Sashe 136
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
e ba Omar" ta fa a tana zama akan kujera shima ya zauna da Marmerh a hannunsa. Didi ta kalle shi ta ce, "Yanzu sai me..." kafin ta arasa aka kirata a waya, ta duba ta ga Mama Zainab ce ta yi murmushi ta ce, " an uwa sai kira na suke yi a waya, iya wannan ma abin alfahari ne." auka tayi tana amsawa, itama Nayla Abiy ne ya kira ta yana kashewa ya kira Omar. Omar da ya auka murna dai Abiy yake taya shi daga nan ya kashe sai ga Yayan Nayla ma ya kira shi. Zaman falon gaba aya amsa waya yake yi shida Nayla, sai da akayi kiran sallah sannan suka fita shida AbdulHamid aka bar su Didi. Kafin su dawo Nayla ta kawo abinci, Omar yana zama Didi ta ce, "yanzu sai meye abu na gaba?." Omar ya ce, "Sai zuwa gobe zan san abinda za a yi." Didi da fara'a da alfahari ta ce, "Allah ya kaimu." Ya amsa da amin daga nan bai sake cewa komai ba, Marmerh tana hannunsa ta yi luf a jikinsa har ta yi bacci. Nayla da ta dawo daga rakasu Didi zama tayi suna waya da Jidda tana fa a ta shiga comments section taga an matan da suke son mijinta. Bata bi ta kan maganar an comments section ba hoton ta tsaya tana kallon, yana tsaye a tsakiyar an China, su biyu suna gefensa kowa ya ri e takardar aka yi hoton. Ya yi matu ar kyau sosai, in ka kalle shi sai ka sake kallo saboda yadda ya yi kyau kamar ba shi bq. Ajiyar zuciya ta yi ta tashi ta shiga aki. Kaya ta canja zuwa na bacci ta shiga akinsa ta same shi a zaune yana duba waya ta shiga ta zauna ya kalle ta amma bai ce komai ba. Nayla ta ce, "YaMar!." Kallon ta ya yi bai ce komai ba ta ce, "ka yi ha uri." "Laifin me ki ka yi?" Ya fa a ba tare da ya kalle ta ba. Kafin ta yi magana ya ce, "kinga lokacin farin ciki ne yanzu, ki adana damuwar nan taki mu fuskanci abinda yake gaban mu." Nayla ta ce, "amma fushi ka ke yi dani." "Ni ba fushi nake yi dake ba. Mun yi magana da Didi tace ya kamata ayi sadaka da saukar alkur'ani, dan haka zata yi abinci za a yi sadaka, sannan akwai wannan malamin da na baki labari, na samu ansa na ce ayi saukar alkur'ani sannan na bada ku i na ce ayi sadaka. auyensu Bash inda an uwansa suke suna da bu atar ruwa sosai, shima na tura ku in yanzu za a yi musu ruwa guda biyu. aya da niyar Allah ya ji an iyayenmu nida ke, aya kuma sadaka akan abinda ya faru da wanda ma zai faru gaba." Nayla ta girgiza kai cikin gamsuwa ta ce, "Hakan ya yi, Allah ya amsa mana ya ji an iyayen mu." "Amin. Sai me ki ke ganin za a yi? Na san baza ki iya aiki mai yawa ba shiyasa nace Didi abincin." "Duk aya ne." "Me ki ke ganin ya kamata bayan wannan?." Nayla ta ce, "Ai duk abinda ya kamata in ka yi, amma akwai asibitin nan na cikin gari mun ta a zuwa da Hajja wani lokaci da nazo Kano, akwai masu bu ata sosai, sai ka ga mutum yazo ga rashin lafiya amma babu ku in magani." Omar ya ce, "to me ki ke ganin za a yi?." "Mu shiga gobe da daddare, duk mara lafiyan da yake ciki mu basu sadaka, wani ko ku in abinci ba shi dashi. Ko mutum biyar aka taimakawa mun gode Allah." Omar ya girgiza kai ya ce, "Allah ya kaimu goben." "Amin ya Allah. Shiyasa ka ke cigaba a rayuwar ka, duk abinda ka samu ka farantawa wani da abin da ka samu wallahi Allah bazai barka ba, sai ya ninka maka ninkin abinda ka samu. Allah ya dafa maka Rouhii." "Amin Ashiq!. Na tashi da yin sadaka gaskiya, ban sani ba a jinina abin yake ko kuma dan Didi ce ta raine ni ban sani ba. Didi akwai ta da taimako, ta yarda ta rasa inda wani zai samu, ko ku inta kenan tana iya yin kyautarsa ta ce Allah zai bata wani, shiyasa nima na bu e ido da yi. Kuma Malamina marigayi Malam Salahudeen a duk sanda na je wajansa yana fa a, duk abinda na samu kar naci ni ka ai na kyautatawa na kusa dani, kuma na bawa wanda bashi dashi. Tun bana aukar nasihar saboda yadda nake a lokacin har ta shiga jikina. Yanzu ina ganin amfaninta sosai, kuma zan iya cewa itace silar nasarata a rayuwa." Nayla ta ce, "Gaskiya ne, Allah ya cigaba da bamu ikon taimakawa wanda bashi dashi." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Amin ya rabbi. Mutanen Kaduna sun yi min waya suna ta taya ni murna" ya fa a yana kallon ta da murmushi. Ta yi murmushi ta ce, "Abin murnar ne ya samu, dan ma an mata suna ta tanka min kai, ni kam ina ta fa a tabarakallahu asanul khaliqin!." an girgiza kai ya yi ya ce, "kin kyauta." Ganin yadda ya amsa mata kawai ta san ba a an kirkin yake ba. Ya mi e tsaye ya ce, "Bacci zan yi." Nayla ta ce, "nima haka." Tare suka kwanta amma hannunsa bai zo inda Nayla take ba, zuciyarta na son kasancewa dashi amma gangar jikinta bata so. Da kanta ta matso jikinsa ta kwanta bai hanata ba ya yale ta dan bazai neme ta ba sai dai ta neme shi. Labari ya baza duniya, ana ta cecekuce ana ta yiwa Omar fatan alkhairi da nasarar da ya samu. Abinda yake trending kenan a media a kwanakin, ba kamar hoton Omar da yake aukar hankali, kallon farko zaka yi masa ka fassara shi a an gata gaba da baya, saboda kyuan da Allah ya yi masa. Abu kamar wasa ig account insa ya cika da dms, kuma yawanci duk mata ne, shi abin ma dariya yake bashi ko bu ewa baya yi balle ya ce zai basa amsa. KRB3P83 Nana haleema Bayan kwana biyu da yin abun ranar Monday Nayla ta tashi da azumin godiya ga Allah, ta yi mamaki da ta ce masa zata yi azumi bai tanka ba ya ce Allah ya bada ikon yi, a nan ta tabbatar da warai fushi yake yi da ita. Sai ta ure yake ri e hannunta, amma hugging ko kiss duk ya daina, hakan yana damunsa shi kansa balle ita da take ganin laifi tayi masa. Bayan ta sha ruwa ya shigo falon ya zauna ya kalle ta ya ce, "Kin sha ruwa lafiya?." "Lafiya lau." "Ina tunanin jibi zan koma China tunda akwai visa, akwai takardar da zan saka hannu a can, kuma akwai kayan da zan siyo saboda zamu fara tura musu kaya a wannan watan." Nayla ta kalle shi ta ce, "Jibin zaka je?." "In sha Allah." "Ka siyi ticket in ne?." "A'a ban siya ba, yanzu maganar zuwan ta tashi ke na fara fa awa." "Allah ya kaimu." "Amin." Ta sake kallon sa ta ce, "tare zamu je din?." Kallon ta ya yi na wani lokaci, kafin ya janye ido ya ce, "A'a, ina yi miki batun tafiya jibi kina zancen tare zamu je?." Nayla a sanyaye ta ce, "Amma ka ce baza ka sake tafiya ka bar ni ba." Ya an shafa kansa ba tare da ya kalle ta ya ce, "in na je dake yanzu amfanin me zaki yi min? Damuwa zaki ara min kawai." Kallon sa tayi da mamaki, kafin ta yi magana ya ce, "A ina zaki zauna in na tafi?." Muryarta ta fara rawa sosai ta ce, "Wajan Hajja." "Baza ki je Kaduna ba?." Ta aga kai alamun eh hawaye na sakko mata. Sai ta karya masa zuciya, yana matu aunarta yana kuma tsananin bu atarta amma ya rasa abinda ya yi mata take gudunsa, shiyasa yake bata space bai sani ba ko akwai dalilin ta na yin hakan. Kusancinsu cutar dashi ya ke yi, shiyasa yake baya baya da ita. Ita kuma sai ta ke gani kamar ya canja mata ko ya daina sonta bayan ba haka bane, shi ka ai ya san halin da yake ciki na rashinta. A hankali ya ce, "Meye na kukan?." Kamar jira take ya tanka ta fashe da kuka mai sauti, ya yi ajiyar zuciya ya taso ya zauna a kusa da ita ya ce, "Jidda!." Bata kalle shi ba ta kwanta a jikinsa bashi da za in da ya wuce ya ri eta a jikinsa amma shi ka ai ya san illar da hakan zai masa. Bayanta yake trapping a hankali ya ce, "ki bar kuka Ashiq, ko kina so na yi kuka ne nima?." Ta girgiza kai tana kuka ta ce, "ka....dai....na....so....na....Rouhi!." "Shiii! Har abada bazan daina sonki ba Jidda, da sonki Allah ya halicce, da sonki zan bar duniya, da sonki zan tashi har a aljanna. Babu wani dalili da zai saka na daina sonki, ina baki space ne kawai." "Ka yi ha uri!." "Baki yi min laifin komai ba Jidda, ki daina kukan mu yi magana." Ta ago daga jikinsa tana kallonsa, ya share mata hawaye ya yi mata kiss a goshi, ta lumshe ido jin umin lips insa a fuskarta, rabon da ya yi mata haka har ta manta. Fuskarta ya ri e ya ce, "Kinga tafiyar gaggawa ce ta same ni shiyasa baza mu tafi tare ba, amma in sha Allah tafiya ta gaba tare zamu yi dan na san yanzu zan dinga shiga asar a kai a kai." aga kai alamun to ya ce, "To ki yi murmushi mana ." Bata yi murmushi ba ta zuba masa ido musamman lips insa da ta missing sosai, a hankali ta ta matsar da bakinta kusa da na shi ta fara kissing a hankali. Runtse ido ya yi jin tana sake birkita masa nutsuwa, ya san abin yana yim nisa jikin zai fara rawa ta gudu. Kiran sallah aka yi ya saka shi ya janye jikinsa da hanzari, ya kalle ta ya ce, "Ki kwantar da hankalinki, zan je nayi sallah na dawo"