Sashe 40
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sosai amma tayi bacci. Tashi ya sake yi ya auko waya ya dawo ya zauna ya shiga page insu na Instagram ya duba sai ya ga gaba aya an goge video Nayla kamar yadda ya ce. Ajiyar zuciya ya yi ya kifa wayar a irjinsa yana jin zafi-zafi a irjinsa ba tare da ya san dalilin hakan ba. Shi dai ya san bai ta a jin abinda yake ji akan kowa ba sai ita in, bai san me hakan yake nufi ba, amma yafi danganta hakan da yadda aka bashi ita baya so. Da wannan tunanin ya yi bacci a kan cousion ba tare da ya sani ba. Haka ya dinga yin baccin yana farkawa saboda ya takura dan shi ya saba kwanciya a waje mai girma. Bai samu wani baccin kirki ba har asuba tayi, ya tashi zaune yana ri e wuya saboda yadda ya ri e masa yana an juya kansa ka an. Kallon ta ya yi a lokacin ta motsa itama da alama ta ji kiran sallar a zuciyarta. Ajiyar zuciya ya yi ya mi e ya shiga ban aki, yana fitowa ya saka doguwar riga da slippers ya taka zuwa kofar akin, yana jan ofar yaji ta bu e. Dariya ya yi mai sauti a ransa yana girmama makircin Didi. Har zai fita sai ya kalleta ya ga bata tashi ba sai ya ja ofar kawai ya fita. Da ya dawo bai duba inda Didin ta ke ba akin ya shiga kai tsaye ya samu Nayla akan sallaya. Kallon sa ta yi ta ce, "Ina kwana." Maimakon ya amsa sai ya zauna sannan ya ce, "Lafiya." Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru amma yana so ya tambayeta ciwon kan da ta kwana dashi amma izza da aji bazai bashi dama ba. Sai kuma ya sake tashi zai fita ya ake ji a kulle ofar. Dariya ya yi mai sauti a bayyane ya ce, "Didi makira ce." aramin tsaki ya yi ya dawo ya zauna amma har lokacin fuskarsa da annuri sosai. Nayla saboda ciwon kan bata tsawaita zaman ba ta mi e ta koma inda ta kwanta ta zauna, sai take jin yanyinta gaba aya babu da i. Hasken take son kashewa amma tsoron fa ansa take yi shiyasa ta ha ura ta sake kwanciya kamar jiya. Shi dai Omar bai motsa ba yana dai kallon ta tana satar kallonsa a tsorace. Gaba aya ta rufe jikinta har fuskarta saboda hasken ya dame ta ga kanta da yake ciwo. Ya jima a haka kafin ya tashi ya kashe hasken akin ya koma ya zauna. Bai saba bacci bayan asuba sosai ba amma sai gashi ya kai har tara na safe a zaune yana bacci. A hankali ya bu e ido akin babu haske sosai saboda labulayen a sake suke kuma an kashe hasken akin. Wayarsa ya ta a ya ga safiya tayi sosai, ya juya kansa da jijiyar wuyan ta ri e ya kalli inda Nayla take ya ganta luf bacci take yi. Hamdala ya yi da bata riga shi tashi ba, ya mi e da yar saboda ri ewar afarsa da wuyansa ya yo ya shiga ban aki. Ruwan zafi ba wani damunsa ya yi ba hakan ya saka bai kunna water heater ba ya kunna ruwan fanfo ban akin ya yi wanka. Har ya fito ya shirya Nayla ko motsi bata yi ba, shi kuma hakan ya yi masa da i sosai ya samu ya shirya yadda yake so. Bai bu ofar ya fita ba sai goma na safe sannan ya fito zuwa falon. Motsin Didi ya ji a kitchen ya shiga kitchen in a karo na farko a rayuwar zaman gidan, yana shiga suka ha a ido da ita sai tayi dariya kafin ta yi magana ya ce, "ina kwana." Maimakon ta amsa sai ta ce, "Angon Nayla, yau kaine har goma kana bacci? Lallai bacci ya yi maka da "Hmmm" shine abinda ya furta kawai ba tare da ya ce komai ba. Didi ta kalle shi cike da tsokana ta ce, "har wani kyau na ga ka ara yau, sai hamshi ka ke yi ka fito a sak ango." Nan ma bai tanka mata ba ya ma auke kai daga kallonta kamar ko yaushe fuskar babu fara'a. Didi ta ce, "Don Allah kai kanka baka ji da i a ranka ba? Ai ko babu komai na saka ka kwana aki aya da matarka." "Shiyasa ki ka kulle ofar kenan?." "Na san hali ne ai, tsaf zaka zo kana yi min wannan hargitsin na ka shiyasa nayi maganin ka." Omar ya shafa fuskarsa ya kalle ta ya ce, "da ki ka yi hakan wacce riba ki ka samu?." Didi ta ce, "riba da yawa na same ta, ciki harda rashin tashin ka da wuri." "Hmm Didi kenan. Kina arin ganin yarinyar nan ta raina ni, kina yi min abinda ki ke so a kanta." "Babu zancen raini, matar ka ce ta sunna. Nan gaba ma haihuwa zaku yi tare." Kallon asan idanu ya yi mata kamar zai yi magana sai ya share ta yi dariya ta ce, "ka yi magana mana, ka fa a kar ta kashe ka." Banza ya yi mata bai kuma cewa komai ba ta gyara tsayuwa ta ce, "Omar wai kana siyo an kaya haka na gidan nan matsayinka na mai gida? Kamar su bread haka da safe, ku in kayan miya, ku in masu wanki, ku in guga, da sauran kayan amfani na yau da kullum, kana yi?." Ya kalle ta bai ce komai ba sai ta sassauta murya ta ce, "Omar ka san ha in aure, ka san duk responsibilities in yarinyar nan yanzu a kan ka yake. Ka duba saboda tsoronka da take ji ko akinka bata ta a shiga balle ace ta kwana, balle kuma ace ka sauke mata ha in da Allah ya ora maka a kanta. Baka san rashin lafiyarta ba balle ka siya mata magani, baka san me take so ba balle ka siya mata. Duk da iyayenta sun kawo ta da gara akwai anunun abubuwa da in ka bata fuska zata fa a maka tana da bu atar su. Tana da mai aiki da take taimaka mata da aikin gidan nan itama ita take biyanta, duk da...." Katse Didi ya yi ya ce, "Au har mai aiki ce da ita?." "Ba ma ka sani ba kenan?." "An fa a min? Wai gaibu na sani ne da zan dinga sanin abubuwa ba tare da an sanar dani ba Didi?." "Baka san gaibu ba, amma in ka tambaya za a fa a maka. Kai ka san yarinyar nan ar gata ce baza ta iya aikin gidan nan ita ka ai ba, wannan dalilin ya saka mai aiki take zuwa da yamma in ta dawo daga wajan aiki ta an yi mata gyara-gyare ta koma. Duk da mai aikin ta gidan kakarta ce amma ha in biyanta a wuyan ka yake. Har ku in wanki ita take biya, duk da akwai washing machine a ban akin akinka da nata amma baza ta iya wanki da kanta ba, ta san a gidansu ba itace take yi ba yi mata ake yi. Omar kar ha inta ya kama ka fa." Omar ya ce, "Didi duk abinda ki ka lissafa ban sani ba, ko kina so ki ce zan san abu ne ba tare da an fa a min ba?." "Baza ka sani ba Omar, amma in ka tambaya zaka sani." "Ki kai arshen maganar ki sauri nake yi" ya fa a yana sake tamke fuskarsa. Didi ta ce, "ni dai ina fa a maka gaskiya, don Allah gyara saboda gaba." Ta e baki ya yi ya ce, "Didi ba auren nan nake so ba, auren ya zo ne a lokacin da ban shirya ba. Bana so kamar yadda itama bata so, wani dalilin iyayenta ya saka suka aura mata ni a matsayin hukunci saboda ga mai munin hali na duniya gaba aya. Har gobe Ina zama a nan ne saboda ke, ba dan ke ba da yanzu ta jima da yin wani auren ma." Didi ta ji haushin abinda ya ce, tana mamakin yadda yake fa ar baya sonta kai tsaye ko nauyi bata ji, ta ce, "baka yi saboda ni in ba ai, da kayi saboda ni da ka kar i auren nan hannu biyu kun yi rayuwa kamar ko wanne ma'aurata." "Uhum in da ban yi dan ke in ba da yanzu ba wannan zanem ake yi ba. Zan bayar a kawo miki bread in" ya fa a yana niyar fita. "Ka bar shi bana ci, Kuma ka tsaya ka ci abinci." "Babu abinda zan yi a duk abinda ki ka ce" ya fa a yana fita ya bata waje. Ajiyar zuciya tayi ta tsaya kawai tana tunanin yadda zata yi da Omar, lamarinsa gaba yake in ta biye tashi sai su kai shekara a wannan rayuwar. Ita kuma Nayla take tausayi, in ba dan ita ba Ina ruwanta da rayuwarsa?. "Didi Ina kwana." Didi jin muryar Nayla sai ta juya da fara'a tana kallonta ita kuma sai wani sunkuyar da kai ta ke yi. Dariya ta bawa Didi ta ce, "Kin tashi lafiya amaryar Omar?." Nayla ta kalle ta cikin shagwa a ta ce, "Didi shine jiya harda kulle ofa." "Ya jikin ki?." "Da sau i, ban tashi da ciwon ba. Don Allah Ddi ki fito daga kitchen in nan, bara na je nayi wanka nazo nayi breakfast in." Didi ta ce, "kina can wajan mijinki ba dole na tashi na dafa miki abinci kafin ki fito ba? Kar ki damu ni na gama komai ke nake jira." Nayla kunya ta kamata, duk da ba wani abun ne ya faru ba amma sai ta ji nauyin Didi. Ta ce, "Gaskiya ban ji da i ba wallahi, ya zaki yi girki da kan ki?." Didi ta ce, "kar ki damu, ni ai ba ba uwa ba ce. Jeki ki yi wankan ki dawo." arasowa tayi ta kunna gas ta ora ruwan zafi ta ce, "YaMar ya shigo nan ne?." Didi ta ce, "eh, bai jima sosai da fita ba." Girgiza kai tayi ta ce, "naji hamshinsa, for the first time ya shigo kitchen in nan" ta fa a tana murmushi. Bata jima