Sashe 182
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sannan ya iya yin alwala ya yi sallah. Yana idarwa ya dawo ya bu e fuskarta wai ko zai ga ta farka amma bai ga alamun ta motsa ba, ya shafa fuskarta ya koma ya jingina da kujera tare da lumshe idanunsa. KRB3P114 Mutuwar ta ratsa ko ina, social media ta cika da hoton Omar da Didi da sauka auka a madina wanda ya dafata tana gefensa sanye da abaya ta yi dariya. Jidda ce ta fara ora hoton a status, kafin ka ce kwabo ya zaga inda ba a yi tunanin zai zaga ba. Duk inda ka bi zaka ganshi an rubuta Allah ya yiwa Yayar Omar Usman, C.E.O Exclusive Footwear by Tiger rasuwa, Za a yi jana'izar ta arfe tara na safe a gidansa. Gida ya cika dam da mutane da ba a san su ba ma, mutanen Kaduna duk sun zo kowa ka kalla zai kaga fuska tayi ja alamun an sha kuka. Har karfe takwas da rabi Omar yana zaune a gaban gawar, yana kallo wannan ya shigo ya yi mata addu'a ya fita shi dai bai motsa ba kuma bai ce komai ba har lokacin. Tausayi yake bawa kowa, iya kallon yanayin da yake ciki ma kuka yake saka mutane saboda kowa ya san wacece ita a wajansa, an san matsayi da girma da take dashi a gare shi. Kowa ya san Omar aka yiwa mutuwa shiyasa ake matu ar tausayinsa musamman rashin maganar da baya yi. A haukace Nayla ta fa o falon jikinta na wani irin rawa kayan jikinta sun aci da bushshen jini, ta rame lokaci aya ta koma kamar zararriya. A gaban gawar ta zube guiwa biyu hannu na karkarwa ta bu e fuskar Didi sai ta fashe da kuka. A hankali ta ce, "Didi bata mutu ba, bacci ta ce min zata yi, bacci ta ce min zata yi fa. Ku saka ta farka bata mutu ba, hannuna ta ri e ta ce min Nayla bacci nake ji, bacci take yi ba mutuwa tayi ba" ta fa a tana kallon mutanen falon wanda duk an uwan Didin ne harda Hajja a zaune tana kuka. Nayla ta mi e a firgice ta auko iv da Didi ta kawo a ajjiye akan table hannu na rawa ta ce, "kun gani, jiya ta kawo da kanta ko awa ashirin da hu u ba ayi da zuwan ta ba. Kun gani, a nan..a nan......ta zauna muna hira, A nan ta zauna...wallahi a nan ta zauna." Ta fa a murya na rawa matu a haka jikinta ma rawa yake yi. Kuka ta saka mutanen falon Mama Sa'adatu da take biyw da ita ta ce, "Nayla ki nutsu, ki nutsu don Allah" ta fa a tana kuka tana arin ri ota. Fizge jikinta tayi ta zube a gaban Omar ta saka hannu biyu ta jijjiga kafa unsa ta ce, "ka fa a musu bata mutu ba, Didi bata mutu ba, bacci ta ce zata yi fa, daga fitarka kai da Yaya AbdulHamid ta ce na bata ruwa zafi take ji, daga nan ta ce min Nayla bacci zan yi. Wallahi Didi bata mutu ba, ka fa a musu ni na fa a sun i yarda dani......" ta fa a tana kuka sosai. Omar kallon ta kawai yake yi bayan wannan babu abinda ya iya aikatawa, ya dubawa Nayla ido kawai kafin ya lumshe idon ya bu e yana ji ina ma shine ya samu damar da ta samu na zubar da hawaye, da ya fi kowa farin ciki dan nauyin da zuciyarsa take yi masa ya san tabbas zai ragu. Hajja ta kalli Mama Sa'adatu cikin kuka ta ce, "Sa'adatu ki auke Hauwa'u daga wajan nan." Mama ta taka zuwa inda Nayla take ta mi ar da ita tsaye ta ce, "ki yi ha uri Nayla, kowa lokaci yake jira, nata lokacin ya yi yanzu." Ta kalli Mama ta ce, "Lokacin ta bai yi ba, ba fa mutuwa tayi ba bacci take yi wallahi. Ni fa ta cewa na bata ruwa, na bata ruwa ta ce min zata yi bacci, ya zaku dinga cewa min ta mutu bayan bacci ta yi? Ku daina fa a bana so" ta fa a tana janye jikinta daga na Mama ta sake komawa inda Didi take kwance. "Didi! Didi!! Didi!!" Ta fa a sau uku sai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin gawar cikin fitar hayyaci. Mama Sa'adatu da Maman Nayla ta Kaduna suka ri o Nayla suna bata h kuri cikin tsananin tausayi. A lokacin karfe tara na safe ya buga, Kawu ya mi e ya ce, "Lokaci ya yi, mutane suna jira a auko ta, Omar tashi mu je!" Ya fa a yana ri o Omar. Omar ya mi e tsaye yana bin wanda suka shigo da makara da kallo. A akan idonsa aka saka Didi a makara aka fita da ita daga falon. "Didi!" Nayla ta fa a cikin jan numfashi kafin ta yi baya ta zube a kan carpet, mutanen falon aka yi kanta gaba a amma Nayla ko numfashi bata yi. A kan idon Omar ta zube amma sai ya rasa gane me hakan yake nufi, Kawu ya ja hannunsa suka fita. Sai da ya kare fuska da hannunsa saboda hasken da ya gani, ga mutane kowa shi yake kallo shi dai kallon su kawai yake yi. A nan aka yi sallah aka wuce zuwa ma abarta. Nayla kuwa asibiti aka koma da ita daman gudowa tayi babu wanda ya sani, aka jona mata ruwa da taimakon gaggawa dan numfashinta ya tsaya cak ga rashin jini da babu a jikinta dan ta zubar da jini sosai. A cikin gidan aka zauna ana kar ar gaisuwa, AbudlHamid ya yi namijin arin jurewa yana ta kar ar gaisuwa, Omar dai yana zaune da kayan jiya a jikinsa. Ya san dai in aka mi o masa hannu yana bada hannu a gaisa bayan nan babu abinda yake iya yi yana dai zaune kamar mara hankali. Har rana ta fito sosai baya iya cewa komai, a lokacin Baba Adamu ya taso ya kamo hannunsa bai musu ba ya mi e tsaye zuwa wajan da babu mutane sosai, ba jimawa sai ga Mama Zainab a wajan ya kalle ta ya ce, "Yaron nan yana cikin wani yanayi, yana bu atar ya ci abinci Zainab." Mama Zainab ta kalli Omar da jajayen idanunta ta ce, "Sannu Omar." Bai iya tanka mata a hankali ta ce, "Matarsa ma na asibiti a kwance, kasan yanayin da ake ciki" ta fa a murya na rawa sosai. Baba ya ce, "Dole ayi wani abun, shima ko a kai shi asibitin kawai." Omar gajiya ya yi da tsarguwa ya cire hannunsa daga na Baba yana takawa a hankali zuwa inda zai bi ya hau samansa ya hau saman bai sake kallon kowa ba. Da ya hau saman ma tunani ne yake neman tarwatsa masa zuciyarsa, ga zafin da yake ji a zuciyarsa da fatar jikinsa har tiriri yake ji yana tasowa yana mamaye masa zuciya. Jin zafin ya dame shi ya saka shi shiga ban aki ya kunna ruwan sanyi ya tsaya ruwan na sauka a jikinsa ba tare da ya cire kayan ba. Waje aya yake kallo a ban akin, duk inda ya kalla babu abinda yake gani sai fuskar Didi tana murmushi. Ko ya ji sautin muryar tana kiran sunansa bayan nan babu abinda yake iya ganewa. Kamar zautacce haka ya koma, ya fito ba tare da ya cire kayan ba ya zauna yana rawar sanyi saboda sanyin ya yi masa yawa amma baya so ya cire. Bai san lokacin da ya auka a haka ba ya dai ji ana buga ofar akin bai iya motsawa ba a lokacin aka bu e aka shigo. Baba Adamu ne da Mama Zainab suka shigo akin da sallama, ya kalle su bai ce komai ba kuma bai motsa ba. Baba Adamu ya ce, "Subahanallah, Omar me ya same ka haka?." Bai ce komai ba yana dai zaune sai ya dafe kai da hannayensa saboda ciwon da suke yi masa kamar zasu tsage. Mama Zainab kasa ri e kuka tayi ta fita tana kuka sosai, ba jimawa Baba ya fito yana yi mata fa a akan zata sake tayar masa da hankali in tana kuka a gabansa. A lokacin ya fito ya saka jallabiyya fara mai gajeren hannu suka sauka tare saboda nema sa da ake yi in an zo. Haka aka kwana uku Omar baya cikin hankalinsa, abun kullum sake gaba yake yi dan baya magana, in an yiwa Didi addu'a dai yana iya motsa bakinsa ya ce amin amma tun a asibiti ba a sake jin muryarsa ba. Zaman makoki ake yi mai capacity, kowa a danginsu Omar bada gudunmawa yake yi na abinci da abin sha. Mutane zuwa kawai suke yi wasu ba a san su ba kawai suna shigowa ne. Nayla har lokacin tana asibiti ta farfa o amma ta kasa nutsuwa, jininta ya hau ga kukan da yake yi kullum. Jidda da Salma ne a wajan ta in Mama bata nan, Musliha na wajan su suna ta rarrashi amma bata iya dainawa har sai an yi mata allurar bacci. A ranar kwana na ukun ne ta an samu nutsuwa, kukan ya ragu sai ciwon kai da yake damunta. In ta rufe ido ta tuna Didi ta mutu sai ta ji zuciyarta ta buga ta sake gigicewa. A ranar kwana na hu u suka dawo gida, tana shiga falon gabanta ya fa i ta tuna inda Didi ta zauna ranar da zata mutu sai kuka ya sake cin arfinta. Abiy da kansa ya yi mata nasiha yana bata ha uri amma ta kasa daina kukan jikinta ya zama wani iri ta koma kamar ba ita ba. Bayan ta zauna ta an nutsu Musliha tana hannunta Marmerh ta shigo da gudu ta fa a jikinta ta ce, "Mummy ina Ummi?." Nayla ta zubawa Marmerh ido hawaye suka sakko daga idanunta. Umma Saroot ta ce, "Nayla ki yi ha uri, wannan damuwar da kika saka a ranki ciwo zasu saka miki, wanda ya bar duniya ya mutu bazai dawo ba, ita ta dace tunda ta samu yabo da kyakykyawar shaida, na tabbatar mala'iku sun auki abinda mutane suke cewa da shi zasu yi amfani.