← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 205

Sashe 130

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka take zama ta lalace a video call dashi ko gajiya da wayar basa yi, kewar junan su na sake damun zuciyarsu. A cikin garin Kano aka fara events na bikin Salma, Nayla itace kan gaba komai tare ake yi da ita sai Jidda da ta shigo ciki, Sune annen Ango kuma awayen amarya. Tun daga kan masu henna, da masu kwalliya duk tare ake yi musu, Nayla dai iya ba in henna tayi iya hannu ta ce baza ta yi ba sai mijin ta zai dawo suka dinga tsokanarta. An yi kamu, an yi dinner aka aura aure ranar Friday, ranar Saturday aka tafi da amarya garin Kaduna. A can Kaduna ma wani bikin aka sake yi, Nayla sai zirga-zirga take itace wajan ango itace wajan amarya. Kowa in ya ganta sai ya yi dariya ya jinjina mata ana tsokanarta anwar ango awar amaryar, gashi ta yi kyau ta sake yin haske sai aka dinga tunanin ciki ne da ita. Mama ma ta auka ciki ne da ita, shiyasa take hanata wani yawo, sai da ta tambayeta ta ce ita bata da komai sannan ta yaleta. Amarya bata je gidanta ba sai ranar lahadi da daddare, su Nayla ne yan rakiyar amarya ita da Jidda da Ummimi. A tsakiya suka saka Salma suna ta tsokanarta tun tana yale su har ta fara basu amsa, sai da ango ya shigo sannan suka dawo gida ita da Jidda cikin farin ciki. Biki ya watse kowa ya koma gida ana huta gajiya, Nayla ma ta sha baccin gajiya, kiran wayar mijinta ne ya tashe ta a firgice ta duba ta ga video call ne. auka ta yi ta kalle shi ta ce, "good morning Rouhii!." are mata kallo yake yi dan kayan bacci ne a jikinta, rigar mai aramin hannu kuma bata da kauri sosai sannan bata saka komai ba sai rigar kawai dan haka ana iya ganin jikinta. Ganin ya yi shiru yana kallon ta sai ta kalli abinda yake kallo ta kalle shi sannan ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na yi kewarki Ashiq, ni ka ai na san halin da nake ciki da bakya tare dani, Kin san dai halin mijinki, mayenki ne." Nayla ta yi kasalalliyar dariya da ta saka Omar ya lumshe ido ya ce, "Kina sake kashe min jiki Jidda, kar ki saka ni kuka mana." Ta wara ido ta ce, "wace ni na saka YaMar tiger kuka? Sai daina saka shi farin ciki." Murmushi ya yi ya ce, "kuka na nawa kuma? An ce da kare ya sunanka ya ce na nawa kuma?." Dariya ta yi sosai shima dariyar ya yi ya ce, "ko ba haka ba ne?." "Ni dai babu ruwa." "Yanzu rufe jikinki in ya so sai mu yi magana, in ina kallonki a haka akwai matsala." i tayi ta shagwa e fuska tana kallonsa ya auke ido ya ce, "Jidda ki yi abinda na ce, Allah zan rasa nutsuwata, ki taimaka min. Kar ki saka aljanuna su tashi gashi bakya kusa balle ki yi min ru iya." Dariya tayi sosai sannan ta ja bargo ta rufe jikinta ya kalle ta ya ce, "Wai waye ya saka ki yi wannan shigar?." "Gajiya na yi sosai, wannan in ma a cikin kayana na nemo ta." "Amma wannan kayan da zaki saka a gida ba ne, akwai an biki, ko wata ce ta ganki a haka ai ta cuce ni." Nayla tayi dariya ta ce, "yanzu zan yi wanka." "Ya gajiyan biki?." "Bari kawai Rouhi, na gaji sosai." "sannu, ai dole ki gaji, awar amarya anwar ango." Dariya ta yi ka an tana kallonsa ta ce, "ni ko ina dani a wannan bikin. Yau baka je kasuwar ba?." Ya aga mata gira ya ce, "zan je sai anjima, akwai da wanda mu ke zuwa tare." "Allah ya taimaka ya dawo min da kai lafiya." "Amin. Na agu na dawo nima wallahi, duk na gaji da zaman." "Nima na gaji da zama baka nan." "Hmmm Kamar gaske." "Da gaske mana, in ka dawo zan tabbatar maka da na yi matukar ewar ka." Murmushi ya yi bai ce komai ba ta ce, "kasan meye?." Ya girgiza kai alamun a'a ta ce, "yau na tashi da azumi, rabona da azumi har na manta, tun dai wanda muka yi tare guda uku nida kai." Omar ya ce, "ki yi abinda ki ke so kafin na dawo." "Don Allah meyasa baka so na yi azumi?." "Akan me zance bana so ki yi ibada? Kawai bana so a shigar min lokacina ne. Ina so na kasance dake kuma ga azumi, kinga akwai shiga ha i, maimakon ki samu lada sai ki kwashi zunubi tunda ba azumin farilla bane. Ina ta a ki zaki ce azumi ki ke yi, to akan me nida ha ina kuma matata mallakina? Shiyasa gwara ki ha ura kawai." Dariya tayi zata rufe fuska ya ce, "kina rufe fuska zan kashe wayata, a wayar ma kunya ki ke ji?." Dariya ta yi sosai har ya shagala da kallon ta kafin ta ce, "Daman Didi sai da ta fa a min, ta ce da yar in baka hana ni azumin litinin da alhamis ba, nayi-nayi ta fa a min dalili ta i, ta ce na jira na gani in har ka hana in zan fahimta, gashi kuwa na gane." "Ta san aninta bai yi kama da mai ha uri ba, ta san aninta yana da ulafuci akan abinda yake so. Inda zan iya zan barki kiyi ai lada zaki samu, babbar matsalar indai zan barki kiyi sai dai in na fita tun safe baza ki ganni ba sai kin sha ruwa. Dan in muka ha u, in idanuna ya fa a cikin naki ke kan ki baza ki san kin karya azumin ba. To me ya yi zafi? A dinga karya azumi da gangan? Maganin kar a yi kar a fara. Baazan iya ba, ji zanyi kamar za a zare min rai daga jikina. Ya za a yi na iya tsallake dadda an yanayin nan na bayan sallar asuba?." Dariya tayi sosai tana rufe ido ta ce, "kana bani kunya Rouhii." "to arya nayi? Ke kan ki lokacin baya burge ki don Allah? Ki fa i gaskiya banda arya, aljanun da suke tashi a lokacin na san baza ki so a shiga ha insu su i tashi ba." Bata ce komai ba sai fuska da ta rufe ya yi aramin tsaki ya ce, "komai kunya, zan kashe wayata in baza ki bu e fuska ba." Nayla ta ce, "Kana adawa da wannan kunyar tawa, ni kuma ba ni nayi kaina ba." "Kunyar ta gulma ce ai, inda ya kamata tazo bata zuwa. Ki tuna daren za zan yi tafiyar nan mana, mantawa ki ke yi da kunyar, sai daga baya ki fara rufe min fuska." Ido ta rufe tana dariya suka cigaba da hira cikin nisha i da soyayya. KRB3P079 Nana haleema Narma ta kammala idda amma har lokacin bata walwala kamar da, iyayenta sun auka tunda ta gama idda zata dawo kamar baya amma sai suka ga akasin haka har lokacin ware kanta take yi a cikin su. Suna zaune a falo gaba aya har da Yayansu Dad ya kalle ta ya ce, "Narma wai meye matsalarki ne? Na auka da kika gama idda zaki dawo kamar dah kina walwalarki sai na ga akasin haka. Me ki ke so ne?." Narma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Abinda nake so ba samu zan yi ba shiyasa gwara na yi shiru kawai." Mum ta ce, " an daban nan ko?." Narma ta ce, "Mum sunansa Omar, Omar sunansa ba an daba ba." Mum ta ce, "na rasa me ya shiga kanki, ina ke ina wannan yaron?." "A haka nake sonsa! A haka nake so na rayuwa dashi Mum. Shekara aya kenan da ku ka raba ni dashi, amma zuciyata har yanzu tana tare dashi. Matu ar baku amince min da aurensa ba baza ku ta a samuna a yadda ku ke so ba. Yadda na bi abinda ku ke so na auri Ashraf, ku ma ku yi min adalci na aure shi!." Dad ya ri o hannunta cikin rarrashi ya ce, "yi a hankali my love, ke yanzu kin san inda Tiger in yake? Kuma kina da tabbacin zai kar e ki?." "Indai zaku amince na aure shi zan nemo shi a duk inda yake, kuma zan tabbatar da na dawo da soyayyata a cikin zuciyarsa. In kuma ba ku amince ba zan iya barin gidan nan na koma Kano na rayu dashi." Jin abinda ta ce Nabil Yayanta ya ce, "Baki da hankali." Dad ya dakatar dashi ya kalle ta ya ce, "Narma yaron nan ba type inki bane, na rasa abinda ya shiga kanki kika kasa fahimtar matsayin da ki ke dashi. Mahaifinki fa takarar governor yake yi, meyasa zaki dinga cewa kina son wanda ko makaranta bai yi ba?." "Dad!.....A haka nake sonsa, a haka nake so na aure shi, in zaku bani dama ku bani, in baza ku bani dama ba wallahi in na tafi baza ku sake ganina ba. Na gaji, na gaji da wahalar da zuciyata da ku ke yi, na jure a lokacin baya, amma a wannan lokacin bazan ta a iya jurewa ba. Ko ku yarda, ko kar ku yarda zan auri Faruk ko bakwa so!" Ta fa a tana fashewa da kuka mai sauti. Najwa ta kalli iyayen ta ce, "Mum, Dad, Yaya, don Allah ku yaleta ta aure shi, tana sonsa, tana aunarsa meyasa baza ku amince ba?. Kuma shi wanda ku ke cewa type inta ne ga abinda ya aikata mata, Inda tun farko ta auri Omar in da hakan bai faru ba" ta fa a tana tasowa ta araso inda take ta rungume Yayarta. Mum ta kalli Dad bata ce komai ba ta tashi ta hau sama. Dad ya kalli Narma ya ce, "Kar ki damu Narma, zan yi tunani a kan hakan, Ina zuwa" ya fa a yana bin Mum sama. aki ya same ta ya ce, "Sai muna yi mata a hankali, kin manta Dr ya ce a daina saka ta a damuwa?." Mum ta ce, "tana maganar auren an daba ne fa, tana maganar in ba shi ba zata bar gidan nan, ya
Chapter 130 · 0% Book details