← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 205

Sashe 47

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nata ya yi arfi, ya tashi daga hawaye ya koma kuka mai sauti ta ce,"Ka....yi....h u....ri YaMar......"yadda taja arshen sunan tana kuka ya ba wani sabon style da ya sake jefa shi a wani yanayi na daban. Ajiyar zuciya ya yi dan gaba aya ya sauka daga dokin fushin da ya hau, ya kunna motar suka fita daga asibitin yana tafiya a hankali. Kukan na ta ya dame shi, tun yana jin sautinsa a kunnensa har ya koma jin sautin a zuciyarsa, babu macen da yake damuwa da kukanta sai Didi, baya so ya ga Didi tana kuka ko ka an lokaci guda sai ya tashi hankalinsa. Abinda yake ji game da kukan Nayla yafi wanda yake ji akan kukan Didi, ratsa zuciyarsa kukan yake yi yana nutso a cikin jininsa. Bai san ya runtse ido ya bu e ba sai da ya kalli gefenta ka an sannan ya ce "ki bar wannan kukan!." Yadda ya fa a a kausashe ya saka ta dakata tana cewa, "bana na ata maka rai ne, bana so ka dinga yi min fa a ko ka an." Kallon ta ya yi suka ha a ido yaga yadda idanunta suka yi ja sai ya auke kai yana mamakin wannan kukan nata kamar daman akan ga ar yin take. Goge ido take yi a hankali ya sake cewa, "na ce ki bar kuka." Nayla jin ya sassauta murya sai ta ce, "to" a sanyaye tana jingina da kujerar tana kallon titi. Sai kuma ta auki wayar tana duba hotunan Babyn ta yi murmushi ta yiwa hoton kiss, ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba ta ce, "YaMar ka ga hoton babyn, tana da kyau ko?" Ta fa a tana haska masa wayar. Juyowa ya yi ya kalla ka an ya auke kai bai ce komai ba. Murmushi ta sake yi ta ce, "Twiny na ta iya haihuwa, ji nake kamar na taho da babyn gida" ta fa a tana sake zooming hoton tana gani. Shi dai bai tanka mata ba amma ya yi murmushi a zuciyarsa yana cigaba da tafiya a hankali. Wani check up suka ga ana yi a kan titin har aka zo kansu. Sauke glass ya yi kamar yadda kowa yake yi ya kalli officer in da yake tsaye. Officer in ya ce, "Ah Tiger na mu" ya fa a yana bashi hannu shima Omar ya bashi hannu suka gaisa. "Daga Ina haka?." "Unguwa" ya bashi amsa a ta aice a kuma asaitance. Office ya ce, "kwana biyu, fatan komai Lafiya?." Omar ya ce, "lafiya, ya aiki?." "Alhamdu lillah. Wannan Madam ce?" Ya fa a tana kallon Nayla da take kallonsu. Kafin ma ya bashi amsa officer ya ce, "Madam barka da dare." Nayla ta ce, "barka dai." Zai sake magana Omar ya ce, "na gode" ya fa a tana aga glass in ba tare da ya sake cewa komai. Nayla mamaki tanke yi ya akayi an sanda suka san shi? Ko dan ya kasance mai aikata laifi ne a baya?. Shi dai bai kalle ta ba abinda yake gabansa kawai yake yi kuma tu i a hankali kamar baya so su je gida. Wajen tarin an shaye-shaye suka da suke zaune a gefen titi ga makamai a gefen su suka zo. Har ya gota sai kuma ya tsaya ganin sun tsayar da wani mai machine ya san da yar basu wace masa machine in ba kuma sun cutar dashi ba. Baya ya yi a hankali a daidai lokacin da suke shirin cutar mai machine in ya sauke glass ya ce, "kar wanda ya cutar dashi!." A tare duk suka juya suna tunanin wanne mai arar kwana ne wannan yake magana cikin bada umarni. Ha a ido da shi ya saka su yin ihu a tare da fa in, "Allah ya biya Damisa!." Kallon Nayla ya yi da take kallon sa bai ce komai ba ya aga glass in ya fita daga motar. Tana ganin su suna magana kuma ta ga mutumin da suka tsayar ya tafi basu yi masa komai ba. Magana ta ga suna yi sosai har ya saka hannu aljihu ya basu ku i yana murmushi kafin ya bu e motar zai dawo. Gaba ayan su sun rako shi bakin motar yana bu ewa ya ce, "To ya isa haka, na gode. A daina fitina bata da amfani, duk wanda ya shirya ya yi min magana Ina da wajan ajjiye shi." "Godiya mu ke Damisa, Allah ya bar ka da Madam." Bai ce komai ba ya bu e ya shiga ta ja motar da sauri yana murmushi. Kallonsa tayi ganin yana murmushi bata ce komai ba amma taa mamakin yadda ya hana su cutar da wancan, sannan gashi ya yi magana da an sanda ya kuma zo yana magana da abokansa na baya. Meyasa suke girmama shi har haka? Bata ce masa komai ba har suka je gida ta sauka daga motar, a ofar gidan suka samu yaransa suna nan, aka bu e gate in aka shiga da motar itama ta shiga gidan. A falo ta tsaya tana jiran shigowarsa, ba jimawa sai gashi kuwa ya shigo ta mi a mata key ta kar a ta ce, "Na gode YaMar, Gobe in Allah ya kaimu zan je gidanta." "Allah ya kaimu" ya fa a yana shiga ciki ta amsa da amin itama ta shiga ciki. Kamar yadda ta ce kuwa da safe sai tafi gidan Twiny, tun safe har magriba sannan suka dawo tare da Salma gaba aya jikin Naylan a sanyaye. Yanayin da take ciki ne ya saka Salma ta bita ciki tana ta rarrashin dan kuka take yi sosai. Ta ce, "Haba Nayla meye na kukan don Allah?." Zata yi magana Didi ta kira Nayla a waya ta auka ta ce, "Didi barka da dare." "Barka dai Nayla, an samu aruwa." "Eh Didi." "Allah ya raya mana ita." "Amin Didi." Didi ta ce, "tana gida ai ko?." Nayla ta ce, "eh tana gida, amma gobe da zasu wuce Kaduna." "Kaduna! Na auka a nan zata zauna ai." "Ai kowa na dangin mijin yana can itama kuma kinga haka, aiki ne kawai ya kawo shi nan shiyasa zasu koma." Didi ta ce, "kai amma ban ji da i ba, bara yalla ai ya zo ya mi a ni na yi mata barka bazan jira har sai ta dawo daga Kaduna ba." A sanyaye Nayla ta ce, "To Didi." Yadda Didi ta ji maganar ta san tana cike da damuwa kuma ta san damuwar bai wuce tuna gida ba, in ba dan auren Omar ba da yanzu da ita za ayi shagalin haihuwar nan amma yanzu babu ita. Sallama suka yi Didi bata tambayeta abinda ya faru ba dan ta san amsar, kuma a ganinta abinda ya faru family issue ne bai shafe ta ba. Salma ta kalle ta bayan ta kashe wayar ta ce, "meyasa ki ke kuka don Allah? Ki yi ha uri mana dole ne zuwa Kaduna?." Ta kalli Salma cikin kuka ta ce, "Salma Twiny fa, komai tare mu ke yi, tare muka tashi muka yi komai. Sunan arta ta fari ace babu ni za a yi ai dole na yi kuka." "To ya zaki yi? Ko zaki je ne?." "A gaban ku dai Abiy ya ce kar na sake zuwar masa gida sai ya neme ni, ta ya zan je masa gida yanzu bai neme ni ba?." "To ki yi ha uri, ni kukan ne bana so naga kina yi." Nayla tayi murmushi kawai ta ce, "Salma ni ka ai na san abinda nake ji a zuciyata. Mahaifina ya ce kar nazo masa gida sai ya neme ni, akwai abinda ya kai wannan ta a zuciya da sanya zubar hawaye? Tunda na zo gidan nan ko video call ban yi dashi ba, ke kin san yadda nake da Abiy dole na shiga damuwa." "Na sani, amma ki yi ha uri." "Na yi Salma." Ta fa a a sanyaye ta jingina da kujera. Da yar Salma ta rarrasheta sannan ta tafi saboda dare ya yi har an yi i'sha. Omar duk ya ji abinda aka tattauna, yana mamakin wai meye dalilin mahaifinta na aura masa ita? Me tayi masa har ya ce kar ta zo masa gida?. Yana zaune a aki yana tunani babu mai bashi amsa haka ya kawar da tunanin daga zuciyar sa. Narma ta ware sosai ta samu sau i sai dai ta zama shiru-shiru babu magana sai ta zama dole, ko yaushe tana aki, ko aiki ta daina zuwa, bata hira da kowa sai ta ga dama. Mum ta yi mata fa an har ta gaji ta share ta itama, kuma har lokacin laifin Omar take gani shine ya saka arta a wannan yanayi. Da daddare suna zaune a dining tana juya spoon in hannunta plate in gabanta tana yiwa abincin cin yanga. Dad ne ya kalle ta ya ce, "Daughter me yasa ki ke haka?." Ta ajjiye spoon in ta ce, "Dad me na yi?." Dad ya ce, "kin koma wani iri ko magana bakya yi, hakan daidai ne a rayuwarki?." Kawar da kai ta yi ta ce, "Dad kawai bana son hayaniya ne." Dad ya kalli Mum da take kallosa suka yi mata shiru bata ce komai ba. Bu ofar falon aka yi aka shigo duk suka kalli wanda ya shigo suna mamakin ganinsa. Dad ya mi e tsaye ya ce, "Ashraf! me ka zo yi gidan nan?." Ashraf ya ce, "Dad I just come here because of my wife, I need to take her out." Mum ya mi e tsaye ta ce, "You're not serious Ashraf. Let me tell you something, Narma ta gama auren ka wallahi. Divorce paper zaka bata ko kana so baka so." Ashraf ya ce, "Mum bazan sake ta ba, Ina son zama da matata." Dad ya kalle shi cikin fusata ya ce, "Ashraf ka fita ka bani waje, zan yi magana da babanka baza ka kuma zaman aure da Narma ba har abada." Ashraf ya kalli Narma ta da take zaune tana kallon sa ya kalli Dad ya ce, "Dad gaskiya bazan sake ta ba, Ina son matata, babu wanda zai saka na sake ta." "Dole ka sake ni Ashraf ko baka so!" Narma ta fa a tana tasowa daga inda
Chapter 47 · 0% Book details