ala'mun yashiga kitchen a matukar zabure ta mike tare da kwasawa da matsiyacin gudu tabar falon din.... Ya fito daga kitchen rike da kofin ruwa a rude.....kawai yaga wayam babu ita babu alamunta Ya kwala mata kira hrt beart..... garam yaji anja murfin kofa..... take ya fahimci me tayi bai sanda ya saki kofin da ruwan dake rike a hannunsa ji kakeyi ratsatsatsa..... *miss you guys* mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE