← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 205

Sashe 183

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Addu'a ya kamata ki dinga yi mata kin ji?." Ta ri e Marmerh a jikinta ta kalli Umma ta ce, "Umma bacci ta ce min fa zata yi, hannunta yana cikin wannan hannun nawa" ta fa a tana kallon hannunta. Umma Saroot ta ce, "na sani Nayla, amma ikon Allah ai ya fi gaban wasa. In lokacin mutum ya yi baya ara ko second aya a duniya yake mutuwa, lokacinta ya yi a lokacin da ta ce miki bacci zata yi." "Meyasa zata mutu yanzu? Meyasa?." "Haba Nayla me ki ke fa a haka? Kar hankali ya gushe ki yi sa o fa." Hawaye suka sake sakko mata, Marmerh tana jikinta har lokacin ta kasa sakinta. Hajja ta ce, "Hauwa ki tashi ki je ki duba Omar, an ce ya hau sama tun azu bai sakko ba." Umma Saroot ta ri e Marmerh, Nayla ta mi e a sanyaye ta hau saman memories in Didi na dawo mata tana kuka. Halin da ta tarar da Omar a ciki ya saka ta sake gigicewa, domin kuwa yana kwance shima kamar yadda Didi take. Ta arasa inda yake a gigice tana jijjiga shi da iya arfin da ya rage mata amma baya motsi kamar yadda Didi bata motsi. Ido ta wara tana girgiza kai kafin ta kwasa a guje ta tana ha a steps zata kifa ta sakko tana hakki ta ce, "Shima baya motsi, shima baya numfashi irin Didi, shima yana kwance, baya motsi." A firgice take maganar hakan ya saka hankalin mutanen wajan ya tashi sosai. Nayla ta sulale ta zauna a wajan tana sake maimaita abinda ta fa a, tana ganin su Umma sun hau saman da sauri ita dai ta kasa motsi. Tana gani su Baba Adamu da AbudlHamid suka hau saman, ba jimawa sai su Kawu da cousins in Omar an hau sama gaba aya. auko Omar aka yi cak aka fita dashi ta ofar da zata fitar da kai compound in gidan ba tare da an shiga ta falo ba aka wuce asibiti. P115 ar gaggawa aka yi masa, aka shiga ceto ransa domin yana cikin mayuwancin yanayi. Sun jima a kan Omar kafin a samu a daidaita komai likitan ya fito repection inda suke zaune ya ga dukkansu kallon sa suke yi alamun arin bayani. Dr ya ce, "Akwai abinda yake damunsa ne? Ina nufin abinda ya jefa shi a cikin wannan yana yin. AbdulHamid ya ce, " warai akwai, Yayarsa Allah ya yiwa rasuwa." "Allah sarki, Allah ya gafarta mata." Aka amsa da amin likitan ya ce, "gaskiya jininsa ya hau sosai, sannan akwai yunwa a tare dashi wacce ta taimaka wajan sakin jikinsa da galabaitar dashi. A yadda na fahimta akwai rashin bacci, shima ya taimaka wajan hawan da jininsa ya yi." Baba Adamu ya ce, "Yanzu ya jikin nasa?." "Numfashinsa ya dawo daidai a yanzu, an saka masa ruwan da zai daidaita blood pressure insa. Sannan an yi masa allurar bacci wacce zata saka shi bacci na dogon lokaci, mun yi isolating insa a special room wanda ba a hayaniya wajan saboda ana bu atar ya yi bacci walwarsa ta dawo daidai. Sannan an saka masa nasogastric tube, wacce za a dinga bashi abu mai ruwa ta cikinta yana zuwa har cikinsa, kamar tea ko kunu da sauransu. Yunwar da take damunsa ta wuce drip ya yi masa magani gaskiya. So za a samu mutum aya da zai dinga shiga yana bashi abincin amma ban da hayaniya, in bai samu baccin da ake so ba zai iya samu ta walwa." A tare kowa ya yi ajiyar zuciya likitan ya ce, "kar ku damu, da ya tashi daga baccin in sha Allah za a samu canji sosai." A tare suka ha a baki suka ce, "Allah ya sa." Tsakanin dangin Baba da dangin Maman su Omar har rige-rigen kula da Omar ake yi, kowa ya ce shi zai zauna saboda halin da Nayla take ciki itama bazata iya kula dashi ba. Da yar aka bar autan su Kawu a asibitin duk suka koma gida saboda masu zuwa gaisuwa. Nayla ma tana gida su Mama sun sakata a gaba tana cin dafaffiyar hanta wacce aka dafata da alaihayu, da yar take iya kaiwa bakinta ta tauna, da tunanin Didi ya fa o mata sai aga hawaye yana zuba daga idonta. Marmerh da take gefe tana bacci ta kalla ta shafa kanta tana kuka ta goge ido tana cigaba da ci a hankali. Salma ta dafata ta ce, "Nayla don Allah ki daina kuka, addu'a take bu ata yanzu." Nayla ta kalle ta ta ce, "Salma hannuna yana cikin nata, ashe ta mutu ban sani ba. Ta juyo ta ce min nima fa ina son Omar ba ke ka ai ke sonsa ba, sai ta yi murmushi ta yi dogon salati ta rufe ido. Ni gani nake kamar ba mutuwa tayi ba suka je suka binne ta." Jidda ta ce, "Haba Nayla, ki daina furta wannan maganar mana, Ana wasa da mutuwa ne? Lokacin ta ya yi wannan maganar itace ta arshe da zata yi miki. Don Allah ki kwantar da hankalinki, sai kin nutsu zaki iya kula da mijinki shima yana asibiti." Ta kalli Jidda da take maganar zata yi magana Mummynsu Salma ta ce, "Don Allah Nayla ki nutsu, rashin nutsuwar da baki da ita ne ya saka ki ke a nan da kina tare da mijinki. Yana can a kwance, in baki nutsu ba ta ya shi zai nutsu?." Hawaye ya zubowa Nayla ta ce, "To Mummy, in na tuna da Didi ne sai zuciyata ta karye." uri zaki yi, an san zaki ji zafi a zuciyarki amma daurewa ake yi, addu'a take da bu ata ba wannan koke-koken ba." Nayla ta goge ido ta kalli Marmerh da ta tashi daga bacci ta ce, "Mummy Ummi." Nayla ta ri eta ta kasa magana sai kuka. Jidda ce ta auke Marmerh ta ce, "Marmerh muje na baki cocholate?." Marmerh ta ce, "Ummi za ni." Jidda ta ce, "zan kai ki, amma ki fara sha ko?." Ta aga kai sai kuma ta ce, "da daddy." Murmushi Jidda tayi, hawaye na zubo mata itama ta fita da Marmerh kamar yadda Musliha take hannun Salma. yar aka samu Nayla ta sakko asa saboda masu zuwa gaisuwa, in Omar baya nan dole ita za a nema. Nayla dai kallon mutane take yi har lokacin itama bata dawo daidai ba shiyasa ba a tura ta asibitin ba. A haka aka akayi kwana bakwai da rasuwar Didi, gida ya watse har lokacin Omar yana asibiti bai tashi ba. Ranar kwana na takwas da yamma aka kai Nayla asibitin, Musliha da Marmerh suna wajan Umma Saroot dan ita a wajan Nayla take kwana. akin da Omar yake ta shiga ta ganshi a kwance yana sauke numfashi a hankali, shafa kansa tayi da gashi ya taru gashin a kwance, kallo aya zaka yi masa ka san ya rame sai haske da ya sake yi musamman fuskarsa da afarsa. Hawaye ta goge tana kallonsa ta zauna a gefensa tana kallo irjinta ma bugawa matu a. A asibitin ranar ta kwana ita da Umma, wannan dare ya tuna mata Didi, dan da ace tana da rai tare zasu kwana da ita suna kula dashi. Ta sha kuka son ranta ta share hawaye tana yiwa Didi addu'a a zuciyarta. Washe gari da safe Nayla tana gefe a zaune a gefensa,Umma Saroot na gefe ita Marmerh da Musliha suna bacci Omar ya bu e ido. A hankali ya juyo ya kalli Umma Saroot da take zaune suka ha a ido sai ta ce, "Omar ka farka? Sannu" ta fa a tana mi ewa zuwa inda yake. Nayla ta kalle shi suka ha a ido, yadda idanunsa suka koma sai da gabanta ya fa i ta ri e hannunsa ta ce, "Sannu." Ido ya lumshe a hankali, ya jima a haka kafin ya sake bu e idon ya kalli Nayla muryarsa dashe matu a ya ce, "Abinda ya faru mafarki ne ko gaskiya? Nayi mafarki wai Didi ta rasu, da gaske ne?." Sai kawai Nayla ta fashe da kuka, ta ora kanta a hannunsa hawayenta na sauka a hannunsa. Omar ya kafa mata ido yana kallo kafin ya kalli Umma Saroot da take tsaye tana goge hawaye ya ce, "Meyasa ku ke kuka? Ba mafarki na yi ba kenan? Ni na ri e Didi aka sakata a kabari da gaske?." Da sauri Umma ta fita daga akin tana kuka, sai da ta daidai kanta sannan ta kira likita kamar yadda ya ce in ya farka a sanar dashi. Kallon Nayla ya yi da take kuka ya ce, "Hajiya ki daina kuka, zaki sake tayar masa da hankali. Kwanciyar hankalinsa ake da bu ata yanzu." Nayla ta share hawaye likitan ya ce, "sannu." Bai iya motsawa ba likitan ya ce, "Akwai abinda yake damunka?." Omar ya nuna kansa ya ce, "kaina na ciwo sosai, irjina ya yi nauyi sosai." "Sannu, damuwa ce tayi maka yawa in ka sassautawa kanka zaka ji sau i, Zaka iya tashi zaune?." Omar ya girgiza kai alamun a'a saboda baya jin arfi ko ka an. Likitan ya ri e babban an yatsansa na afa yana matsawa a hankali ya ce, "kana ji ina matsa afarka?." Omar ya aga kai alamun yana ji, ya ri ayar afar ma ban ma ya ce yana ji. Hannunsa ya ri e ya matsa nan ma ya ce yana ji likitan ya ce, "Zaka iya tashi, gwada." Omar ya motsa da yar sai ya koma ya zauna ya ce, "kaina!." "Sannu, in ka zauna zaka ji da i." Da yar ya mi e ya zauna yana jan numfashi da yar. Bp insa ya auna ya ga jinin ya an sauka amma ba sosai ba, ya kalli Omar ya ce, "Kana da bu atar ka yi wanka sannan ka ci abinci, zaka ji da i sosai a jikinka." Omar ya lumshe ido bai ce komai ba likitan ya fita dan kawo magani. Umma Saroot ya kalla ya ce, "Ina Didi take? Ban ganta ba." Ya fa a dan shi manta maganar da aka yi a farkon tashinsa. Shiru tayi bata amsa ba ya kalli Nayla da take ta ajiyar zuciya ya ce, "Didi bata zo ba?." Nayla ta
Chapter 183 · 0% Book details