← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 205

Sashe 22

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kayan aiki suna jira ka ce wani abun. Tsaki ya sake yi ya fita zuwa wajan dan ganin abinda yake faruwa, yana fitowa ya ga matasa da makamai an taru ana jira ya fito, yana fitowa suka fara hayaniya wannan yace wannan wancan ya ce wannan. Gab aya baya fahimtar abinda ake fa a hakan ya saka ciki cikin tsawa ya ce, ya isa! Ya isa!. Duk suka yi shiru ya kalle su ya ce, ban ce kowa ya yi wani abun ba, ban ce kowa ya aikata wani abun ba. Kar wanda ya yi musu komai, a bari hukuma tayi aikin ta. Ina sake maimaitawa, kar wanda ya auki doka a hannunsa. aya daga cikin matasan ya ce, Madugu har gida fa, har gida suka zo aka yi mana ba daidai ba kuma ka ce mu bari?. Kaima wasa ka ke yi baza mu yale su ba wallahi. Ranmu fansa ne a gare ka Damisa, zamu iya atawa da kowa mu shirya da kai wallahi. Omar ya ce, ni dai na ce kar wanda ya yiwa kowa wani abun, in kuma ba haka ba duk wanda ya aikata sa anin abinda na ce zai ha u da fushina mai yawa. Kowa ya wuce ya tafi ya yi alwala ya tafi masallaci ya yi sallah. Wani zai sake magana cikin tsawa ya ce, Na ce ku bar nan ko!. Dukkan su barin wajan suka yi ya kalli su Bash ya ce, ban ce kowa ya aikata wani abun ba, haka zalika ban bawa kowa umarnin tura wasu su yi wani abun ba, ku yale ni ni nasan matakin da zan auka. Tk ya ce, Amma Damisa Shiru! Na ce a yale ni ya fa a a tsawace yana kallon sa dole ya yi shiru suka fita shi kuma ya koma ciki. Kamar ya shiga akin ya duba ta amma sai ya fasa ya yi zaman sa yana ka afa cikin acin rai mai yawa. Wai shi za a zo har gida aka yiwa wannan wula ancin, in ba dan kura tayi lafiya ba ai da gobe garin Kano an wayi gari jini ya ata ko Ina, azumin gobe jama ar Kano da jini zasu sha ruwa. Babbar sa ar da suka yi Omar in dah dana yanzu akwai banbanci, in ba dan haka ba da duk sai dai iyayensu su haifi wasu, koda bai auki mataki da kansa ba za a aukar masa. A bayyane ya ce, ko ya ya kayi arin zama mutumin kirki sai an yi abinda za a saka ka koma na banza. Tsaki ya yi ya fita yana kallon gate in ya mayar ya rufe dan ba alla shi suka yi duka suka yi masa har lock in ya zare. Ko key bai saka ba ya dawo ya zauna a kan kujera yana ka afa yana tunanin irin hukuncin da ya kamata ya yi musu. Yana wanna tunanin ya ga arfe uku na dare ta yi ko ina sallah ake yi. Kawai sai ya tashi ya yi alwala shima ya tayar da ta sa sallar. Nayla kuwa baccin wahala ta yi alarm in wayar ta ne ya tashi ta, ta tashi da nauyin jiki da ciwon kai daman dashi ta kwanta gashi tayi kuka kuma bata samu baccin kirki ba, alawala tayi ta tayar da sallar tahajjud. Washe gari sai arfe goma na safe ya tashi, kasanacewar juma a ce manyan kaya ya saka ya fita, kai tsaye police station in da ya saka kai yaran ya wuce. Da yake Dpo da suka saba ne suka tattauna ya ce masa za a auki mataki mai arfi, zuwa ranar monday za a tura su kotu bisa tuhumar tayar da fa a har cikin gida al ali yanke musu hukunci. Omar ya san za a yi hakan shiyasa bai damu ba ya wuce zuwa shago. Kowa mamakin ganin sa yake yi kuma ba a ji wani tashin hankali ya sake faruwa ba, kowa mamaki yake yi da labari bai zagaye gari ana cewa Tiger ya mayarwa da kura a niyar ta ba. Duk inda ya wuce kallon sa ake yi yana kuma sane da kallon da ake masa kawai babu wanda ya isa ya tunkare shi da maganar ne sai dai kallon kawai. Nayla ranar bata je aiki ba ita da aiki sai ranar monday, tana zaune kiran Didi ya shigo wayar ta tana auka a gigice Didi ta ce, Nayla lafiya ki ke dai ko? Na ji labarin abinda ya faru jiya. Ina fatan dai kina lafiya?. Nayla a kasalance ta ce, Lafiya lau Didi, Amma a tsorace nake sosai. Ina Omar in?. Ni ban sani ba ta fa a murya na rawa sosai. Ki nutsu Nayla, babu abinda zai same ki. Bara na kira Omar in naji abinda yake faruwa ta fa a tana yanke wayar. Nayla tayi ajiyar zuciya har lokacin zuciyarta bugawa take yi dan bata ta a ji ana cewa za a yi kisa a zahiri ba sai dai a film. Abu na social media nan da na labari ya zaga ko Ina da ko wanne gari. Arewa bloggers suna ta rubuta an kaiwa Omar Tiger babban an daba mai murabus hari har cikin gidan sa ana yi yun urin kashe matarsa. A can Madina a lokacin Mama tana zaune bayan sun dawo daga sallar juma a suna zaune ita da Abiy sai ga yaran nasu gaba aya sun shigo akin Abiy gashe shi. Suna zaune ana hira Mama ta auki waya tana dubawa. Mama ta ce, Innalillahi wa inna ilaihir raji A tare duka suka kalle ta a gigice jin salatin da tayi Abiy ya ce, lafiya?. Mama ta kalle shi ta kalli wayar ta ce, Jiya da daddare an kaiwa babban an daba na jahar Kano mai suna Tiger hari har cikin gidansa, an yi yun urin kashe matarsa Allah ya ta aita Mama ta fa a cikin sigar karanto musu abinda yake da rubuta. Jidda ta ce, Innalillahi wa inna ilaihir raji un! Mama Twinny! Ta fa a a gigice tana wara idanu waje. Mama a ru e ta ce, ku kira mana wayar ta da hanzari don Allah. Yaya J da Yaya Ahmad da Jidda har rige-rigen kiran wayar Nayla ake yi cikin tsananin tashin hankali. Abin haushin gaba aya basa samunta sai kira ake yi amma bata shiga. Yaya J yayi tsaki ya ce, Ba a samun ta a waya. Abiy ya bisu da kallo ganin duk sun ru e su ga masu ar uwa, ya yi dariya ya ce, meye duk ku ka tashi hankalin ku haka? Abinda ta aura kenan daman, kuma kun san haka zata iya faruwa ko yaushe, to meye na aga hankali kuna salati haka?. Yaya ya ce, Abiy batun kisa ake yi fa, kisa fa. Abiy ya auke kai bai ce komai ba. A lokacin Jidda ta same ta WhatsApp call tana auka ta saka a speaker ta ce, Twiny lafiya ki ke dai ko? Yanzu mu ka ga abinda ya faru jiya a social media, kina lafiya?. Nayla a sanyaye ta ce, Lafiya lau nake Twiny, babu abinda ya same ni. Kin tabbatar? Ya na ji maganar ki haka kamar kin yi kuka?. Bani da lafiya Twimy, stress na aiki ya saka ni a gaba ga azumi, kullum a wahale nake yini saboda gajiya ga ciwon kai. Ina Abiyna? In kin je akinsa ki ce ina gaishe shi ina yi masa barka da juma a. Na yi masa missed call bai auka ba. Jidda ta kalli Abiy da ya duba wayarsa bayan ya ji abinda Nayla ta ce sannan Jidda ta ce, Yana jin ki, muna tare gaba aya Mama ta ga abinda ya faru. Kuma babu wanda ya kula a cikin mu sai yanzu, da wani abun ya same ki tun a jiyan da sai yanzu zamu sani. Yaya J ne ya ce, Nayla kin tabbatar lafiya lau ki ke ko?. Nayla ta ce, Lafiya lau Yaya J, Ina Yaya?. Yaya Ahmad ya ce, Nayla gani nan, gaskiya baki da lafiya Nayla? Gaba aya voice inki ya canja, sannu kin ji, ki samu ki je asibiti a baki magani. Yaya Strees ne kawai wallahi, yau kuma da yake ban je aikin ba ma Ina gida bana ji da in jikina. To sannu, Allah ya ara lafiya, Allah ya kiyaye gaba. Ki yi magana da mijin na ki gaskiya a san matakin da za a auka, bazai yu shi da aikata laifi hukunci da arin shafar ki ba. Nayla ta ce, to Yaya. Ina Anty Halisa da Amma?. Sun shiga masallaci ita da Jalila, Amma kuma gata nan a wajena. To Yaya a gaishe su, a gaishe da Mama da Abiy. Mama sai a lokacin ta ce, Nayla kina lafiya dai ko?. Tayi murmushi ta ce, eh Mama lafiya ta lau, ki gaishe min da Abiy. Abiy jin tana ta ambatar sunansa sai ya ji zuciyarsa tayi rauni ya ce, Mamana ya ibada?. Nayla jin muryar Abiy da hanzari sai ta ce, Abiy barka da Juma a, ya ibada?. Alhamdu lillah Mamana, yanzu na ga kiran ki na je masallaci. To Abiy. Allah ya amsa ibada. Amin ya fita daga nan bai sake cewa komai ba. Jidda suka yi sallama ta kashe wayar. Kafin wani ya sake magana a cikin su Abiy ya ce, Ku bani waje zan huta kafin lokacin sallah. Duk suka mi e suka fita tare da jan ofar,bayan sun fita ya kalli Mama da take hawaye ya ce, lafiya?. Ta goge ido ta ce, Irin zargin da ake yi min akan auren Nayla da abinda ake fa a a kaina ne yake karya min zuciya. Yanzu tsakani da Allah meye amfanin auren irin wannan mutumin? Gashi tun auren bai je ko ina ba an fara neman rayuwarta akan abinda bata san ma anyi ba. Ni ban san Nayla wacce irin yarinya ba ce da ta nace akan wannan banzan mutumin ba wallahi, ka duba yanzu tambayarta ake yi amma sai maimaita lafiya lau take yi, kar ma ta ce ba lafiya ba ace za a raba su kenan ko?. Abiy ya ce, to waye ya ce zai raba su?. A yanayin Yaya da Jawad tsaf zasu iya raba auren nan in wani abun ya same ta. Shine
Chapter 22 · 0% Book details