← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 205

Sashe 153

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayla ta ce, zaki ci abinci ko sai kin tashi daga bacci?. Didi ta ce, bana jin yunwa Nayla, ba na son cin komai. A gajiye ki ke Didi, na san kina jin yunwa. Rouhii bara na sauka asa na siyo mata tea. Hannunta ya ri e yana kallon ta ya ce, babu inda zaki je, kema ai kina bu atar ki huta, sai zirga-zirga ki ke yi kin san ba haka mu ka yi dake ba. Zauna ya fa a yana zaunar da ita cikin bada umarni. Didi ya kalla da take kallonsa ya ce, Didi don Allah ki bar wannan kukan kin ga ba lafiya ce da ke ba, in kina kuka sai naga kamar baki farin ciki ba. Didi ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, me zata cewa Omar? A ganinta kalaman bakinta sun yi ka an wajan nuna masa jin da in ta da farin cikin da take ciki. Tun bayan da tayi aure, Omar ya auri Nayla suka fara zaman soyayya da jin da i bata da wani buri da ya wuce ta ziyarci Madina. Ko tafiyar da mijinta zai yi sai da taji kamar ta bishi, har ya yi mata al awari indai yana da rai a shekarar zai biya mata taje. Ga aninta da suke ciki aya ya cika mata wannan burin a matsayin bazata, to in bata yi kuka ba me zata yi? Ta ri e hannunsa gam ta ce, Omar Allah ya cigaba da farantawa rayuwarka, Allah ya kare ka ya cigaba da aukaka ka zuwa matakin da baka yi tunani ba. Allah ya ji an iyayenmu, Allah ya raba matarka da abinda yake cikin ta lafiya, Allah ya baka mai faranta maka kamar yadda ka ke faranta min ta fa a sabon kuka yana wace mata. KRB3P093 Nana haleema. Omar ya bita da kallo auna da tattali, a sanyaye ya ce, "Amin. Ya isa kukan don Allah. Didi in ban miki ba waye zan yiwa? Ke ka ai nake da ita, ke nake kallon a matsayin uwa, uba, anwa, awa, sannan Yayata. Kece matakin nasarata, kece silar auren wacce nake so, kece silar zuwana wannan mataki. To in ban saka ki farin ciki ba wa zan saka farin ciki Didi?. In dai ina da rai yanzu ki ka fara farin ciki in sha Allah, a yanzu ne zaki san kina da an uwa Omar!. Ki nutsu ki daina kuka" Ya fa a yana ri e hannunta yana kallon ta. Murmushi take yi tana kuka tana kallonsa ta ce, "tunda nake a duniya ban ta a farin ciki irin na yau ba, Omar ko ranar da nayi aure ban yi farin ciki irin wannan ba. Ni ce Madina har na shiga masallacin Annabi..?. Allah ya saka maka da alkhairi Omar, Allah ya baka abinda ka ke nema duniya da lahira." "Amin Didi. Indai kina so na san kin yi farin ciki ki daina wannan kukan, sannan ki nutsu ki huta zuwa anjima sai ki koma masallacin." Ta share hawaye ta ce, "To Omar na daina." "Kina jin yunwa?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "mu je ki huta, kin ga Marmerh har ta sake yin bacci." Da kansa ya ri e ta har akin da ta shiga azu, sai da Didi ta kwanta ya dawo ya kwantar da Marmerh a kusa da ita ya kashe hasken akin. Bayan ya fito ya kalli Nayla ya ce, "Ashiq don Allah taso mu je ki huta kema." Ta mi e ta ce, "zan kwanta tare da Didi." Da yake so yake ta kwanta in sai ya ce, "To ki je." Sai da ya bita ya tabbatar ta kwanta in sannan ya iya kwanciya shima. Gaba aya Didi ta sanyaye masa zuciya, rauni da aunarta yake ji a cikin zuciyarsa sosai, ya kuma ji a ransa sai yanzu ya fara rama alkhairi akan wanda ta yi masa. Ta sha gwagwarmaya dashi shi kansa ya sani, bata da nutsuwa kullum saboda auko mata magana da yake yi, ta saka shi a gaba tayi kuka amma hakan bazai saka gobe ya i yi ba. Mahaifiyarsu ta haife shi ne kawai, amma Didi itace uwa a gare shii. Yana son Didi sosai, yana aunar tayi farin ciki, ya san zuwa saudia yana aya daga cikin burinta na duniya shiyasa ya fara mata dashi. Da wannan tunanin shima ya yi bacci. Nayla ta riga su tashi lokacin ana gab da yin sallar azahar, ta sauka daga kan gadon ta sake yin wanka ta saka hijjabi ta fita daga akin. Ba jimawa ta dawo da abinci da kuma paper cup da ta siyo tea ta zauna tana sha. Motsi ta ji a bayanta, ta juya ta kalle shi ta ga ita yake kallo ya araso ya zauna kusa da ita ya ce, "Daga zuwa Madina kuma sai ki canja Jidda?." aure fuska ta kuma yi ta kawar da kai gefe ta ce, "Ai kaine ka jawo hakan." "Da na yi meye Ashiq!?" Ya fa a murya a can asa yana kallon idanunta. Ta ce, "Budurwar ka mana." Murmushi ya kubce masa ya ce, "yanzu daman duk akanta ki ke ta wanna fushin?. Kamar mun gama maganar nan tun a baya ko?." Nayla ta ce, "mun gama kaine ka dawo da ita baya." Ya matso kusa da ita sosai yana jin hamshin turarenta murya a asa ya ce, "to me nayi? Uhum me nayi kuma?." "Meyasa baka fa a min kun ha u a airport ba?." an bu e ido ya ce,"Shikenan daman fushin?." Ta harare shi ya yiwa idanunta kiss, ya dawo bakinta ya yi kissing sannan ya ce, "Lokacin na so na fa a miki sai sawun guiwa ya take na ra umi, da na zo zan fa a miki sai ki ka sanar min da kin kar i ajiyata. Jidda ta ya zan tuna da batun wata bayan ina murna zan zama uba?. Daga nan na manta da batun, amma na so na fa a miki." Nayla ta shagwa e fuska ta ce, "to me ta ce maka?." Ya shafi fuskarta ya ce, "Ba ki ji abinda ta maimaita ba? Ni ban nuna na gane ta ba Jidda, kuma na gane ta in amma kawai bani da lokacinta." "Amma ita tana da naka lokacin, gashi tana cewa tana sonka zata aureka, Har maahifinta yana zancen yana son ganinka." Ya sake ri e ta a jikinsa ya ce, "Ashiq!." Ya yi shiru ya zuba mata ido yana jujjuya idanunsa a kanta sannan ya ce, "Baki yarda da mijinki ba ne?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "ki bani amsa." Nayla ta ce, "A'a, na yarda da kai." Omar ba tare da ya daina kallon idonta ba ya ce, "To meyasa ki ke tunanin zan iya amsa kiran mahaifinta ko kuma zan iya aurenta?." Ta yi shiru bata amsa ba ya kuma cewa, "Ki daina wannan tunanin, ni naki ne ke ka ai kawai. Saboda ke ka ai Allah ya halicce ni, ki amince da wannan maganar da nake fa a miki. Inda ina da ra'ayin aure zan sanar dake, kece ta farko da zan fara fa awa zan yi aure lokaci kaza, ko kiji da in maganar, ko kar kiji ni dai bani da wanda zan fa awa sai ke in. Kuma koda ina da ra'ayin auren bana tunanin zan iya aurenta. Jidda in nayi gaba bana dawowa baya, in na ce na bar abu na bari kenan har abada!." Wasa take da azurfar hannunsa tana shafa gashin hannunsa ta ce, "Amma ai nima ka ce baka sona kuma daga arshe ka canja, ka ga itama zaka iya canjawa ai." "Jidda ke daban ita daban, wallahi ban ta a sonta ba, sai da na fara sonki na tabbatar da ita ba sonta nayi ba Jidda. Ki amince dani, ki bani yardarki bazan ci amanarki ba har abada....." ya matse hannunta a cikin nasa cikin taushin murya ya ce, "Jidda koda zaki ganni da mace a aki aya kawai ki tuna da yardar da ki ka yi min, ni kuma na yi miki al awarin bazan ci amanarki ba har abada!. Ni naki ne ke tawa ce, dan ni aka yi ki dan ke aka yi ni. Wata tarkacen ar Sen da ma ko wacce mace bata kai Omar ya kalle ta ba, har yanzu sunan yana nan....Tiger! Har gobe sunana ne. A wajan ki ka ai na canja, amma ga kowa haka nake. Ke ka ai ki ke ganin fara'ata ko a yaushe, shiyasa ki ke tunanin zan yiwa matan kan titi, ki tuna damisar da ki ka sani a baya har gobe ita ce!." Rungume shi tayi da sauri ya yi ajiyar zuciya yana shafa bayanta ya ce, "kin azabtar dani, rabon da na ji ki haka tun a Abuja, don Allah ki daina ha e min rai Ashiq, kina sakawa ina fita daga hankalina." Nayla ta ce, "ina sonka Rouhii, ina kishinka sosai." "Son da ki ke yi min wasan yara ne akan wanda nake miki. Ina sonki, Allah shaida ne, ina kishinki wanda ban san iyakacinsa ba." Nayla ta ce, "Alfarmar wannan gari mai albarka, alfarmar wanda yake kwance a cikinsa baza ka yi min kishiya ba, Allah yasa ka cigaba da sona har a aljanna, Allah ya sa baza ka ta a jin sha'awar wata mace ba sai ni ka ai." Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Amin Jidda, Allah ya amsa addu'arki." "Amin Rouhii." Ta yi luf a jikinsa, shima bai ce komai ba idonsa a lumshe kafin ya ce, "Ina kewarki sosai Ashiq, aljanun da suke kawo mana ziyara ma suna kewa Jidda." Ta ago ta kalle shi taga ya marairaice fuska ta ce, "Didi tana nan." an wara ido ya ce, "sai me? Ta san tunda muka zo tare ai dole sai tana rufe idonta." Murmushi ta yi tana kai masa duka a ijinsa ta ce, "baka da kunya ne kawai." "Ke kina da ita ai." Cikinta yake shafawa a hankali ta ce, "na siyo abinci fa, gashi nan." Bai magana ba sai matso da fuskarsa da yayi kusa da tata, yana kallon idon ta har lokacin yana shafa cikinta ya ce, "kin san in ka aikata aikin lada a asar nan Allah ninka maka ladan yake yi
Chapter 153 · 0% Book details