Sashe 59
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawo ba, tun safe muna jira har yanzu shiru." Ajiyar zuciya ya yi mai arfi ya ce, "zan auko yanzu." "Godiya mu ke" ya fa a yana fita. Lumshe ido ya yi ya bu e idon, a bayyane ya ce, "Wai me yake damun zuciyata ne? Me nake ji haka mai matu ar zafi da ciwo?. Anya ba wani ciwon ne yake damuna ba?." Babu mai bashi amsa ya sauke numfashi ya mi e ya auki key in gidan ya tafi. Yana bu e falon gidan hamshi mai da i ya doki hancinsa, ya ja numfashi ya sauke yana bin falon da kallo a hankali. Duk da akwai duhu a falon hakan bai hana shi ganin abinda yake ciki ba. Wani irin bugawa zuciyarsa take yi,har sai da ya kai hannu ya dafe zuciyarsa yana rutse ido da arfi. A hankali ya bu e ido yana jan numfashi da yar, ya sake kallon falon yana hakki kamar wanda ya yi gudu haka yake sauke numfashi. Takawa ya ke yi zuwa tsakiyar falon yana jin bugun zuciyarsa na sake aruwa jikinsa na sake yin sanyi. akinsa ya bu e ya shiga a sanyaye ya auko abinda zo gidan aukowa. Kallon inda Nayla ta zauna ranar da take ciwon kai yayi, sai ya ga kamar ita in ce har yanzu a zaune a wajan. Rufe ido ya yi ya bu e ya sake kallon wajan sai ya ga babu kowa a wajan, ya dafe kai cikin rashin sanin abinda zai yi. Daga akin ya fito yana kallon aramin falon da ya kasance mazauninta yana ji a zuciyarsa kamar tana ciki a zaune. "YaMar!" Sautin da ya ji a kunnensa kenan, ya juya da sauri amma bai ga kowa ba bai kuma ji daga inda aka yi maganar ba. Ta bayansa ya sake jin sautin, "YaMar don Allah na je!.?" Omar ya juyowa da hanzari amma still babu kowa a wajan ko wadataccen haske babu. Kalle-kalle ya ke yi a falon amma bai ga kowa ba amma komai yana nan yadda yake. Shiru ya yi yana sake arewa wajan kallo, ya rufe ido ya bu e har lokacin numfashi yake saukewa kamar wanda yayi gudu. Fita ya yi daga gidan ya kira Goje ya bashi abinda suka nema sannan ya sake komawa gidan, haka kawai yake ji baya so ya bar cikin gidan domin jin zuciyarsa yake a karye, yana jinsa kamar kwalin da babu komai a cikinsa iska na jansa. A hankali yake takawa har inda ta saba zama yana kallon wajan cikin rashin sanin dalilin da ya saka yake jin abinda yake ji. Kallon akin ya yi sai ya tuna cikin azumi da yaran nan suka shigo gidan, da yadda ya ji ihunta har tsakiyar zuciyarsa. Kai tsaye akin nata ya bu e a hankali ya kunna hasken akin yana kallon akin. Komai yana nan tsaf dashi, kallon inda ta diro daga kan gadon ta taho wajansa a guje tana neman agaji yake yi. Rana ta biyu da ya shiga akin a rayuwar da ya yi a gidan kenan, ya arasa jikin madubin akin yana kallon sauran tarkacenta da suke ajjiye a wajan. Kamar wanda ya farka daga bacci, ya yi firgigit ya kalli akin ya kalli kansa a madubin ya ce, "Wai me nake yi haka? Me yake damuna ne?" Ya fa a yana sake arewa kansa kallo amma bai ga alamun canji a tare dashi ba, shi in ne dai a tsaye a akin Nayla. Fita ya yi daga akin da sauri, yana zuwa tsakiyar falon ya sake jin an kira sunansa kamar yadda Nayla take kira. Cak ya tsaya ya waiwayo amma babu kowa, ya dafe kansa ya fita daga gidan da hanzari dan ya lura aljanu sun cika gidan. Duk yadda ya so yakice damuwar abin ya faskara, shi ba an uwa ne dashi ba balle ya fa a masa ya bashi shawara, shi ba mahaifiya ba, shi ba mahaifin ba, shi ba aboki ba. Didin dai itace kawai mafitarsa. Washe gari da yamma ya bi umarnin zuciyarsa ya kira Bashir ya ce yazo su je gidan Didi. Sai da suka je ofar gidan sannan ya auki waya ya kira ta. Didi tana zaune a falo tana tunaninsa, tayi kewarsa sosai, basu ta a irin wannan dogon fushin ba sai wannan lokaci. Ta san tana ata masa rai ya yi kwana biyu bai kulata ba, amma ba a ta a yin sati aya bai neme ta ba sai wannan lokacin. Ganin kiransa ya bata mamaki da farin ciki, ta auka da hanzari ta saka a kunne ta ji ya ce, "Ina ofar gidanki." Didi da hanzari ta mi e ta araso ta bu e masa ta tarar yana magana da Bashir kafin Bashir in ya tafi ko gaisuwa ma basu yi dashi ba. Kallon ta ya yi kamar yadda take kallonsa, in ba gizo idonta yake mata ba sai ta ga ya rame amma kuma fuskarsa ta yi haske sosai. Didi ta ce, " araso mana." Bai musa ba ya arasa har cikin gidan ya zauna ta kawo masa ruwa da lemo ta zauna a gefe ta ce, "Ka sha ruwa." aramin tsaki ya yi ya ce, "bana son sha." Didi ta bi shi da kallo ya yi shiru bai ce komai ba. "Didi!" Ya kira sunanta ba tare da ya kalle ta ba. Didi ta ce, "Na'am Omar." "kin ata min rai kuma kina fushi dani." Didi ta ce, "ni ba fushi nake yi da kai ba, kaine ka daina kirana balle ka ji lafiyata." Kallon fuskarta ya yi ya ce, "amma kin san laifinki ne ko? Duk abinda ya faru ke ki ka jawo." Didi a sanyaye ta ce, "na ji, ni ban yi dan ranka ya aci ba gaskiya na fa a maka. Kaine ka ata min rai da wannan hargagin naka har na mareka ban sani ba, amma ka yi ha uri." Kallon ta ya sake yi ya lumshe ido ya bu e ya kasa furta komai. Didi ta ce, "Baka da lafiya ne? Na ga ka rame amma kayi haske." Omar ya kifta idanu ya ce, "Nima ban sani ba Didi, nauyi nake ji a zuciyata sosai. Na auka rashin magana dake ne ya kawo hakan shiyasa nazo na ganki, amma gashi ina magana dake in ina ji kamar ana ara min nauyin a zuciyata. Anya ba wani ciwon ne ya kama ni ba?." Didi ta ce, "to me ya kawo hakan? Wani abun ya faru ne?." Omar ya an juya hannunsa ya ce, "ni ban sani ba." Didi ta bi shi da kallo ta ce, "Allah ya kawo mafita. Babu wani ciwo da ya kama ka kawai fushin da ka ke yi dani ne ya kawo hakan, haushin na yi maka fa a har na mareka a gaban matarka duk shine ya kawo hakan. Amma yanzu a hankali zaka ji ka dawo daidai, musmaman ita matar ta ka da ka ce baka so ta bar gidan ta baka space in da ka ke nema a rayuwarka. A ganina ai babu sauran damuwa kuma Omar." Kallon Didi yake baya ko kiftawa musamman da ta sako zancen matarsa sai yaji wani abu ya soke ji a zuciyarsa, har ta kai arshen maganar kallonta yake yi sannan ya ce, "yanayin nan yana damuna Didi, ban ta a jin kaina a wannan yanayin ba tunda Allah ya halicce ni." Didi ta ce, "zaka daina ji musamman in ka saukewa kanka nauyin da yake wuyanka. Iyayen Nayla suna jiran takardar sakin arsu daga gare ka, ya kamata ka je ka kai musu takardar sakin ka hutawa kan ka itama ta huta tayi aurenta a inda aka san mahimmacinta ake kuma aunarta. Da zarar ka yi hakan shikenan zance ya are, zaka cigaba da rayuwarka lafiya lau fiye da baya." "Didi na zo nan ne dan na ji sau in abinda yake damuna, na auka in na zo nayi magana dake komai zai wuce zan warware na daina jin abinda nake ji amma ban daina ba. Maganganunki sai na ji kamar ma nauyi suke sake ara min." Didi ta yi murmushi ta ce, "To Omar me zan yi maka? Gaskiya ce nake fa a maka. Kai ka ce baka son yarinyar nan, baka son aurenta baza ka ta a so ba har abada. Har wallahi ka ce, kuma na san duk abinda ka yi rantsuwa a kai gaskiya ne a zuciyarka baka canjawa, shiyasa nake fa a maka abinda ya kamata ka yi ka saukewa kan ka ha in da yake wuyanka. Ka saki yarinyar nan itama ta huta da igiyar aurenka da yake kanta, ta cigaba da rayuwarta ta yi aure ta auri wanda yake son zama da ita. In ka aikata hakan zaka daina jin nauyin da ka ke ji." Zuba mata ido ya yi yana kallo bai ce komai ba, itama sai ta yi shiru bata sake magana ba har mintina biyar sannan ta ce, "ka zuba min ido kana kallona baka ce komai ba." Sai a sannan ya janye idanunsa daga kanta ya yi ajiyar zuciya ya kulle ido ya bu e ya ce, "ban san me zan yi ba." "Sakinta zaka yi." "Ita wa?." "Nayla mana." "Hmmm!" Ya furta yana kallon wani wajan daban. In ta furta kalmar sakin nan sai yaji kamar ana soka masa kibiya a zuciyarsa, dafin dake jikin kibiyar yana tafiya har cikin jininsa yana zaga ko wanne sashi na sassa jikinsa. "Yaushe zaka je ka kai musu takardar sakin?." "Ni babu inda zan je, babu wanda ya isa ya saka ni na je inda ban yi niya ba" ya fa a a fusace yana kallonta. Didi ta ce, "ai kuwa zasu aiko maka da sammaci daga kotu. Ni na rasa wannan abu irin na ka, kace baka sonta ba sai ka saketa ba?." Ya kalle ta da idanunsa da suka fara canja launi ya ce, "Meyasa ki ka ce min ko mahaifinta ne ya ce na saketa kar na aikata hakan? Kin manta ke kika ce min haka?." Didi ta ce, "ni na fa a, na kuma san ba wai ka amince bane kawai ka ji ni ne. Kuma yanzu ni na ce ka saketa in ai, in da ni na hana yanzu ni na ce ka