Sashe 131
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka ke so mu yi mata?." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "tunanin abinda ya kamata zamu yi ba fushi ba My dear, kin ga Narma yarinya ce arama, kuma ga abinda ya faru da ita a auren ta da Ashraf, dole tana bu atar rarrashi daga wajena da ke, yin fushi ba na ki ba ne." "Dole na yi fushi fa, domin bazan amince ta aure shi ba wallahi, wallahi bazan amince ba sai dai in bani da rai. Kai ko bani da rai bazata aure shi ba, aurensa kamar cin mutunci ne a gare ni." "Calm down! Zamu san abinda zamu yi, amma ki daina nuna mata bakya so kar mu wayi gari bata nan, mu cigaba da binta a hankali sai komai ya wuce." Mum ta ce, "mu bita a hankali ta yi tunanin zamu bari ta aure shi kenan? Dear bazan iya wannan pretending in ba gaskiya, dan ko a mafarki bazan ta a bari ta aure shi ba wallahi." Dad ya ce, "zaki iya, kina son Narma na san zaki iya." Shiru ta yi bata ce komai ba amma ko me zai faru Narma baza ta auri Omar ba sai dai ta mutu. Narma kuwa tana falo tana kukan, awarta ta yi sallama ta shigo falon. Najwa ta kalle ta ta ce, "Welcome Sis, don Allah taimaka ki kai ta aki ko zata daina wannan kukan." Ri e hannunta ta yi zuwa akin Narma ta zauna da ita ta ce, "what wrong kuma?." Ta kalle ta ta ce, "Safna Faruk, I so much love him wallahi." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Yanzu me ya faru?." "Na fa awa su Dad in dai ba su amince na aure shi ba a wannan lokacin baza su sake ganina cikin farin ciki ba. Kuma zan tattara na bar gidan nan gaba aya." "Like seriously!" Ta fa a tana wara ido tana kallon ta. Narma bata ce komai ba Safna ta ce, "Narma ya kamata ki dawo hankalinki." Narma ta ce, "in dai ba auren shi na yi ba bazan ta a dawowa hankalina ba." "Shi kin tabbatar da yana sonki ne?." Ta kalli Safna ta ce, "yana sona mana, har gidan nan ya zo saboda son da yake min su Dad suka wula anta shi, yana matukar sona yana kuma aunar zama dani matsayin matarsa." Ajiyar zuciya ta yi ta kalle ta ta ce, "Narma ya kamata ki fara dawowa tunaninki ki fahimci kuskurenki, a angaren auren Ashraf kawai ya isa ki gane rayuwarki." Narma ta kalle ta matsayin ban game ba ta ce, "i'm talking about your rubbish sexy dress Narma, shine babbar matsalarki wacce ta kawo ki a wannan yanayi da ki ke ciki." Narma ta kalle ta tace, "meye ha in wannan maganar da wacce ki ke yi?." "Akwai mana, da farko kin auka Ashraf yana sonki ne ashe ba ke yake so ba jikinki da yake gani a bayyane yake so. Ya yi arin ganin kin bashi dama kafin ya aure ki kika i, amma da ya biyo ta hanyar aure ai kinga ya same ki. Narma na fa a miki tun ba yanzu ba, wannan dress in da ki ke ba farin jini zai jawo miki ba, a cikin maza goma da zasu ce suna sonki in suna ganki da wannan shiga tara a ciki jikinki su ke so Narma. Kuma suma kamar Ashraf ne, da zarar sun samu jikinki zaki fita daga ransu tunda daman ba soyayyar gaskiya suke yi miki ba. Shi kan shi Faruk in da kika haukace a kansa baki da tabbacin son ki yake yi, maybe shima irin Ashraf ne jikin ki yake so, da ya mallakeki......" "Hold on Safna!" Narma ta katse ta, suka ha a ido Narma ta ce, "Faruk yana sona, Faruk ni yake so ba body structure ina ba." Safna ta ce, "ya aka yi kika sani? Shi Ashraf in kin yi tunanin ba son ki yake yi ba?." Narma ta yi shiru bata amsa ba Safna ta ce, "Baki yi tunanin haka ba saboda baza ki fahimta ba, yana yin duk abinda yake yi ne dan ganin ya mallakeki ya samu jikinki daga nan kuma ya tsallake ki tunda amfaninki ya are a wajansa. Narma let me give you example, ki auki alawa ki cire ta daga jikin ledarta kin ajjiye, kin auko wacce take a rufe a jikin ledarta ki ajjiye a kusa da ita. A cikin wacce aka bu e da wacce take rufe wacce ce flys zasu fi zuwa kusa da ita?." Narma ta yi shiru bata amsa ba Safta ta ce, "ki bani amsa mana." Narma ta ce, "the opened one." "That's the real example of you. Wannan wacce take a bu in kece, wannan flys in da suka mamaye kuma mazan da suke yi miki caa, ko yaushe suna cewa suna sonki bayan ba so bane kin kasance a bu e ne shiyasa suke zagaye dake. And the closed one is Ikram, yes ikram wacce Ashraf zai aura yanzu. Yarinyar ko a social media ko yaushe jikinta a rufe yake, bata ta a bu e wani angare na jikinta balle wani ya gani yayi sha'awa har ya nemeta. Wannan shine dalilin da ya saka Ashraf yake matu ar sonta saboda Allah ba saboda jikinta ba." Narma ta ce, "yanzu so ki ke na koma saka hijjab kenan? Kuma meya amfanin halittar da Allah ya yi min in ban yi kwaliyya dashi ba?." "Noo ni ban ce haka ba, amma kalle ni don Allah" ta fa a tana tashi tana juyawa a gabanta ta ce, "kin ga wani angare na jikina a bu e?." Narma ya auke kai ta ce, "to ke abayar ma in zaki saka sai kin bawa wannan shegen tailor nan naki ya yi shaping inta sannan zaki saka, a ganinki shine daidai kuma shine za a kalle ki ace ana so, kuma shine zaki fito a Barr Narma ar Sentor Sagir. You fail Narma, this is your failure, wallahi kin fa i indai wannan ne tunaninki. Abu mai arha a ko yaushe ya fi customers, abinda ya kasance mai tsada sai wanda ya san mahimmacin sa ne yake zuwa inda yake. Amfanin surar da Allah ya yi miki ki yiwa mijinki ado a gidansa, ki yi masa kwalliya ta auki hankalinsa Allah ya rubuta miki lada. Amma in ki ka bu e wani waje har wani ya gani ba, ko wani ne ya ji wani abu ransa sai Allah ya kama ki, in ya ce Allah ya isa wallahi sai ta kama ki. Maybe ha in mazan da ki ka auka ne ma ya saka komai ya canja miki." Narma ta ce, "ni ban kira ki ki yi min wannan maganar ba, na kira ki saboda Faruk, ina so na san inda yake da kuma me yake yi yanzu." Safna ta ce, "gaskiya dai na fa a miki, in kin ga zaki gyara fine, if not zaki ta shan wahala a wajan maza. Saboda babu namijin da zai miki son gaskiya sai dai saboda jikinki." Ta koma ta zauna Narma ta ce, "ni fa ba bu e jiki nake yi ba." "Meye marabar kayan da ki ke sakawa da tsirara in Narma?." Narma ta auke kai bata ce komai ba, Safna ta kalle ta ta ce, "me ki ke so na yi miki?." "Ina so ki yi min bincike akansa, a inda yake zaune da komai da komai nasa." "Zan yi ari in sha Allah, duk abinda na gani zan sanar dake. Amma ina so ki kwantar da hankalinki, sannan ki daina wannan dress in dan ko a yanzu kin ga disadvantages insa." Narma ta yi ajiyar zuciya tana kallon Safna ta ce, "zan daina." "Better, shi kansa Faruk in in ya ganki da shiga mai kyau ta musulunci zaki fi burge shi." Jin ta sako maganar masoyin ta sai ta yi murmushi ta ce, "da shigar kafirai nake yi?." "Har gwara ta kafirai ma akan wacce ki ke yi, na sha fa a miki bakya ji, saboda su Nasreen suna zugaki suna ce miki mai figure eight kanki yana fashewa saboda ke ga mai shape ko?. Yanzu gashi kin jawowa kan ki bala'i, ni nayi mamaki ma da har ki ka yi aure ba a yi disvirgin inki ba. Dan yadda maza suke haukacewa a kan ki tsaf wani zai yi raping inki wallahi. Allah ya sa Tiger in ma bai manta dake ba." Narma ta ce, "Allah yasa yana lafiya zaki ce, dan na san Faruk ina har yanzu yana sona." Safna bata amsa mata ba ta ciro sim card in ta mi a mata ta ce, "Sabo ne, bani nayi register ba sister na ce. Zaki iya amfani dashi." Narma ta kar a tana murmushi ta ce, "Thank you my friend." "Amma wanne amfani zaki yi dashi?." "Zan kira Faruk dashi, tunda nayi aure ya yi blocking number ta. Zan kira shi ko na yi masa message." Safna ta ta e baki tana mamakin ko ina class in Narma ya je oho, gaba aya ta haukace akan wannan Faruk in kamar shine autan maza na duk duniya. Komai Faruk, motsi ka an Faruk, mafarki Faruk, tunani Faruk Duk ta rasa nutsuwarta ta dalilin shi, tunda ta fara sonsa har kawo yanzu bata sake samun sukuni ba. Safna ta ce, "gaba aya kin koma wata mara aji akan wannan Faruk in." "I love him so much, in ban aure shi ba ji nake zan iya rasa raina Safna." "In kuma ya yi aure fa? Ya zaka yi?." Narma ta yi shiru tana kallon Safna alamun tunani kafin ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah ma bai yi aure ba, In ma ya yi auren na san yana sona, zai iya sakinta ya aure ni" ta fa a cikin arfin guiwa tana kawar da fuska gefe. Safna da mamaki take kallon ta kafin ta ce, "oh really?." "Yes, in ma bai saketa ba zai aure ni naje a matsayin matarsa ta biyu, amma matayina da nata a wajansa da banbanci. Yana sona sosai, yana sona fiye da wacce yake aure, zai bani mahimmaci fiye da ita. In ma ya yi auren kenan, dan na san bai yi auren ba.." Safna ta