Sashe 69
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki tuna bayan Allah ya ji an iyayen mu, bayan zumunci akwai wacce ya kamata ki saka." Didi ta yi murmushi ta ce, "wacce kenan?." Ya an yi aramin tsaki ya ce, "Sai an yi magana ki ce na san halin ka fiye da kowa a duniya, amma gashi kin kasa gane abinda nake nufi" ya fa a cikin kwaikwayon muryar Didi. Didi ta yi murmushi ta ce, "Allah ya bar ka da matarka Nayla." Murmushi ta ji ya yi mai sautin gaske ya ce, "na yarda a duniya babu wanda ya zan Omar kamar ki. Amin Yayata, Na gode da addu'arki, ki kula min da ata zan zo na ganta." Didi tayi murmushi tana kallon Nayla ta ce, "Allah ya kawo ka." Omar ya amsa yana yanke wayar. Umma Saroot ta ce, "Aisha Allah ya bar zumuncin ku da Omar har abada, Allah ya wanke masa zuciyarsa ya daina jin abinda yake ji akan dangin mu da na mahaifinsa. Omar mutum ne mai kirki da aunar zumunci, mu muka lalata komai amma in sha Allah komai zai wuce." "Amin Umma, in sha Allah komai zai wuce." Ta girgiza kai tana goge hawaye ta ce, "ana kirana a waya" ta fa a tana shiga ciki. Didi ta kalli Nayla ta ga tana murmushi har lokacin Babyn tana hannunta ta ce, "Nayla duk da Omar akan katanga yake amma mijinki ne, ki taya ni yi masa godiya." Nayla murmushi kawai tayi amma bata tanka ba, zuciyarta kuwa farin ciki take ji kamar ta taka rawa. Sai bayan sallar magriba sannan driver ya dawo ya auke ta suka koma gida. Tun daga ranar Nayla kullum sai ta zo gidan Didi, Didi bata ta a yi mata maganar Omar ba itama bata yi mata. Dangin su Nayla kuwa kamar dangin Didi haka suka dinga tururuwar zuwa yiwa Didi barka. Hajja da kanta sai da ta je da kayan barka masu matu ar yawa, da su yajin jego, da kayan amfanin mai jego. Mama Sa'adatu ma kaya ta kawo mata masu matu ar yawa harda lace da atampa. Haka Mummyn su Salma kowa ya yi mata kyauta wacce ta saka Didi zubar da hawaye saboda farin ciki. Nayla kayan da ta kai mata sai da Didin ta dinga fa a tana cewa bazata kar a ba sun yi yawa da yar dai ta amince ta kar A ranar litinin Nayla ta auki hutu saboda Mama ta ce ta auka saboda shirin da suke yi. Gyaran jiki Mama ta ke ta yiwa Nayla, kasancewar ta fara cikin kwana biyu ta sake yin haske da kyau fatar ta ta sake yin laushi sosai. Har lokacin babu maganar da ta sake ha ata da Omar, duk ta damu tana ganin kamar daman baya so ta dawo. Shi kuwa ya bada lokacin ne kamar yadda iyayenta suka ce, sai dai ya kai result in gwajin jinin kamar yadda Daddy ya ce masa. Kuma da ya je kai musu ya sake samun tarba mai kyau a wajan Daddy har sai ya yi mamaki sosai, sai dai Daddy ya ce masa ya ara ha uri Nayla zata dawo in sha Allah. Haka aka yi sunan ar Didi wacce ta ci sunan mahaifiyarsu ake yi mata la abi da Marmerh. An yi shagalin suna sosai, Didi ta zama ar gata domin dangi na ko wanne angaren sun zo an yi shagali sunan Marmerh. Marmerh kuwa kayan da ta samu daga haihuwar ta zuwa suna Didi bazata iya lissafa su ba, ta samu kaya da ku i da atamfofi. Har lokacin Omar bai sake zuwa gidan ba, amma kullum sai ta tura masa hotunan Marmerh dan a yanzu hoton ta ne ma akan screenlock in wayarsa. Yana matu ar son yarinyar kamar shine ya haifeta haka yake ji, ya kan tsaya yana kallon hotonta kawai yana murmushi. Washe garin sunan yana zaune yana duba wayarsa kawai hannunsa ya kai kan status in Didi. Ya ga hotunan suna ne na jiya ta saka, ya dinga bi a hankali yana gani yana ya ta e baki saboda ganin danginsu wanda baya aunar gani. Har ya wuce ya dawo ya sake wara idanunsa yana kallon Nayla ta yi murmushi tana ri e da Marmerh a hannun. Ajiyar zuciya ya yi ya zuba mata ido yana gani yana murmushi shima. Screenshot hoton ya yi sannan ya fita daga WhatsApp in ya kira Didi a waya. Tana auka ya ce, "Didi ki goge hoton da ki ka saka a status yanzu, ta ya zaki auki hoton matata ki saka a duniya tana gani? Ki goge yanzu sai mu yi magana." Yana fa a ya yanke wayar. Ba jimawa ya sake kira ta ce, "To Omar na goge." "Na gani. Kar ki sake ora hotonta a status. Ina Marmerh?." "To ubana. Ga Mamerh tana bacci a kusa dani." "Ki shafa kanta a madadina, zan zo na ganta." Didi ta yi murmushi ta ce, "To sai ka zo, tunda dai kana ta cewa zaka zo baka zo ba." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba Didi ta ce, "ya dai?." Omar ya ce, "dama ta zo gidanki jiya?." Didi ta ce, "kaima ka san ta ya za a ce bazata zo sunan Marmerh ba?." Ya girgiza kai cike da jin haushi ya ce, "tana ta zuwa inda take so ba tare da izinina ba." Didi ta yi murmushi ta ce, "To ai ita kaga...." aramin tsaki ya yi ya ce, "kar ki kira abinda zai ata min rai don Allah." Didi ta ce, "shikenan Omar, amma yanzu ya ake ciki da maganar?." Omar ya ce, "Ina gab da kasa jurewa Didi, na yi ha urin, nayi juriyar amma abin yana neman yafi arfina." Didi ta ce, "ka kira ta a waya?." Ya girgiza kai kamar tana gabansa ya ce, "tunda aka ce na bata lokaci shine na bayar, bana son yin abinda za a ga rashin kyautawata shiyasa ni ko waya ban kira ta ba." "Kana kewarta sosai ko?." "Fiye da yadda zan fa a miki Didi, ban san me zan ce miki ki gane ba." Didi ta ce, "to ka je gidan ka same ta mana." "Didi ban son na je ayi min wani abun raina ya aci wani abun ya faru, a karo na farko ina gudun acin raina a wani waje." "Ranka bazai aci ba in sha Allah, ka je ka sameta." "Didi gaskiya bazan je ba." Didi ta ce, "to ai shikenan, sai ka cigaba da jiran tsammani" ta fa a dan ta san bazai iya jurewa ba. Katse kiran ya yi ya nemo number Nayla da har lokacin bai yi saving ba, ajiyar zuciya ya yi kawai ya kira number. Nayla a lokacin tana zaune an gama turara mata jiki kenan ta ga ana kiranta, kamar baza ta auka ba sai kuma ta aga ta ce, "Hello." Shiru ya yi bai amsa ba jin saukar muryarta har cikin walwarsa. Tsaki ya ji tayi ta katse wayar ya kifa wayar a kirjinsa yana lumshe idanunsa. Nayla tana katse wayar Mama ta shigo akin ta kalle ta ta ce, "Daddy yana ta fa a wai kin yi shiru, na ce masa kin amince kawai muna an gyare-gyare ne, yana ta fa a ya ce ki koma a wannan satin." Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama ta ce, "Ko baki son komawa ne?." Nayla ta yi shiru Mama ta ce, "Nayla fa a min abinda yake ran ki, kin ce kin amince amma yanzu ina ganin kamar baki son komawa." Nayla ta ce, "Mama har yanzu ko waya bai sake yi min ba balle ya zo, Ina ganin kamar baya so na koma." Mama ta yi murmushi ta ce, "Yana so mana Nayla, dan bai yi miki waya ba ko bai dawo ba ba hakan yana nufin baya sonki ba. Tunda har yaje gaban iyayenki yana sonki wallahi, wata ila bai neme ki ba saboda lokacin da aka ce za a baki." Nayla ta ce, "Mama ni sai nake ganin kamar baya so ne kawai." Mama ta shafa kanta ta ce, "Kar ki damu yana sonki, yana kuma so ki koma da ra'ayin kan ki ba dan tilastawa ba." Nayla ta goge idanun ta bata ce komai ba. Da yamma Salma da Jidda suka zo gidan suka dinga rarrashinta amma ta kasa fahimta ita gani take yi kawai ba sonta yake yi ba tunda bai neme ta ba. Salma ta ce, "kema kin cika rigima wallahi, kin san halin mijin nan naki meye zai dame ki? A ganina ai tunda har ya kalle ki ya ce bazai sake ki ba, sannan ya fa a a gaban su Daddy me zai dame ki kuma?." Nayla ta ce, "gani nake kamar...." Jidda ta katse ta ce, "Haba me ki ke so ya yi miki kuma? Ke ki ka ce sai an baki lokaci, an baki lokacin kuma kin damu." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba. Wayar ta ce ta yi ara ta duba ta ga number ce sai kawai ta auka ta saka a speaker ta ce, "Hello." "Ina cikin gidan da ki ke, zan iya ganin ki?." Gabanta ya fa i ta kalli su Jidda da suke kallon ta ta ce, "waye ya ke magana?." "Ki zo zaki gani" yana fa a ya yanke wayar Nayla ta bi wayar da kallo. Sai kuma ta yi ihu ta fa a jikin Salma suka rungume ta Jidda ta ce, "Wai ke nufin ki Omar in ne?." Nayla ta ce, "wallahi shine Twiny, ko a mafarki zan gane maganarsa." Jidda ta ce, "to ga abinda mu ke fa a miki ya tabbata." Murmushi ta yi tana goge idanuta. Salma ta ce, "ya aka yi ya san kina gidan nan? Sananan kuma ya aka yi ya san gidan nan?." Nayla ta ce, "ban sani ba." Jidda ta ce. "yanzu dai a fa awa Mama zuwansa sai ki je ki sha kalaman soyayya ki dawo." Murmushi ta yi ta kalli Mihada da take gefe tana bacci ta shafi fuskarta. Salma ce ta fa awa Mama batun zuwan Omar ta aika ta ta ce taje ta shigo dashi. Salma ta yi mamaki gani sa a mota a zaune a wajan gate in gidan dan bai shigo ba.