Sashe 174
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *Allah messenger saw said A true Muslim is one from whose tongue and hand the Muslim are safe* page 60 cikin zaman da bai ce minti 20 sai ga wani matashin saurayi ya shigo, wanda akalla shekarunsa na haihuwa bazasu wuce ashirin da biyar ba bakine , amman irin bakin nan me kyau, ahankali yakarasa shigowa cikin office din ya zauna tare da gaishesu, suka amsa. sannan ya gaisa da likita. "yauwa mahruf wannan hjyr zaka duba mana lfyr hannuta ka gano mana meye matsalar hannu nata, sbd muji dadin bata taimakon daya dace. " to yallabai matashin saurayin ya mike daga inda yake zaune yakaraso xuwa inda su'ad ke zaune ya tsugunna a gabanta yana satar kallonta. ak dake zaune ya taso daga kujerarsa shima ya tsugunna gefen da su'ad ke zaune fuskarsa a hade, kmr tayi dariya sbd ganin ya kasa hakuri ya yazi ya kasa ya tsare. amman sai ta dake itama ta bata rai kmr farko . amman lokacin dataji saurayin ya matsa hannuta , ta saki wani kara sbd yadda irin damkar dayayiwa hannuta yasha banban da irin wanda doctor yayi mata wajen zafi ashe na doctor shafar mai ne akan nasa "kai! kai!! wash, kai wallahi tsaya da zafi fa sosai, kayi min ahankali ,yasa hannusa daya a tafin hannunta ,dayan km ya fara taba yantsunta dashi ta sake sakin wani razananniyar kara tare da damkar rigar ak dake makale daita da iyakacin karfinta tana kiran washi Allah zan mutu . "dakata dakata dakata!!! kaga tana jin zafi fa . "yallabai hkr zakayi yasamu ya duba mana ita sbd abun sai wanda yake aikin shine zai iya ganewa musan matsayin ciwon hannuta inji cewar likitan . "ok ok shikenan doctor yayi mata amman dan Allah yabita ahankali ina jin ciwon har cikin raina bari ma na fita dan bazan iya ganinta cikin wannan tashin hankali ba sbd tanaji zafi sosai su'ad wacce ta runtse fararen idanunta gam tana jin radadin azabar zafi, tasan ba wani zance dan zataji zafi ne zai sashi fita daga office din ba, tsabar jarabar kishi ne kawai na kada yaga saurayin na taba mata hannu yana kallo ke damunsa amman duk da yace fita zai yi ya kasa fita ya dawo bayanta ya zauna ya rungumeta ajikinta tsam... . yayinda ita km tun tana iya daurewa har sai gata tana zubda hawayen azaba , a hk me gyaran hannu yasamu ya dubata ya gayawa likita targade tayi a hannuta ,nan take doctor ya bashi umarnin ya kama mata kuka su'ad take sosai har da rike AK kam kam ,sbd wani irin tsananin azabar zafi datake jin yana ratsata. da kyar tasamu ta daure aka gama daure mata hannu sannan likita ya rubuta mata magunguna har dana shafawa a hannu suka baro office din Doctor tana kuka ak rike da hannuta kmr wata karamar yarinya. suna shiga mota kasa daurewa tayi tacigaba da zubda hawayen da suka rage acikin kwarnin idanunta na azabar zafin ciwon hannuta. matsowa AK yayi sosai kusa daita yana kallonta cike da tausayawa, ji tayi ya kai hannunsa ya dago kanta dake duke batare da yace mata komai ba ya ciro hanky agaban aljihun rigarsa ya kai hanunsa yasoma goge mata hawayen dake tsiyaya daga ciki kwarnin idanunta "da zafi ko? sorry hrt dina bansa yadda za'a yi in cire ciwon daga jikinki ba ya dawo kaina ba danayi ahalin yanzu "ya dan yi shr tare da sake tsura mata mayatattun idanunsa yana kallonta kana ya numfasa ahankali sannan yacigaba "dana san hk zaki sha wahala irin hk daban kawoki ba ,ni na janyo miki ciwo har hk ko? "sannu kinji my Hrt beat "hk ya dinga rarrashinta da daddaden kalamai masu tsuma zuciya wanda alokacin har taso manta inda suke sbd sanyi dataji yana ratsa sansar jikinta a hk har yasamu kukan nata ya tsaya sannan ya tada motar . "maimakon yayi hanyar da suka biyo da zasu taho hospital sai taga ya dauki wata hanyar daban suna cikin tafiya taga kmr ta cikin unguwarsu ya biyo daita dayake idanunta na kallon bangaren glass din motar ne, da wani sauri ta juyo inda yake zaune yana tuki wanda kadan ya rage bata fama ciwonta ba. cikin rawar jiki ta daura hannuta kan hannusa dake kan giyar motar "pls ka tsaya muna cikin unguwarmu ne, "idan ka kai karshen layin akwai zaka gida me bakin get pls ka tsaya agurin nashiga naga lfyr ummata nayi kewarta dayawa ina son naganta pls , duk maganar datake bai waigo ya kalleta ba balle ya tanka mata har ya nuna mata ya fahimci abinda take nufi. tana rawar jiki take sake yi masa bayanin yadda tayi missing din ummanta amman ko kallonta baiyi ba tana kallo sanda yazo daidai kofar gidansu ya taka motar da karfi ya kwasa a guje ya fice daga unguwar. tayi shr kawai tare da tsare shi da fararen idanunta tana kallonsa hawaye na zuba daga idanunta kmr ta shake masa wuya hk taji aranta. wani irin kololon baki ciki taji ya caki makoshinta "tarasa meyasa abdulkabir batason ganin mahaifiyata "hk kwanakin baya tacewa ammi tana son zuwa dubo ummanta tace ta tmbyi shi ,bata tmbayeshi ba tasa eiman ta masa "yace kartaje wanda tarasa dalilinsa na hanata zuwa gashi yau km tana ji tana ganin ya wuce gidan ya hanata ganin kyakkyawar fuskar mahaifiyarta dake kwantar mata da hankali. cike da matsanancin takaicinsa ta dauke idanunta akanshi ta mayar bangaren titi tana kallon mutane da ababen hawa dake wucewa. kai tsaye companies na addas mall ya nufa daita yayi parking a harbar company tana kallonsa ya fito yana gyara zaman rigar jikinsa sannan ya dan kallo inda take "yace mata tajirashi yana zuwa yanzu ,ko kallonsa itama batayi kmr yadda shima yayi mata dazu sai ma kawar da fuskarta datan gefe tayi tare cewa aranta "daga can ma karka dawo mugu kawai me mugun hali bansa meyasa ma na fada tarkon sonka ba. addas mall hadadden company ne wanda ak ya budesa a yan watanin baya da suka gabata anan cikin a bega before under bridge din da zai kai mutun mowe ibafo. company addas mall guri ne wanda yasamu karbuwa takowani fanni agurin mutabe waje ne wanda yake bangare daban daban ata kewaye dashi, company ne wanda ake saida hadaddun kayan manya maza dana manya mata har ma dana kananan yara, tattare da kayan jeweris da takalma design ata bangaren dama akwai health Plus da gurin yin duk wani na'in wanda ya danganci snack . tafiya yake ahankali cikin takunsa na isa da takamar shi wani ne agurin sannan km dan wani kusa a kasar Nigeria ,yayinda Manya ma'aikatan da idanunsu ya sauka akansa suka mike tare da karasowa zuwa gareshi cike da girmamawa suna kwasar gaisa hannu ya mimika musu suka gaisa kasancewar shi bashi da girman kai idan dai bakasan sanshi bane zaka iya masa kallon me shegen girman kan tsiya . "yallabai yau da kanka inji cewar manage gurin daya karaso alokacin byn ya gaida me gidan nasa,"wallahi damola akan hanya nake sauri ma nake ina tare da madam ne nace na san leko "gsky mun gode suka soma tafiya tare acikin compay suna tautaunawa yayinda AK ke daukar abubuwan daya shigo dominsu daga karshe ya zarce inda ake sarrafa snacks da ice cream.. bai fi 30 minit da shiga ba sai gashi ya fito tare da wasu matasan samarina guda biyo biye dashi hannuwansu rike da fararen ledodi sai wani mutun daban wanda batasanshi ba sanye cikin wasu haddaun bakaken suit. tun kafin yakaraso daya daga cikin samarin ya hanzarta karasowa domin bude masa motar amman ya dakatar dashi ta hanyar cewa "dont worry gbenga ,yakaraso ahankali ya bude murfin mota yashigo ya zauna sannan ya amshi ledodin dake rike a hannusu ya mikowa su'ad ,kin amsa tayi daga hannunsa ganin hk yasa yayi saurin ajiye ledodin a set din abayan motar dan kar batada shi agaban yaransa yayi reves yana musu sallama suna tsaye a harabar compay har sai da suka ga wucewarsa sannan kowanensu yakama gabansa. tafiya kadan yayi yaja birki ya faka a gefen titi still bata juyo ta kalli inda yake ba muryarsa a matukar kasalance yace "akwai kayan gyaran fuska cikin daya daga cikin ledodin ki duba ki gyara fuskarki kada ammi ta dauka ko wani abu na miki kijamin fada. "ta juyo da kyakkyawar fuskata ahankali ta sauke akansa tana dan hararasa tare da turo masa dan karamin bakinta "ni bazan gyara wani fuska ba . "uhmm hrt beat dina kar muyi hk dake fa ,"tausayi kike bani if not da sai na biya duk kudin wannan hararar da kallon da kika min yanzu ,hk fa kika dinga min irnsa a office din likita wanda sauran kadan nayi losing control gashi yanzu ma kin kara ko in rama ne? "tayi shr taki cewa dashi komai sai fararen idanunta dake yawo ajikinsa. ya marairaice murya sosai kmr zai yi mata kuka "ki gyara mana "sai ka fita daga cikin motar "ina zani ni da matata? "ni ba matarka bace.. matarka na gidanka ka baro tana jiranka amman ni matar r..... kafin takarasa abinda take son fada ya fige motar aguje diraving yake ransa a matukar bace batare da ya kalli inda take ba sai sautin muryarsa dataji cikin slow motion "ban gaya miki ki daina furta min irin wadan nan kalaman ba da sunan mu rabu va? " ni mijinki ne ,mijin mutu karaba wallahi bazan iya sakinki ba ahalin yanzu koda kuwa naman jikina zaki dinga yanka, ina tabbatar miki sai dai ki mutu da aurena akanki.. "su'ad kullun ranar duniya sake shiga cikin zuciyata kike sannan na lura yanzu kin fi son ganina cikin bacin rai akan kwanciyar hankali, "allah ya huci zuciyarka ni dai yanzu kayi hakuri ka mayardani gida dan Allah. "gida kike son zuwa? uhm "ok zamu gida yanzu kuwa ya kai hannusa ya kamo hannuta cikin nasa yana massaging ahankali ahankali yana cigaba da deraving yana jin yadda jikinsa ke sauyawa akanta . bata ce masa komai ba kmr yadda shima yayi mata banza yacigaba da tukinsa ,tana jiran taga ya dauki hanyar zuwa gida sai taga ya