← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 205

Sashe 146

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baya, tunda na ga Jidda da ciwo a hannunta nake danasanin abinda na aikata. Meyasa baza su auki fansa a kaina ba? Ai ni na aikata ba ita ba, kuma yanzu ina ruwan cikin da yake jikinta da aka tsallako kansa?. Illar dabar kenan ai, wannan gabar da son aukar fansar da take tsakaninku zata iya zuwa har kan jikokinka wallahi, bama cikin Nayla ka ai ba, har jikan da zaka bari a duniya sakayya zata iya fa a masa. Ka kiyayi sakayya Omar, ka kiyayi ha in wanda ka zalunta ba tare da laifin komai ba. Allah yana yafewa bawansa laifin da ya yi masa duk girmansa, amma laifi tsakanin bawa da bawa Allah baya yafewa, sai dai in aya ne ya yafewa aya. Itama matar aura yake ko waye ai itama ba ita tayi laifin ba, bata san komai ba balle kuma cikin jikinta da bai zama mutum ba. Ka kwashi yara aka je har gida aka yi mata abinda ya firgita ta har ciki ya zube, daga arshe ta rasa ranta. Omar in nace ha in mutuwar ta a kan ka yake kar ka musa. Ya girgiza kai ya ce, a Didi, babu ha in ran kowa a kaina, don Allah ki daina fa Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, abar tausayin ma Nayla ce ba kai ba, ta auri mijin da sakayya da fansa take bibiyar rayuwarsa ta ko ina. Sau biyu ana arin kashe ta, yau ga na uku ana so a kashe ta har da an cikinta. Wannan aure bai amfana mata da komai ba sai tashin hankali, meye ribar wannan auren don girman Allah?. Ta gaba da baya Nayla bata dace da kai ba wallahi. Omar ya yi shiru bai ce komai ba, Didi ta ce, yanzu in aka sake cutar da ita da wanne ido zaka kalli mahaifinta? Wancan ya samu labari ya yi shiru bai ce komai ba, ya sake faruwa nan ma bai ce komai ba. Kana tunanin in ya sake faruwa zai yi shiru?. Omar bai ce komai ba ya sake yin shiru yana jinta. Didi ta ce, Omar domin ceton rayuwarta da rayuwar abinda yake cikinta me zai hana baza ka sake ta ba?. KRB3P088 Nana haleema Wani irin kallo yake yi mata mai kama da baki da hankali, ya bu e ido yana sake kallon ta dan ya tabbatar tana cikin hankalin ta kuwa. Didi ganin kallon da yake mata sai ta bu e baki zata yi magana ya dakatar da ita cikin fusata ya ce, da ina da wani wajen da zan je a bani shawara wallahi bazan zo wajan ki ba, a ko yaushe sai kin ata min rai akan duk maganar da na kawo miki. Ni ki ke kallo ki ke cewa na saki Jidda? Ni ne zan sake ta?. Anya baza a kai ki asibitin mahaukata a bu e miki file ba? Dan wannan kalaman na ki bai yi kama da aikin mai hankali ba!. Didi ta an yi murmushi dan wallahi dariya ya bata, ta ce, Ni ba haka nake nufi ba, saboda ceton rayuwarta shiy..! A fusace ya katse ta ya ce, shiyasa ki ke kallona kina cewa na sake ta? Ko kunyar idona baki ji ba ni ki ke fa awa haka Didi?. Kin ce aurena bai amfane ta da komai ba sai tashin hankali nayi miki shiru ban tanka ba, kince bata dace dani ba shima na share ban ce komai ba. Yanzu kuma idona ki ke kallo ki ke cewa na sake ta? Anya Didi ke jinina ce?. Bata san lokacin da ta fara dariya mai arfi ba, ta kwanta a akan kujera tana dariya dan wallahi dariya ya bata, ko ka an bata ji haushin kalamansa ba dan inda sabo ta saba. Tsaki taji ya yi, ta san arshen abun kuma fita zai yi. Da sauri ta mi e ta ri e hannunsa yana niyar fita, ta ce, Don Allah yi ha uri, ni ba da wani abun na fa a ba wallahi, bana so a cutar mana da unborn shiyasa na ce haka. Amma ka yi ha uri bazan sake irin wannan maganar ba, ka dawo ka zauna don Allah. Hannunsa ya zame ya ce, bazan zauna ba, dan nazo ki bani shawara ki ka saka ni a gaba kina dariya dan kin mayar dani mahaukaci. Naji, ka yi ha uri mu cigaba da maganar. Wallahi bazan zauna ba ya fa a yana auke kai. Didi ta ce, to mu cigaba da maganar a tsaye. Yanzu ya kake ganin za a yi? Wanne mataki za a auka akan hakan?. Banza ya yi mata bai amsa ba, ta ce, don Allah ka yi ha uri mu yi magana. Shirun nan bazai amfane mu ba, kar a cutar mana da ita ko abinda yake cikin ta. Omar ya sauke numfashi ya ce, Meyasa baza su auki mataki a kaina ba sai kan Jidda ko abinda yake cikin ta?. In aka ta a maka ita sai kafi jin zafi akan a ta a ka, ko me suka yi maka baza ka ji ciwo a ranka ba, zaka fi jin ciwo in aka ta a Nayla ko abinda yake cikin ta. Shiyasa auran ya yi jinkirin aukar fansa, dan yana son ya ta a rayuwarka gaba da baya. Ya yi shiru bai ce komai, Didi ta ce, yanzu meye mafita? Zaka je ka samu auran ka bashi ha uri?. Wani kallo ya yi mata mai cike da harara, Didi ta ce, eh Omar, abinda ya kamata ayi kenan. Ka je ku yi sulhu hakan zai fi, in aka bar maganar nan bamu san abinda zai faru ba. Ya gyara tsayuwa ya ce, Didi kai tsaye akwai wanda ya ta a ce miki baki da hankali?. Dariya ta kama Didi, amma gudun kar tayi ya fita sai ta ce, a, ba a ta a ba. To yau na fa a miki. Na daina tantama, tsaf aka bu e miki file a gidan mahaukata gado zasu baki. Didi ta karyar da kai tana oye dariya ta ce, to na gode. Dan mai hankali bazai cewa Omar ya je ya nemi sulhu da wani aramin alhaki kamar aura, ni zan je na nemi sulhu dashi Didi? To Wal iya da Kb ban je na nemi sulhu dasu ba sai wannan aramin abun da bai wuce na taka shi kamar yadda yake taka asa ba. Ni bazan je neman sulhu ba, nafi arfin neman sulhu. Didi ta bishi da kallo, ta auka yayi sanyi akan Nayla zai iya watsar da girman kai ya je ya nemi sulhu a wuce wajan ashe da saura. Didi ta ce, ni na rasa yaushe zuciyarka zata yi sanyi Omar, na rasa abinda za a yi maka da zai saka kayi sanyi wallahi. Babu, babu abinda zai saka na sakko asa Didi. Didi ta ce, ai shikenan. Kawai zan je mu ha u dasu, ayi kare jini biri jini, koni ko su, ko su karni ko na karsu. Abinda nake so dake koda zasu kashe ni, ki tabbatar da Jidda ta kasance cikin oshin lafiya, ki tabbatar abinda yake cikin ta ya rayu cikin aminci. In ta haifi namiji ki saka masa sunana, in macece sunanki. Amma ki fara tambayarta, in tana da za in suna a saka za inta. Sannan ki san duk yadda zaki yi ki tabbatar da Jidda bata auri wani namijin bayan ni ba, ta cigaba da rayuwa a haka har tazo ta same ni mu tashi a aljanna. In ta auri wani bayan ni bazan ta a yin farin ciki ba har abada! Ya fa a so serious yana kallon Didi. Rauni ya mamaye zuciyar Didi ganin da gaske yake maganar, ta ri e hannunsa ta ce, Omar me ka ke fa a haka?. Gaskiya nake fa a miki Didi, zan iya sadaukar da raina akan Jidda da abinda yake cikin ta. Marmerh a iya kallo aya soyayyarta ta cika zuciyata, cikin jikinta kuwa tunda aka ce min an same shi nake jin son ko meye a zuciyata. Da na rasa abinda yake cikinta gwara na sadaukar da raina a huta. Daman ba saboda ni suke wannan abubuwan ba? To in na mutu ba shikenan an huta ba?. Didi ta fara kuka cikin rauni ta ce, babu abinda zai same ka, baza ka mutu ba Omar, baza ka mutu yanzu ba in sha Allah. Kuma Omar in ka koma ka auki makami dan tsayar da wannan maganar hakan ba masalaha bane, domin wallahi baza su ha ura ba. Kuma Omar duk aukakar da ka samu a rayuwarka ka rasa dame zaka sakawa wanda ya yi maka sai ta hanyar cigaba da abinda ka bari!?. In ka yi haka baka godewa Allah akan ni imar da ya yi maka ba, in ka aikata haka wallahi ka butulcewa ni imar Allah, kuma ka bar baya da ura, domin baza a ta a daina bibiyar mu ba har abada!. Ka fini sanin illar daba, kai da kanka ka ta a bani labarin wani babban mutum da yayi irin rayuwarku har girmansa, arshe har gida aka shiga aka yi masa yankan rago saboda aukar fansa kawai. Kowa ya san daba haka take, kai zaka aikata laifi amma a kan danginka za a auki fansa, matu ar ka sake komawa ruwa ka gama cutar kan ka da ahlinka. Yadda ka juya mata baya ina so ka sake juya mata baya, ka sauke kai asa domin wannan fitinar ta lafa. Yayi ajiyar zuciya yana shafa goshinsa da yatsunsa kamar yadda ya saba, ya rufe ido ya bu e cikin rashin mafita. Didi ta ce, ka je ka same su Omar, ba lallai sai ka bada ha uri ba, ko ku i ne ka biyasu akan su janye. Bazai janye ba, na san halinsa. To ku tattara ku bar Kano kai da ita, kana da arzu in da zaka iya zama a wani garin ba lallai sai nan ba. Ya harare ta ya ce, kawai ki ce naji tsoro na gudu na bar garin saboda tsoronsu. Ba tsoro bane Omar, ja da baya ne. Su a wajansu tsoro ne, kuma inaso ki tuna, Omar baya ja da baya. Didi ta ce, ni dai bana so ka butulcewa mahaliccinka akan ni
Chapter 146 · 0% Book details