← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 205

Sashe 152

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayla ta fa a da sigar tambaya tana nuna mata. Didi ta kalli wajan ta sake kallo ta kalli Nayla ta ce, A Madina nake da gaske?. Nayla ta ce, Mu je mu hau mota mu je hotel, zan kai ki masallaci annabi, na tabbatar in muka je can zaki gasgata Ita dai Didi gani take kamar wasa suke mata hakan ya saka ta cigaba da tafiya suka fito wajan airport in da taimakon Nayla. Zuciyar Didi ta tsinke ganin larabawa a mota, garin kana gani ka san ba Nigeria ba ce ba. Omar ya ga kamar tana jiri ya ri eta ya ce, Ki nutsu Didi. Ta kalli Omar ta ce, kuma son haukata ne kai da matarka, ku daina yi min wasa don Allah. Omar bai ce komai ba Nayla kuwa har ta gama magana da driver ta fa i inda zai kai su ta kalle shi ta ce, mu je. Baby pusher in aka na e aka saka a bayan mota Omar ya shiga gaba Nayla ta shiga baya ita da Didi. Didi ta zama kurma sai kalle-kalle ta ke yi zuciyarta na bugawa sosai, wai itace a Madina dan kawai an raina mata hankali, madinan masallacin gidan sarkin Kano ne da zata je lokaci aya haka?. Tafiya suka yi mai an nisa kafin su tsaya, Nayla ta auko ku i ta biya ta ri e hannun Didi ta ce, Didi zo mu je Hannunta ta ri e suna takawa Nayla na jan jaka aya haka Didi ma na ja Omar da Marmerh suna tafiya. Hotel suka shiga Nayla ta zaunar da Didi suka arasa reception ita da Omar, Nayla ta nuna musu evidence na rooms in suka yi reserving da komai suka bata card akin. Wajan Didi suka dawo ta kalle shi ta ce, ka taho da kayan zamu je da Didi, floor 18 ne. Mu je tare dai. To tsaya na samu empty elevator sai mu shiga gaba aya, ko da yake lokacin sallar asuba ya kusa da yar a samu empty. Barin wajan ta yi ta arasa wajan elevators ta danna aya aka ayi sa a aka samu, suka saka kayan ya ri o Didi suka shiga Nayla ta danna floor 15 suka wuce. Suka fita daga elevator in Nayla ta arasa wajan akin ta saka card in ya bu e suka shiga da kayan parlor, ta bu e rooms in ta ga bedrooms biyu ne da parlor kamar yadda ta yi booking. Didi ta kalla da ta zama kurma sai kallon akin take yi cikin ru ewa. Nayla ta ce, Didi mu je ki huta kin gaji. Didi ta kalle ta ta ce, Nayla kar ku haukata ni don Allah. Kiran sallar asuba aka fara yi, sai Nayla ta ce, ga kira nan ana yi, Rouhii zamu je sallah ko sai ta huta?. Ya girgiza kai ya ce, A gajiya ki ke kema, ya kamata ki huta. Amma ina so Didi ta fita daga ru anin nan, gwara mu je kawai. Didi taso ki yi wanka zamu je masallaci na tabbatar miki. Didi kamar Nayla umarni take bata ta tashi suka shiga aki aya daga cikin akunan, Nayla ta bu e mata ban aki ta fito da kayanta ajjiye harda sabulun wanka ta ce, ki yi wanka Didi. Fita tayi ta barta a akin, tana fitowa tayi kamar zata fa i ya ri ota ya ce, Yi a hankali, kin gaji ko?. Gimtse fuska tayi ta kalle shi ta ce, ta shiga wanka, nima wanka zan yi ta fa a tana jan jakarta shiga da ita akin Didi, ta bu e ta auko hijjab da doguwar rigar da zata saka ta fito da kayan a hannunta zuwa aya akin ta shiga wanka. Tana fitowa daga wankan ta same shi a zaune a akin, bata kula shi ba ta saka kaya ta ora hijjabinta kalle shi ta ce, Mu zamu wuce. Omar ya bita da kallo ya ce, Ashiq ba haka muka yi dake kafin zuwa nan ba, kin ce min zaki kula da kanki da lafiyarki, yanzu meye ki ke yi haka? Daga zuwa yau kin canja maganarki. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, Ni ban gaji ba, kuma sallar asuba kawai zamu yi zan dawo. Zata fita daga akin ya ri e hannunta ya ce, Jidda!. Ta tsaya cak bata juyo ba ya ce, Duk wannan abun na meye ne wai? Duk akan Bata bari ya arasa ba ta zame hannunta ta ce, Muna jiran ka in ka shirya mu tafi gaba aya. Fita tayi ta bar shi ta koma wajan Didi ta tarar har Marmerh ta yiwa wanka tana mamakin kayan da ta gani na Marmerh. Nayla ce ta ta arasa shirya Marmerh ta ce, Didi mu je. Tare suka fito har lokacin bai fito ba, ta nufi akin zata shiga akin ya fito ya saka doguwar riga jallabiyya mai kyau da laushi. Ta ce, auki key aya ko da zamu rabu. Bai tanka mata ba suka fito tare tana ri e da Didi, Marmerh kuma tana hannunsa suka sake shiga elevator suka sauka zuwa reception suka fita. Da yake babu nisa sosai daga hotel insu zuwa masallaci ba jimawa suka araso. Didi tunda ta hangi masallacin jikinta yake rawa dan ta tabbatar da gaske ne ba arya ba. Tana saka afarta a harabar masallacin ta ji wata fa uwar gaba da wani hamshi da bata ta a ji ba, ta kalli Nayla ta ce, Nayla mafarki nake yi ko gaske?. Nayla ta ce, da gaske ne Didi, gaskiya ce. Didi bata sake cewa komai ba ta zube a wajan a sume. Omar ya araso da sauri ya ri e Didi yana kiranta amma Didi ta suma. Da gaggawa an agajin masallacin suka araso aka saka ta a motar da take yawo a cikin harabar masallacin aka wuce da ita zuwa asibitin da yake can arshe a masallaci. Duk tare suke, Nayla tana ri e da hannunta, ana zuwa aka kar e ta aka kwantar dan taimaka mata. Nayla ta zauna akan kujerun da aka tanada ta dafe kanta, ya zauna kusa da ita Marmerh tana jikinsa dan ta tashi daga bacci ya ce, Ashiq don Allah ki nutsu, ki nutsu don Allah bana son wannan yanayin na ki. Kwanciya tayi a jikinsa dan ta gaji sosai kanta ya yi nauyi tana bu atar bacci. Ri eta ya yi ba tare da ya ce komai ba, ba su jima da zama ba aka tayar fa i ama, tare suka fita dashi ya hau sahun maza ta hau na mata bayan ya bata Marmerh suka tayar da sallah. Shi kansa mamaki yake yi wai yau shine ya yi sallar asuba a masallacin ma aiki, abinda bai ta a kawo shi zuciyarsa ba ko da wasa, sai gashi cikin lokaci ka an Allah ya yi masa ni imar ziyarar masallacin annabi har ya yi sallah a cikinsa. Sai ya samu kansa da zubar da hawayen rauni da godiya ga Allah, ya goge idonsa ya kalli Nayla da take kallonsa daga can gefe, suna ha a ido ta auke kai ya yi murmushi yana mamakin wanann kishin na ta. Tare suka koma aka yi musu bayanin dalilin suman nata, suka ce sun saba samun irin haka, shau i ne da farin ciki yake saka mutane suma. Aka tabbatar musu da lafiya lau take ta kuma farfa o. Tare suka shiga akin suka same ta a zaune, Nayla ta arasa ta zauna kusa da ita ta ce, Didi sannu, ya ki ke ji?. Didi ta ri e hannunta ta kalli Omar da yake tsaye ta ce, Nayla ya aka yi haka ban sani ba? Ta fa a hawaye yana sakko mata. Nayla ta ce, Duk aikin aninki ne Didi, ya ce yana so ya baki mamaki ya kuma saka ki farin ciki shiyasa ba ya da bu atar ki sani, shiyasa da aka fa awa Yaya AbdulHamid aka ce kar ya fa a miki. YaMar ya yi ne dan ki ji da i ki kuma yi farin ciki, sannan ki san Allah ya azurta shi zai iya yi miki komai dan ki ji da Kuka sosai Didi take yi cikin farin ciki, ta kalle shi cikin kuka ta ce, Omar!. Zuciyarsa sai ta karye yaji rauni ya mamaye masa zuciya, aunarta da tausayin wahalar da tasha dashi suka zo zuciyarsa, ya tako a hankali ya zauna kusa da ita ya ri e hannunta guda aya ta ora kanta a kafa arsa tana kuka sosai. A hankali ya ce, Ki daina kuka Didi, kinga baki da lafiya. Bata iya magana ba ta fi mintina biyar tana kuka kafin ta koma sauke ajiyar zuciya. ago ta kalle shi shima ita yake kallo ta ce, Omar Sai ta kasa magana ya ce, ba sai kin ce komai ba, don Allah ko yi shiru, ki nutsu mu je ki yi sallah ki huta. Didi ta goge ido ta ce, Omar na rasa me zan ce, na rasa me zance Omar. Ba sai kin ce ba Didi, kawai ki kwantar da hankalinki shine abinda nake so. Didi ta yi ajiyar zuciya ta kalli Nayla da take kallon ta itama tana hawaye, ta sake ri e hannunsu duka biyun ta ce, Nayla me zan cewa Omar? Da wacce kalma zan yi magana?. Nayla ta ce, Didi ba sai kin ce komai ba kamar yadda ya ce, ki zo mu je ki huta a gajiye ki ke sosai. Da yar suka lalla a Didi suka fito Nayla na ri e da hannunta. Kasancewar asibitin indai kana da visa umra ne free ne ba a kar ar komai, basu biya komai ba har magani aka bawa Didi. Didi kallon masallacin take yi tana hawaye, ta sake urkusawa a wajan tana kuka sosai. Wai itace a harabar masallacin annabi, to me zata yi in ba kuka ba? Me ya kamace ta in ba kukan ba?. Nayla ta ri eta ganin ta sake fita daga hayyacinta, aramar motar da suka hau azu ce ta zo wucewa Nayla ta yi musu magana suka shiga aka kai su arshen harabar masallacin daga nan suka ri e Didi suka koma hotel. KB3P094 Nana haleema. Nayla alwala ta saka Didi tayi sannan ta yi sallar asuba. Bayan ta idar
Chapter 152 · 0% Book details