Sashe 139
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Safna kalli ki ga, kalli Safna, wallahi he's the one, he's my love Faruk, wallahi shine" Narma ta fa a hannunta yana rawa tana nunawa Safna wayarta da take hannunta. Safna ta kalli abinda take nuna mata ta kalle ta cike da takaici ta ce, "You're out of your senses Narma, How come this classy, rich and handsome guy in zai zama wannan thug in?. Kin manta waye Faruk in na ki ne? Haba ki dawo nutsuwar ki mana, wannan ba shi bane." Narma ta dafe kai ta ce, "look, sunansa Omar kalli ki ga abinda aka rubuta, and he live in Kano, kalli fuskarsa mana. Wallahi shine, ko a ina na ga Faruk zan gane shi" ta fa a tana zooming fuskar Omar tana nunawa Safna. Safna ta yi tsaki ta ce, "Ai sai ki yi, dan kawai wannan ya kasance Omar shikenan sai ya zama shine Faruk inki?." Narma a sanyaye ta ce, "Shima fa Omar ake ce masa, ni ce nake cewa Faruk." "Narma ki dawo nutuswarki don Allah, duk kin bi kin haukace akan wannan an daban. Ta ya wannan zai zama shi? Ki kalli shigarsa da matsayin da ya samu da wa anda suke gefensa ki ce he's the one?. Ki dawo hankalinki malama, ina ya ga ilimin da zai kawo wannan matakin? And ina ya ga hankali da nutsuwar da zai yi abin kirki haka?. Na fa a miki zan duba miki inda yake amma duk kin bi kin tayar da hankalinki." Sai jikin Narma ya yi sanyi ta kalli Safna ta ce, "Amma suna kama sossi Safna, ni ban yarda ba shi bane ba wallahi." "Sai ki yi ai, in zaki dawo hankalinki ki dawo, wannan ba shi bane, zan dai je na nemo miki wancan nakin mu gani. Abu aya na sani, an tabbatar min da ya yi aure!." Narma ta dafe irji cikin fa uwar gaba ta ce, "Ya yi aure?." "Yess, ana zancen an yi one year ma da auren" "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Safna ni fa?." "Narma bana ce ba, in har yana sonki ai kin ce you're ready to be his second wife right?." Narma ta aga kai alamun eh Safna ta ce, "Okay don't be nervous, in sha Allah komai zai dawo daidai." Narma ta ce, "to" ta fa a a sanyaye cikin bugawar zuciya. Sai ta bawa Safna tausayi, mace mai aji da kyau da ku i itace Allah ya saka ta a wannan jarabawa ta soyayya. Narma da sai ka kai wani mataki ma take bu e dm inka balle ka yi mata waya ta auka ko ka yi mata magana kai da ita. Amma kalli yadda Allah ya juya sama ta dawo asa, haukan sonsa take yi shi kuma bai ma san tana yi ba, ya yi aurensa ya manta ma da ita a rayuwarsa. Rarrashinta Safna ta dinga yi har ta an dawo daidai kafin ta saka ta su fita su an zaga garin Abuja dan ya dawo nutsuwarta. Satin Omar biyu a China sannan ya sanar da Nayla zai dawo, Nayla murna kamar zata yi me ta rasa ma abinda zata yi. Har gyaran jiki ta yi, duk Mama na kallon ta dan ita tsoro take ji ina mai ciki ina gyaran jiki? kar a je a zubar da shi. Bayan ta gama kwalliyar ne Mama take cewa, "Nayla Omar zai dawo kin sha unshi da gyaran kai ga gyaran jiki, yanzu dai kina da ciki komai a hankali ake binsa, in ba haka ba tsaf za a zubar dashi." Nayla sai taji kunya sosai bata iya kallon Mama ba ita kuma ta fita ta yaaleta. Omar kuwa a Abuja ya sauka kamar yadda ya tafi ta Abuja, yana zaune a airport yana jiran jirgin da zai kawo shi Kano ya zo. Yana zaune cikin manyan kaya na yadi coffee colour, kansa babu hula sai gashinsa da ya kwanta, ya ora afa kan aya yana danna waya ga trolly bag insa a gefe. In ka kalle shi sai ka sake kallo saboda yadda ya kame ya yi kyau, ya zama irin rich handsome guys in nan. "Faruk!." Ya ji an fa a daga bayansa, ya tsaya cak da abinda yake yi dan a kaf duniya ya san wacece ta ta a kiransa da wannan suna, kuma tana fa a fuskarsa ta zo idanunsa dan ya san itace in. Ya maze bai motsa ba kamar ba shi ta kira ba, sai ta ce, "Omar!." A hankali ya ago ido ya kalli idanunta. Narma ta ja doguwar ajiyar zuciya, fuskarta ta nuna yanayin da zuciyarta take ciki, hawaye suka ciko idanunta ta ce, "Safna na fa a miki Faruk ina ne, kalle shi ki ga." Safna da take tsaye a bayanta ta kalli Omar da ya mayar da kai ya cigaba da abinda yake yi kamar bai ga Narma ba, ta an yi tsaki ta ri e Narma ta ce, "Narma please! haba meyasa ki ke arin haukacewa ne? Kin ga wani a waya kin ce shine, yanzu kin ga wannan ma kin ce shine, maza nawa ne zasu koma miki Faruk in?." Narma a sanyaye ta ce, "Kalle shi ki gani, shine wanda na ce miki, shine a cikin wayar kuma shine Faruk in.." ta dawo da kallon ta gare shi ta ce, "Faruk baka gane ni ba? Narma ce fa." Sarai Omar ya ganeta kawai bashi da lokacin dai zai kulata ne, a ganinsa in ya yi mata magana kamar ya ci amanar matarsa ne, amma wani angare na zuciyarsa ya ji tausayinta sosai, musamman kalaman awarta. Tausayinta ya ratsa zuciyarsa, jin yadda muryarta take rawa kamar ba ita ba ya dake shi. Safna ta kalli Omar ta ce, "ka yi ha uri, wani saurayinta ne da mahaukacin so, duk wanda ta gani sai ta ce shine, ka yi ha uri please" ta kalli Narma ta ce, "Narma mu je" ta fa a tana jan hannunta. Narma ta turje ta ce, "Babu inda zan je, shine wanda nake nema kuma shi na gani yanzu" ta dawo kusa da Omar ta ce, "Baka gane ni ba? Faruk say something please, ka yi magana kafin zuciyata ta buga. Na jima ina neman ka, na jima ina so na ganka, Faruk please!" Ta fa a tana ha e hannayenta tare da zubewa a wajan. Omar ya rasa abinda zai yi, tausayinta yake ji sosai, ya san zafin so, ya san ya ake jin soyayya shiyasa yake jin tausayinta yana yin tasiri a zuciyarsa. Musamman yadda take kuka ta kuma zube a gabansa ga mutane da suke ya wucewa tunda rana ce kuma waje ne na kowa da kowa. In ya nuna ya gane ta me zai ce mata?, bai san mai zai furta mata ba gwara ya yi shiru. In kuma ya nuna bai gane ta ba ya kyauta mata kuwa?. Omar ya rasa me zai yi mata, a hankali ya kalle ta suka ha a ido, yadda idanunta suka red, jijiyoyin kanta suka tashi ya sake karya masa zuciya, ya auke kai daga kallon ta ya ce, "Kina ji, ba wanda ki ke nema bane" ya fa a yana mi ewa tsaye ya ri e trolly bag insa zai bar wajan. Hannunsa ta ri e da sauri ta ce, "Wallahi kaine, Muryarka ta tabbatar min da kaine. Ko a cikin mutanen da ban san adadinsu ba in na ganka na san kaine, ko maganar ka na ji na san kaine Faruk. Me nayi maka ka ke arin yi min wannan hukuncin? Meyasa ka ke arin wula anta zuciyar da ta gama narkewa a soyayyar ka? Meyasa ka ke arin cutar da zuciyar da ta jima da cutuwa akan soyayyar ka?. Please Faruk, ka tausaya min kafin na rasa hankalina a kan ka." Omar ya tsaya cak yana jinta, jikinsa ya yi sanyi sosai ya kasa motsawa. Ajiyar zuciya ya yi ya zame hannunsa daga ri on da ta yi masa, bai ce komai ba zai wuce ta. Sake tsayawa a gabansa tayi tana kallon fuskarsa gabanta yana fa uwa, kallon fuskarta ya yi suka sake ha a ido, ya auke kai ganin yadda hawaye yake a kwance akan fuskarta idanunta sun sake yin ja. Hannayenta ta ha e waje aya cikin wani yanayi na kewa da soyayya ta ce, "Please Faruk, allow me to hug you!." Jin abinda ta ce a lokacin ya janye ido daga kanta, tausayinta ya kama ratsa zuciyarsa, baya so raunin da yaji ya bayyana akan fuskarsa. Ya sake ra ata zai wuce ta ce, "ina sonka, ina so na aure ka. Faruk a yanzu babu wanda ya isa ya raba ni da kai." Baice komai ba ya wuce ta dan in ya cigaba da tsayawa zata karya masa zuciya shi kuma ba haka yake so ba. Narma zata bi shi Safna ta ri e ta cikin masifa ta ce, "Haba don Allah Narma, kawai daga ganin mutum sai ki ce shine wanda ki ke nema? Wannan ya yi miki kama da Omar in Kano ne? Ko kuma nan Kano ne da zaki ce ai shine?. A Abuja ki ke, a Abuja ma a cikin airport, wanda ki ke magana a kai me zai kawo shi airport?. Ki dawo hankalin ki Narma, ki daina yi mana shirme, kina gani ana ta kallon mu kamar wasu cartoon. Ni da na sani ma ban ce ki rako ni ba" ta fa a tana jan hannunta da arfi suka bar wajan. Ita kuwa Narma tunanin ta yana ga Faruk inta, duk abinda ya yi mata da abinda ya ce bata damu ba, burinta ya cika ta ganshi ta kuma tabbatar shine. Saura burinta na aurensa, dan a wannan lokacin bazata aga afa ba. Omar kuwa a haka ya shiga jirgi duk sai ya ji ta sake bashi tausayi sosai, jikinsa ya yi sanyi har yana tuna yadda take kuka. Bai bari tausayin ya yi tasiri a zuciyarsa ba, ya watsar da tunanin ya jawo tunanin matarsa yana tuna irin yanyin da zai same ta in ya koma gida. KRB3P085 Nana haleema. A Kano suka sauka ya kira Bashir yazo ya auke shi suka tafi. Sai da suka fara zuwa gidan Didi kamar wancan lokacin dan zuwa lokacin yamma tayi sannan suka wuce gida.