Sashe 17
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk abinda nace mata tana yi kai kuwa fa? Sai na sha wahala na aga murya sannan zaka iya sauraron abinda zan ce maka. Ina tunasar da kai ha inta ne ba dan na za eta na barka ba, yarinyar bata da damuwa ko ka an, inda zaka sauke wannan banzan girman kan naka zaka ji da in zama da ita fiye da kowa. e baki ya yi bai kula ta ba ya auke ido daga kallon ta. Didi ta ce, Ta ce min gobe zata koma aiki, ka sani?. A fusace ya juyo ya ce, Sai na sani? Ta tafi lahira ma ina ruwan Omar?. Kai fa mijinta ne, ta ya zaka ce sai ka sani?. To ni a wajena ba sai na sani ba, duk inda zata je ta je bai dame ni ba. Zama nake yi kawai ba dan Ina so ba sai dan saboda ke, ana yi min abinda bai yi min ba bazan sake komawa gidan ba. Ganin yarinyar ma takaici yake bani balle ta bu e baki ta yi magana, wa adina nake jira ya cika in na bar gidan wallahil azim ko me zaki ce Didi bazan komai ba. Didi ta dafe kai bata san ya zata yiwa Omar ba wallahi, caja mata kai yake yi a ko yaushe da matsalolinsa na yau da kullum. Ta daure ta ce, to ka tashi mu je ka yiwa Hajja sallama zata tafi umra gobe. Kallon up and down ya yi mata yana aga gira sama ya ce, a dangin wa zan je yi mata sallama?. Matsayinta na babba wacce nake kallo matsayin uwa kuma kakata. Sannan matsayin kakar matarka!. Yayi murmushin rainin hankali ya ce, Da kin tsaya a iya na farkon sai na je, amma tunda ki ka fa i na biyun babu inda zan je. Wallahil azim sai ka je ta fa a a fusace tana kallon sa. Kallon ta yake yi jin har ta rantse, ya aure fuska yana binta da harara ya ce, Dan fa na karya miki rantsuwa ba wani abun bane a wajena Didi, ki daina ganin kina yi min dole ina yalewa wallahi an kusa zuwa ga ar da zan kasa jurewa. Ba fa haifata ki ka yi ba wasu shekaru kawai ki ka bani, amma yadda ki ke bani umarni ko uwar da ta haife ni sai haka. Komai kan ki tsaye ki ke cewa wallahi sai na yi, nayi abubuwa da yawa a baya wanda ki ka ce, an kusa zuwa ga ar da wallahi bazan yi ba!. Didi ta har e hannu a irji ta ce, kawai ka ce ka kusa daina ganin girmana da darajata. Ya gir giza kai ya ce, Ni ban ce haka ba, amma dolen da ki ke saka ni ne na kusa daina jurewa wallahi. Gwara na ma fa a miki na kusa daina yin abun da bana so saboda ke. In na i yi ai ba zunubi Allah zai rubuta min ba, tunda ba haihuwata ki ka yi ba balle ace na sa awa uwata! Ya fa a harararta. Dariya ya bawa Didi ganin hararar da yake mata da kalamansa, bai ta a fa a mata haka ba tun yana tantirinsa sai yau, tunda ta ji ya fa a tasan ta kunna shi da yawa. Ta danne dariyar ta ce, ka tashi mu je yanzu. Kamar bazai motsa ba ta sake cewa, ka tashi Omar don Allah. Banza ya sake yi mata sai kuma ya kalle ta ganin ta koma kalar tausayi sai ya kawar da kai. Bazai iya in yin abinda ta ce ba, duk abinda ta ce masa yayi koda baya so dole ya yi saboda ita angaren rayuwarsa ne, koda yaso yi mata tijara da sun ha a ido sai ya yi laushi saboda tasirin aunar da yake yi mata. Ya mi e ba tare da ya kalle ta ba ta yi gaba ya biyo bayan ta. Bai kulle gidan ba suka shiga gidan Hajja fuskarsa a aure dan wallahi ya gaji da wannan abun da Didi take masa, dan yana girmamata yana yin duk abinda ta ce ba hakan yana nufin ta dinga yi masa abinda baya so ba. A bakin falon ya ja ya tsaya Didi ta shiga tana cewa, Hajja Omar ne ya shigo yi miki sallama ya kuma tsaya a bakin ofa. Hajja ta ce, Ummaru shigo mana, ka tsaya daga nan kamar ba aramin tsaki ya yi takaici ya mamaye masa zuciya, ya cize baki tare da ha iyar yawun jin haushi ya shiga falon da sallama a ciki. Hajja ta amsa tana kallon sa tana murmushi ta ce, yanzu nake tambayar matarka kwana biyu ban ganka ba, dan halak ashe zaka shigo. Shi dai bai tanka ba ya zauna ya ce, Hajja barka, an sha ruwa lafiya. Lafiya lau Omar, ya iyali?. Allah ya kiyaye ya dawo daku Lafiya ya fa a ba tare da ya amsa tambayar da tayi masa. Hajja ta ce, amin na gode Ummaru. Kafin Hajja ta sake magana ya mi e tsaye Hajja ta ce, har zaka wuce?. Kai ya aga kawai bai yi magana Hajja ta ce, Nayla ki tashi ku tafi dare yana yi. Tare mu ka zo?. Duk kallon sa yaga suna yi musmaman Didi da take aiko masa da harara, a lokacin ya fahimci su a ganin su fa ar hakan da ya yi kuskure ne kenan. Didi ta ce, Hajja tare zamu wuce da ita ai, shi wannan ma aiki suke yi na ha a takalman sallah. Hajja ta ce, Allah ya taimaka Omar, Takalma suna kyau sosai. Amin ya amsa a ta aice tare da cewa, Sai an jima ya fa a yana fita da sauri. Hajja ta girgiza kai ta ce, Omar kenan. Nayla dai tunda ya shigo bata motsa ba, mamaki ma take yi da ya iya shigowa bata auka zai zo ba duk da ta san Didi ce ta saka ta. Kamar ruwa ya tsince ta haka ta yi tsif ko motsin kirki bata yi, duk abinda ya ce tana ji har ya fita. Diid ta ce, To Hajja Allah ya kiyaye ya sauke ku lafita ya kar i ibada, ayi mana addu Hajja ta ce, Amin Aisha. In sha Allah za a yi addu a bakin gwargwado. Didi ta mi e ta ce, mu zamu wuce. Nayla ma sai ta mi e ta ce, Hajja Allah ya kiyaye hanya, ayi mana addu a Hajja. In sha Allah za a yi Hauwa, Allah ya baku zaman lafiya da wannan Damisar mijin naki, ya sauke masa wannan abinda yake ji a kansa. Mutum kamar aljani. Dariya Nayla tayi suka fita ita da Didi har Salna da ta raka su gate ta dawo. Da yake Didi ta cewa AbdulHamid tana gidan Omar yana ofar gidan da mota yana jiranta. Da afa suke takawa ita da Nayla suna hira. Didi ta kalli gidan su bayan sun fito ta ce, Nayla Omar ko abinci ba ya ci a gidan ko?. Nayla ta kalli Didi ta ce, Didi ni abincin ma nake so a rage ya yi yawa kar ya lalace, ni ka ai ce ba wani abun kirki nake ci ba. Don Allah ki aiko a rage wani abun kar azo ayi asara, ko iya lemo yana nan a jibge ko cartoon ban sha ba har yanzu. Didi jin ta canja maganar sai ta yi murmushi ta ce, Ai Nayla abincin ki ne ta ya za a rage?. To Didi sun yi yawa sosai, ni ko shinkafa ban bu e ba kuma tana nan tafi guda biyar fa. Na dai bu e basmati amma babban buhu ban bu e ba. Don Allah a rage wani abun kar azo ana asara, gwara a rage a bawa masu so. Didi ta ce, gashi ke ka ai ke ci ko?. Nayla ta ce, eh wallahi, Ni ka ai ce taya zan iya da abincin nan?. Didi jin amsar da take so ta samu sai ta ce, Omar baya ci kenan, Allah ya shirya min Omar shirin addini. Nayla ta amsa da amin a zuciyarta. Didi ta kalle ta suna gab da gidan ta ce, Nayla na san halin Omar, ki cigaba da ha uri komai zai zama labari. Wallahi ni kunyar ki ma nake ji. Nayla ta ce, Babu komai fa Didi, kowa da addarar da Allah ya rubuto masa. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, haka ne, Allah ya kawo mana mafita. Ta amsa da amin a lokacin suka zo ofar gidan. Nayla ta arasa ta gaisar da mijin Didi sannan suka yi sallama Nayla ta shiga gidan ita kuma ta hau mota suka tafi. KRB3P009 Arewabook@nanahaleema. Washe gari har ta shirya da safe ta fito harabar gidan bata ji motsin sa ba, ban da Allah ya sa ma taji motsi da asuba baza ta san a gidan ya kwana ba. To ta ji an bu e gate har take mamakin daman yana zuwa masallaci ko yanzu ya fara. Harabar gidan ta ke a tsaye tana kallon motar tana tunanin ta yadda zata fita da ita da baya, ita ta saba da babban gida wanda zata juya mota kawai ta fita ta gaba ba ta baya ba. Bu e gaban motar tayi ta saka laptop ta bu e mazaunin driver ta shiga. Dafe kai tayi tunawa fa ita zata bu e gaye in, tayi tsaki ta fito ta bu e gate in sannan ta shiga motar tana fitowa da baya a hankali. Kasancewar safiya ce babu jama'a sosai kuma babu abin hawa shiyasa ta fito da motar, ba dan haka ba tsaf sai ta bugawa wani motar. Zata fito ta rufe gate in ta ga Bashir shine ya kulle gate in ta kalle shi tana cewa, "Sannu, na gode." "ina kwana Antyn mu." Murmushi ta yi ta ce, "Ka tashi lafiya? Ya ibada?." "Lafiya lau." Key ta sakawa gate in sannan ta shiga shiga mota ta bar unguwar. Wajan aikin ta je tayi duka abinda ya kamata ta yi kafin ta fara aiki a wajan. Sai la'asar suka tashi tana tashi kuma ta auki hanyar Arewa24 a address in da taji an ce suna wajan. Bayan ta je ta fa i abinda ya kawo ta sun yi mata bayanin yadda abin