← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 205

Sashe 162

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mutum kenan, tunda da ya ce kallon dabba yake masa, ya ce ma gwara dabba akansa. Yanzu ya tashi daga jahili kenan ya dawo mai ilimi tunda gashi a zaune a cikin office insa yana kallonsa yana fa a masa ya auri arsa, yanzu ya tashi daga wanda bai zai kaiwani mataki a rayuwarsa ba ya dawo mai matsayi a idon sanata. Soyayyar da ake i irarin yayi asiri yanzu ta dawo ta gaskiya tunda gashi ana cewa ya aure ta. Omar ya dinga binsa da kallo yana tuna abinda ya faru a baya, hakan ya saka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. In ba dan ma yana so ya nuna masa banbancin da da yanzu shi ya isa ya iya ha a ido dashi?. Sen ba tare da jin nauyi ba ya ce, "Gab take da kamuwa da heart attack Omar, ka amince da ita ka aureta zata zama matarka ta biyu, dan ta zo a sencond wife inka ba wani abun damuwa ba ne." Omar ya girgiza kai cikin dubun mamaki, ya yi wani irin murmushi na rainin hankali ya kalle shi ya ce, "Sen Sagir Sani Shatima, yau kaine ka ke neman alfarma a wajan Omar? Ka manta waye Omar ne a wajanka?." Sen ya ce, "ka ji na ce komai ya wuce ai, ni dai burina ka amince ka auri Narma please ." Omar ya jingina da kujerar office yana an motsawa a hankali tana juya shi ka an-ka an ya ce, "to abin ne yake bani mamaki, ka manta kace dabba ta fi ni wajan ka? Ka manta kace ko a mai gadin gidanka bazan zo ba balle sirikin ka?. To ya aka yi aka haihu a ragaya? Ko dai atan kai ka yi kazo wajena? Dan na san ba ni Omar in ka ke nema ba." Sen ya yi shiru bai ce komai ba Omar ya ce, "Wannan Omar in ba shi da ilimin da zai auri arka, arka tana matakin masters ko? arka tana juya ku in masu yawa ko? arka tafi arfina sai dai na zo a mai gadinta ko?. Ina so ka tuna wannan Omar in fa ko takardun secondary bashi dasu har gobe, kai da kan ka ka ce baka aukar mutum aiki a gidanka sai yana da takardar digree ko masters, to ya aka yi ka ke so ka bawa arka jalihin mutum irin Omar?." Sen ya ce, "Please Omar! Abinda ya faru ya riga ya wuce, ka manta mu kalli abinda yake present a yanzu." Omar ya sake yin murmushi ya ce, "Shine nake mamaki ai Sen Sagir, ta ya zaka amince ka bawa arka wanda babu matakin rayuwar da zai iya kai wa?. Ka ce wanda ba shi da ilimi babu inda yake zuwa sai dai rayuwarsa ta are a kan titi kuna cigaba da amfani da rayuwarsu wajan gina ta ku rayuwar da ta anku. Shine amfanin mu kawai a wajanku, ya aka yi ka zo kana son irin wannan namijin ya auri arka?." Sen ya yi ajiyar zuciya yayi ya ce, "Omar ka daina wannan maganar, yanzu magana ake ta ceton rayuwar yarinyata, tana sonka, tana aunarka, tana so ya rayu dakai a matsayin mijinta. Na amince ka aure ta ko dan ceton rayuwarta." Omar ya yi murmushi yana kallonsa yana girgiza kai cike da mamakin an adam ya ce, "Senator Sagir Sani Shatima kenan...." ya sake yin ar dariya ta rsinin hankali ya ce, "tambayarka nake so na yi." Ya kalle shi alamun ina ji, Omar ya ce, "waye ni?." Sen ya ce, "Omar mana." "Ina nufin waye ni..Kai ba Senator ba ne? So nake ka fa a min ni waye kamar yadda ka fa a min a wancan lokacin." Sen ya ce, "Omar ne kai, C.E.O Exclusive Footwear." Omar ya yi murmushi yana girgiza kai ya ce, "A'a, Tiger ne wannan, an daba, an shaye-shaye, mara aikin yi, wanda yayarsa take aukar awainiyar rayuwarsa saboda ya gaza. Mara ilimi ne, jahili, wanda ya yiwa arka asiri, wanda bazai je ko ina a rayuwa ba, Ko ba haka ka ce ba?." Sen ya yi shiru bai ce komai. Omar ya ce, "Haba Sen, yanzu shi ka ke so kace zaka aurawa arka? Ko dai ka yi atan hanya ne kana neman wani Omar in ba ni ba?." Nan ma ya yi shiru bai ce komai ba. Omar ya aure fuska sosai, ya canja daga lokacin fara'a ya dawo lokacin rashin mutumci ya ce, "Alhaji Sagir zan ce ko Malam Sagi..?" Ya sake girgiza kai ya ce, "ina so ka sani ba lallai sai kana da ilimin boko zaka kai wani mataki a rayuwarka ba, meye ilimin bokon....? Turanci ko?. Ina so ka sani akwai masu Digree da masters in da ka ke ta ama dashi a ashina a cikin wajan nan, ni da ka ke kallo bani da ilimi ni ne nake biyansu albashi a duk wata. Ni in dai da kake kallo matsayin wanda ba zai je ko ina a rayuwa ba ni ne dai na kai matakin da kai baka je shi ba. Ba kai ka ai ka ta a yin senator a Nigeria ba, amma ni ni ne ka ai akan matakin babu wanda ya ta a kaiwa a kaf africa ba nigeria ka ai ba, duk wanda zai samu matsayin da na samu a yanzu a bayana yake, ko babu komai sai an ce ai Omar ne ya fara kafin wannan. Ko a iya haka Allah ya bar ni Alhamdu lillah, ya gama yi min komai a rayuwa, balle kullum sake cigaba nake yi." Omar ya an yi murmushi ya nuna shi da ya yatsa ya ce, "Dama ba nace ka kasance a raye ba? Ka auka wasa nake yi ko?. To gaka da rai a gaban Omar a zaune ka zo neman alfarma..." ya fa a yana girgiza kai yana smilling. "Kazo aurawa Omar arka amma ka hana Tiger arka saboda kana kallonsa a ance ko?. Ina so na fa a maka wani abu Sagir, arka Narma bani da bu atarta a cikin rayuwata, ta je ta auri daidai da rayuwarta mai ilimi wanda yake ri e da babban compony kamar dai ita. Ni ka bar ni na cigaba da rayuwata da wanda suke daidai ni ita taje tayi rayuwarta. Bani da bu atarta a cikin rayuwata, ta shigo rayuwata ne dan ta jani na je gidanka ka fa a min maganar da raina zai aci na zubar da shashancin da nake yi a baya. Amfanin Narma kenan a rayuwata, kuma in na tuna da hakan ina gode mata har a zuciyata amma ba dan ina kallonta da wani matsayi ba. Ban ta a son arka ba, ta zama silar amsa kiran rabo na ne shiyasa har amince na je gidanka ba tare da na tantance soyayya da burgewa ba. Dan haka kar a sake zuwar min da wannan maganar, bani da bu atar aurenta kuma bazan yi ba, ta samu daidai ita ta aura!." Sen Sagir ransa ya kai arshe wajan aci, mamakin Omar yake yi da yake fa a masa magana kamar bai san matsayinsa ba. Ya kalli Omar ya ce, "Dan ma ka samu kamar ni na zo ina yi maka zancen ka auri yarinyata shine ka ke fa a min magana?." Omar ya sake aure fuska ya ce, "shiyasa nace ka bar ta bani da bu ata, a kai kasuwa in tallanta ka ke yi, ni baza ka samu damar na taya ba balle har na siya. Meye ma sunanka......Sagir ko? Ina so ka sani a office in Omar ka ke, ka san irin maganar da zaka fa a min, kar ka ja raina ya aci na nuna maka asalin waye ni yanzun nan. Bana son hayaniya, dan haka bismillah..." ya fa a yana nuna masa ofa ba tare da ya kalle shi ba. Sen ya girgiza kai cikin acin rai tare da yin wafa, zai fita kenan Omar ya ce, "ka je ka samu a karya asirin da na yiwa arka, dan bazata ta a samun Omar ba koda zata mutu. In ta mutu bani da asara, asara kai ta kama bani ba." Sen ya girgiza kai ya fita daga office in ransa a ace. Omar tsaki ya yi, ko ka an babu acin rai a tare da shi, babu komai a zuciyarsa a haka ya cigaba da harkokinsa. P100 Omar bai jima an office in ba ya koma gida, sai ya tarar ana ta aikin naman suna, an aiki suna ta aiki ya yi mamaki dan shi ya auka an gama. Ta baya ya shiga har samansa ba tare da kowa ya ganshi ba. Farin ciki yake ji a zuciyarsa sosai, ko babu komai yau Allah ya nunawa Sanata in ya yi nufin yiwa bawansa abu babu wanda ya isa ya hana, Allah ya nunawa masa shima yana da tasa baiwar, akwai kuma inda yake da warewa a kai wanda shi bashi da ita. Gashi shine ya zauna a gabansa yana neman alfarmar ya auri arsa, ko a yanzu Allah ya auki ransa ya gama yi masa komai. Nayla ta ga dawowarsa, daman ta yi kwalliya cikin material tayi aurin ankwali tayi adon gashi a baya, in ka kalle ta baza ka ce itace ta haihu ba saboda yadda jikinta yayi kyau ya kame waje aya. Falon nasa ta shiga da sallama hannunta auke da plate ta ajjiye akan table ta ce, "YaMar sannu da zuwa." Jin maganarta sai ya juyo yana kallon ta, ta bai san ya zuba mata ido ba saboda yadda kayan suka yi mata kyau, gashi dai basu nuna jikinta ba amma sun yi mata bala'in kyau, sun haska fuskarta. Kai ya aga mata bayan ya janye idonsa daga kanta, ta an tura masa plate in soyayyen naman da yake ta hamshi yake yi ta ce, "Ga naman suna." Kallon plate in ya yi yaga harda yaji a gefe ya auke kai ba tare da ya auka ba, abinda bai dame shi ba kenan shi a rayuwarsa, da rayuwar nama da babu duk aya ne. Komawa ta yi ta kawo masa lafiyayyen zo on mai sanyi wanda tayi order a wajan leemars_delicous a jug, ta zuba masa a glass cup ta ajjiye masa ta ce, "ka ci naman
Chapter 162 · 0% Book details