← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 205

Sashe 98

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba amma dai ya san busar da kai take yi. A hankali ya busar mata da kan nata, ya auki ribbon a kan madubin ta ya aure mata kan. Zagayowa ya yi ya tsuguna a gabanta cikin rarrashi ya ce, "Sai me?." Nayla ta sunkuyar da kai asa cikin rauni ta ce, "kaina." Maganinta na ranar farko ya auko ya bata ta sha, shima ya sha na ciwon kai sannan ya sake cewa, "sai me Ashiq? Me ki ke so kuma bayan wannan?." Nayla a shagwa e ta ce, "bacci zan yi." Ya ago ta ya ri e ta har kan gadon ta kwanta a jikinsa ya ce, "to ki yi bacci." A hankali ta rufe idanunta dan bacci take ji. Sai da ciwon kan ya sauka sannan ta yi bacci shima kuma maganin ya saka shi bacci. KRB3P057 Kusan makara sallah suka yi, ana idar da sallah suka farka a tare, ya tashi da hanzari ya yi alwala itama ta yi suka yi sallar a aki. Bayan sun idar kanta yana asa ta ce, "Ina kwana." Ya dawo kusa da ita yana le a fuskarta ya ce, "ina kwana." Bata kalle shi ba ya ce, "ya ciwon kai? Ya daina?." Ta aga kai alamun eh. Ya yi asa da murya cikin muryar soyayya ya ce, "Zafin fa? Shima ya daina ko zamu je asibiti?." Nayla ta aga kai ta ce, "yana yi, amma ka an" ta fa a kamar tayi kuka. Cike da damuwa Omar ya ce, "Yi ha uri Jiddana, kar ki yi kuka kin ji? Ni na saka ki ke jin zafi ko?." Ta aga kai kamar aramar yarinya, ya ce, "Bazan sake ba" ya fa a cikin rarrashi yana pecking goshinta. Ta kwantar da kai a kafa arsa jikinta a sanyaye, ya sake kissing kumatunta ya ce, "Sannu Ashiq." Ta aga kai alamun yauwa. Omar ya an yi tsaki ya ce, "ni ban san sai zuwa yaushe za a daina jin zafin nan ba, na yi tunanin a na ranar farko ne kawai ashe har rana ta biyu ma. Ya kamata na tambaya na ji adadin kwanakin ko?." Nayla ta kalle shi cikin mamaki, ta auka zata ga alamun wasa a tare dashi sai ta ga da gaske yake maganar, ta sunkuyar da kai tana mamakinsa. Da gaske bai sani ba ko kuma dai raina mata hankali yake yi? Bata gama mamaki ba ta ji ya ce, "Babu abinda na sani a wannan angaren Ashiq, shiyasa ake ta samun damuwa, na ji haushin rashin sanin da bani dashi a ranar farko da na rasa me zan yi na taimaka miki. Wai ashe a cikin ruwa mai umi zan saka ki." Murmushi ta yi tana mamakinsa, da gaske yake babu abinda ya sani in ko dai da in baki ne? To yanzu akwai saurayin da zai ce bai san komai ba?. Ko ita tun tana secondary school ta san me aure yake nufi balle shi namiji. Tana wannan tunanin ta ji ya ce, "kinga ya kamata na tambaya na ji, bana so a karo na uku a sake samun matsala ki zo kina ta kukan nan, bana so." Bata san ta ago ido ta kalle ba sai jin muryarta tayi ta ce, "wa zaka tambaya?." "Didi" ya bata amsa kai tsaye. Ta wara ido ta ce, "don Allah kar ka tambayeta, kai baka jin kunyar ta ne?." Cikin rashin damuwa ya ce, "Jidda ina da wacce ta fita ne? Itama ba kunyata take ji ba, lokacin aurenki haka ta dinga maimaita min kalmar mu'amalar aure kamar ruwan sha, inda tana kunya ta baza ta fa a ba. Ni na fa a miki sau daya na ta a jin kunya a rayuwata. Bana jin kunyarta, zan iya fa a mata duk abinda yake damuna ko yake damunki, tare na tashi da ita, da ita ka ai na saba Jidda. Nayla ta ce, "kar ka tambaye ta don Allah." "To wa zan tambaya?." "Zan tambayi wata likita." "To ki tamabaya kafin zuwan na ukun, ba dan ma ina tsoron kukan nan naki ba ai da na ukun yazo yanzu" ya fa a yana kallon ta ta rufe ido da hannayenta. Murmushi ya yi ya ce, "abin mamaki, Omar ya yi mata. Tashi mu kwanta Jidda!" ya fa a yana mi ewa tsaye. Nayla ta ri e hannunsa ta tashi tsaye suka kwanta, tana kwance a jikinsa har suka yi bacci. Da safe ma shi ya shirya mata komai kafin ta tashi, har ta tashi ta yi wanka ta shirya sannan ya shigo akin. Kallon ta ya ke dan ta yi kyau cikin shigar da tayi, ya rungume ta ya ce, "kin yi kyau Ashiq." Bata kalle shi ba ta ce, "kaima ka yi kyau Ashiq." "A'a..YaMar, ya fi min da i a bakinki fiye da komai. Da farko na auka daga sunan ne da kika canja masa salo, da na saka Didi ta fa a sai na ji ba wani armashi" ya fa a yana yatsine fuska. Dariya Nayla take yi tana jikinsa ya ce, "Da gaske nake, daga baya na fahimci daga bakinki ne." ago ta ya yi yana kallon fuskarta da take auke murmushi, ya yi mata kiss a goshi ya ce, "kin yi kyau." Ta yi asa da kai ta ce, "na gode. Kaima ka yi kyau." Wani irin shau inta ne yake aukarsa a kanta, kasalallan shau i da yanayin son sake kasancewa da ita ke taso masa, musmaman da ta yi magana sai ya ji kamar ya kama bakin ta ya yi kissing yadda yake so, ya san in ya yi hakan bazai iya ri e kansa ba gwara ya kama kansa shiyasa ya ce, "Zo mu je ki ci abinci." Nayla ta ce, "ka manta yau Monday? Ni na tashi da azumi." Da sauri ya kalle ta jin abinda ta ce, ya ce, "Azumi! Wanne azumi?." "Azumin da nake yi duk sati mana." "To da izinin wa ki ka auki azumi?." Yadda ya kafa mata ido yana tambayarta ya saka gabanta ya fa i, ita sam ta manta da batun sai ta tambaye shi zata yi azumi, ta saba tashi dashi kawai. Jin ta yi shiru sai ya ce, "ina tambayarki, waye ya baki izinin azumi Jidda?." Nayla ta ce, "Na manta ban tambaye ka ba da daddare, amma ka yi ha uri bazan sake auka ban fa a maka ba." Ya girgiza kai bayan ya ha e rai ya ce, "baki da lafiya zaki auki azumi? Kin manta da ciwon kai ki ka kwana?." Nayla fanin ya aure fuska sai ta karyar da murya ta ce, "Ai na ji sau i shiyasa na auka." Kallon ta yake yi yana jin shau insa na aruwa sosai, jin shiru bai ce komai ba sai ta ago ta ga irin kallon da yake mata sai ta auke da kai. Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Mu je ki ajjiye azumin ki ci abinci." Nayla kamar zata yi kuka ta ce, "da gangan kenan zan karya?." Ya aga gira ya ce, "in baki ci abinci ba ma zan karya shi, gwara ma mu je ki ci. Gobe sai ki sake aukar azumi babu izinina." Nayla kamar zata yi kuka haka ya sakata dole ta ci abinci, gashi ta ji wasu malaman suna cewa in ka karya azumin nafila da gangan sai ka yi kaffara. Har aka gama cin abincin unci take yi idonta ya taru da hawaye. Kallon sa ta yi taga yana kallonta sai hawayen ya sakko kan kuncinta ta ce, "Wasu malaman sun ce sai na yi azumin kaffara tunda da gangan na karya." Cikin rashin damuwa ya ce, "Maganin mai aukar azumi babu izini kenan, Duk ranar da zaki yi na kaffarar sai ki fa a min. Ki goge hawayen nan." Nayla ta goge idanunta ta sunkuyar da kai tana turo baki. "Kin san kina azumin ki ka yi kwalliya haka?." "To mai azumi baya kwalliya?" Ta fa a murya na rawa sosai. Ya ta e baki ya ce, "baki sani ba?." "Ni ban ta a ji ba." "Yau kin ji." Shiru ne ya biyo baya dan wallahi ta ji haushin karya azumin da ya saka ta yi sosai. Shirun da ya biyo baya ya saka ta share hawayen idanunta. Yana kallon ta yana murmushi a zuciyarsa, bai yi magana ba sai da ya ga dama dan kansa sannan ya ce, "yaushe zaki koma aiki?." Kallonsa ta yi ta ga fuskarsa ta canja zuwa wani yanayi na daban, ta ce, "Sai wani satin." Kai ya girgiza kai bai ce komai ba, ta sake kallonsa tana karantar yanayinsa, kana ganin reaction insa ka san baya son aikinta dan babu yadda zai yi ne kawai. Ganin haka sai ta ce, "Ka ce zaka fa a min maganar Abiy, da bai amince ba ya zaka yi?." Ya juyo ya kalleta yana lumshe ido ya ce, "to zo na baki labari." Ta aga kai suka ha a ido ya wara idanunsa a cikin na ta ya ce, "ki zo." Ta no e kafa a kamar yarinya tana turo baki gaba ido na cikowa da hawaye. Ya bita da kallon burgewa da sha'awa, ya kafeta da idanunsa yana kallonta, murya can asa ya ce, "ki zo." "Ni dai uhum uhum" ta fa a tana sunkuyar da kai. Ya yi murmushi ya ce, "to ni bara na zo" ya fa a yana dawowa kusa da ita ya ri ota yana ago fuskarta ya ce, "me ya faru kuma zaki yi kuka? Baki san bana son kukan ki ba?." Bata ce komai ba ta kwanta a jikinsa tana matsar walla ta shagwa "Jidda da gaske inda Abiy ya ce baya bu ata ta a matsayin mijinki zan ha ura dake, kin san Meyasa?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "Mahaifina Allah ya ji an shi, lokacin da aka yi auren shi da mahaifiyar mu iyayenta ba sa so ko ka an. Ba sa son auren ta dashi ko ka an Jidda. Da ta rasu mahaifin mu ma ya rasu danginta sun kasa ri e mu saboda kawai basa son mahaifin mu mu ma basa son mu. Mun sha wahala sosai kafin Allah ya kawo mana mafita, Didi ta sha wahala sosai, na bata wahala, kullum cikin yawo nemana take
Chapter 98 · 0% Book details