← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 205

Sashe 85

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba. Yana cize baki ya mi e tsaye ya duba maganin da ya ta a siya na zazza i ya auko, fita ya yi ya auko ruwa ya dawo inda take ya tallafo kanta ya saka mata maganin a baki ya kafa mata robar ruwan amma sai yaga ruwan yana dawowa kamar yana bawa gawa ruwa. Hankalin Omar ya tashi fiye da azu, a firgice yake cewa, "Jidda! Jidda!! Ki yi magana in kina jina, kina jina....? don Allah ki ce wani abu. Kar ki saka zuciyata ta buga mana, ki yi magana, ki yi magana naji don Allah, ki ce wani abu ko zan ji da i!" Abinda yake fa a kenan cikin fitar hayyaci. Kiran sallar asuba da ya ji ya saka shi tsayawa cak yana mamakin gudun lokacin, inda yana da arfi da lafiya asibiti zai kai Nayla amma bazai iya ba, bazai iya fita a wannan hali ba. tsaf sai su yi hatsari. Wayarsa ya jawo ya shiga number Didi yana kallo amma ya kasa kira, ajiyar zuciya ya yi, bashi da wata in ba Didin ba dole ita zai kira ta zo ta taimaka masa kar Nayla ta mutu ya shiga uku. Danna kiran ya yi ta gama ringing amma Didi bata auka ba, ya sake kira a karo na biyu nan ma bata auka ba, ya ajjiye wayar yana ji kamar ya yi ta dukan kansa saboda takaici da ba in ciki. In ya bar Nayja a haka ta mutu ya zai yi? Wanne hali zai shiga?. Ya juya ya kuma kallonta ya sauke ajiyar zuciya ya dafe kan da yake barazanar tarwatsewa. Yana ji aka tayar da sallar asuba amma bazai iya motsi ba, yana zaune har aka idar da sallar ya kasa motsawa daga wajan. Ana idar da sallah kiran Didi ya shigo wayarsa, da hanzari ya auka ya ji muryarta a firgice tana cewa, "Omar lafiya? Me ya faru?." Bai ma ji me take cewa ba ya ce, "Didi ki zo, na rasa me zan yi, ki zo ki taimaka min. Jidda zata mutu, ki zo!" Abinda yake iya fa a kenan yana lumshe idanunsa. Wayar fa uwa tayi a hannunsa ya sunkuyar da kai ya rasa abinda zai yi. Kallon Nayla ya yi da take yadda ya barta numfashin ma baya fita, ruwan da ya taru a idanunsa suka fara sauka tamkar hawaye, hawaye yake yi na ba in ciki da takaicin kasa taimakonta da ya yi. Yana kallon ta a kwance, ita ba sumammiya ba ita ba wacce take hayyacinta ba, ya kasa yi mata abinda zata ji da i zaza in jikinta ya rabu da ita, ya kasa yi mata komai. Ya kasa sakawa ta dawo daidai, ya rasa abinda zai yi mata wanda zai sakata dawowa hankalinta. Tunda yake a duniya bai ta a zubar da hawaye akan komai ba sai a yau, ya kasa ri e hawayensa sai da suka sauka dan yana ganin komai laifinsa ne, shine yayi gaggawa ya kai kansa inda bai ta a zuwa ba, shine ya kai su inda basu ta a zuwa ba ba tare da yana da ilimi a kai abun ba, gashi gaggawa ta kai shi ga zubar da hawaye, ya kasa yi mata abinda zata iya ko da magana ne balle kuma ta iya tashi. Ya manta ma zai yi sallah, sai daga baya ya mi e da yar ya yi alwala ya dawo ya yi sallar a zaune dan bazai iya sallah a tsaye ba saboda jiri, yana idarwa ya koma inda take kwance, har lokacin numfashi ta yana sauka amma a hankali. Kiran wayarsa ya ji ana yi bai iya auka ba har ta katse, aka sake kira bai auka ba, sai aka kira sau biyar sannan ya iya jan wayar da take kife a asa ya auka. A rikice Didi ta ce, "Omar gani a ofar gidan, ka zo ka bu e min." Runtse ido ya yi yana tunanin ta ya zai iya fita ya bu e gate? Ciwon da yake ji tunda yake a duniya bai ta a jin irinsa ba, ji yake kamar iska tana aukarsa tana hujijjiga shi a sama in ya tashi tsaye, amma dole zai daure ko dan saboda ita. Yana ha a hanya ya fita, yana fita compound in gidan ya ji sanyi na ratsa ko ina na jikinsa, ya bu e gate in Didi ta shigo a firgice mijinta yana jikin motarsa a tsaye shima hankalinsa a tashe. Didi ta ce, "Omar lafiya ka ke? Omar!" Ta fa a da arfi ganin yana arin zubewa a wajan. Da sauri AbdulHamid ya shigo ya ri e shi yana cewa, "Subahanallah! Omar Bba ka da lafiya haka?." Didi ya kalla da idanunsa da suka koma jajaye ya ce, "Didi, Jidda!." Da hanzari ta shiga ciki shi kuma AbdulHamid ya ri o shi suka dawo falo ya zaunar da shi yana jera masa sannu. Didi akin Nayla ta shiga amma bata ganta ba, ta fito ta ce, "tana ina?." Da hannu ya nuna mata akinsa ta bu ee ta shiga. Da sauri ta arasa inda Nayla take tana kiran sunanta amma ta ga kamar Nayla bata numfashi. Didi ta ce, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Me yake damunsu haka? Nayla! Nayla!" Ta fa a tana jijjigata amma ita Nayla bata san tana yi ba. A guje Didi ta fito ta ce, "Yalla ai asibiti zamu je, dukkan su basu da lafiya." AbdulHamid ya ce, "To bara mu je mota dashi, ku fito tare da ita" ya fa a tana kallon Omar ya ce, "Omar daure ka tashi mu je asibiti, daure ka mi e." Omar ya i tashi saboda ya san dai Didi bazata iya fitowa da Nayla daga aki ba, to ta ya za a tafi asibiti kenan?. Didi kuwa da sauri ta dawo akin Nayla ta samu doguwar riga mai an kauri a kayanta, ta koma akin ta ora mata a kan rigar jikinta ba tare da ta cire ba. Ta fito ta kalli mijinta ta ce, "kamar a sume fa Nayla ta ke, ta ya zamu fito da ita?." Omar yayi caraf ya ce, "zan iya." AbdulHamid ya ce, "baza ka iya ba Omar, baka da lafiya kaima, ta ya zaka iya auko ta?." Omar yana jinsa amma baya tunani zai iya bari shi ya auketa, dan in dai ba shi in ne ya auke ta ba to tabbas shi ne zai maye gurbinsa, saboda ya san aikin ya fi arfin Didi. Shi kuwa da hakan ta faru gwara ya aukota koda suna tafiya suna kifawa ne ya amince da hakan. Omar ya ce, "zan iya" ya fa a yana wuce shi ya shiga akin ya auko ta kamar yarinya, da yar da si in goshi ya iya fitowa falon, AbdulHamid ya ri e shi, shi kuma yana ri e da ita a haka aka fita yana tanga i har motar mijin Didi. Didi ta kalle shi ta ce, "Ina key in gidan?." Cikin gidan kawai ya nuna mata ta shiga tana ta dube-dube amma bata gani ba, key in motar Nayla ta gani kawai ta auko ta fito da sauri ta kulle gidan ta shiga gaban motar suka tafi asibiti a guje. Basu tsaya bi ta kan asibitin gwamnati ba, kai tsaye aramin private suka wuce dan abin na gaggawa ne ana kuma bu atar hanzari da aikin gaggawa saboda a taimaka su dawo hankalinsu. KRB3P049 Duk su biyun kwantar da su aka yi, ko wanne an saka masa ruwa yana shiga jikinsa saboda yadda jikin na su ya yi laushi dole sai sun sha ruwa. Bayan an gama daidaita komai dukkan su sun samu bacci hankali Didi ya kwanta, ta kalli nurse in ta fito daga akin ta ce, "Don Allah me ya same su haka?." Nurse in ta ce, "Ni gaskiya ban je kanta ba, shi dai jikinsa ne ya yi weak sosai, sai zazza i mai zafi da ciwon kai, amma yanzu ya samu bacci." Wata Likita ce ta le o daga akin ta kalli Didi ta ce, "Sister ji mana." Didi ta arasa kusa da ita ta kalli Didi ta ce, "mata da miji ne?." Didi ta ce, "eh." "Ya ku ke dasu?." anina ne uwa aya uba aya." Ta girgiza kai ta ce, "Sabon aure ne?." Didi ta ce, "eh to, sabon aure ne." Dr ta ce, "Akwai abinda nake expecting ne shiyasa nake tambayarki, lokacin barina aiki ya yi amma saboda su na tsaya. Ko dai they had their first night ne? Ina nufin ko dai sun kusanci juna a karo na farko ne?." Didi ta kalli Dr gabanta yana fa uwa ta ce, "it might be." Dr ta ce, "let me check" ta fa a tana komawa ta bar Didi da tunani. Kenan in hakan ne dalilin da ya saka Nayla suma kenan? Suma fa, har ya sumar da ita saboda wannan kawai?. Tausayin Nayla ya mamaye mata zuciya, ta koma inda take zaune ta zauna ta yi shiru ta rasa abinda zata ce. Dr da tayi mata magana ta ga ta fito daga akin ta kira wata sun shiga tare basu ce mata komai ba. Sun jima kafin su fito ta kalli Didi da take zaune kusa da mijinta ta ce, "Sis zo ki ji." Ba musu Didi ta mi e ta arasa inda take ta kalli Didi ta ce, "abinda na yi hasashe haka ne ya faru. Amma wannan ani na ki anya ba maganin arfin maza ya sha ba? Kin ga irin aikin da ya yiwa yarinyar nan kuwa?. Gashi kuma da alama ba ta shiga ko an ruwan zafin nan da ake taimakawa amare ba. Duk da dai shima bashi da lafiya sosai, amma ya kamata ace an taimaka mata." Didi ta yi ajiyar zuciya, kunya duk ta bi ta rufe ganin AbdulHamid yana wajan kuma yana ji, duk da dai sun an yi nisa da inda yake amma ta san zai juyo dan ba a hankali take magana ba. Nurse in da take tsaye kusa da Dr ta ce, "Lamarin ya dangana ga inki, amma ba wai sosai can ba, kuma kyau samu ta kwana a nan zuwa gobe ko jibi yadda za a kula da ita in ya so sai ta koma gida." Didi
Chapter 85 · 0% Book details