Sashe 37
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fa. Didi ta kalleta tana bu e ido ta ce, da gaske?. Nayla ta ce, Wallahi. Amma Bashir ne kawai ya sani shine ya ke kawo min sample in da nake yin video. Diid ta ce, wai daman ke ki ke saka takalman ki yi video ayi posting?. Nayla tayi dariya ta ce, Wallahi ni ce Didi, da yake ina da account in na su a hannuna da kaina nake posting Didi ta ce, ai kam ki dinga tofe afarki da lahaula, dan baki ga yadda ake yabon afarki ba, ki dinga shan maganin baki. Ina gani Didi, harda masu cewa su don Allah a basu number mai wannan afar. Didi ta yi dariya ta ce, ba su san matar Boss ba ce. Omar yana tsaye ya ji duk abinda suka ce, wayarsa da take aljihu ya auko ya shiga ig page in nasu yana scrolling yana ganin hotuna da video afarta dan kusan kaf posting in videos in ne. Tsurawa afar ido ya yi yana kallo, afarta ta tayi haske sosai haka faratanta, sannan gata madaidaiciya mara tudu da tsaho. an yatsun ta a jere babu alamun koda jijiya a r sai zallar kyau da haske. Sosai afarta ta ke haska takalman matu a, ko baka da niyar siya zaka tsaya ka kalla saboda kyaun da takalmin yake yiwa afarta. Wani irin abu yake ji mai kama da acin rai yana mamaye ilahirin jikinsa da zuciyarsa, haka kawai ya ji ya damu kansa, hannu yana rawa ya danna comments section in yana karantawa. _Kai ma sha Allah, wannna afa ba dai kyau ba. Ko wacce mai afar nan Ina matu ar sonta, saboda afar nan zan siyi taklamin nan wallahi._ abinda ya gani kenan a rubuce, ya sake yin scrolling yana ganin irin su babu adadi. Cike da bugawar zuciya ya rufe ido ya bu e yana ji kamar ya je ya kwashe ta da mari. Numfashi ya sauke ya tako ya araso falon ya kalli Nayla ya ce, ba na hana ki shiga lamarina in ba ni na saka ki ba? Ba na ce ki daina yi min shishshigi akan abinda ya shafe ni ba!?. Da murya mai amo yake magana cikin tsananin acin rai. Didi ta ce, Omar Lafiya? Me ya faru kuma?. Ya nuna Nayla da yatsa ya ce, duk ke kika jawo min, ke kika jawo yarinya arama kamar wannan ta raina ni har na ce ga abinda za ayi ta tsallake ta ta i yi. Didi ta ce, me ta yi ne Omar?. Na fa a mata babu ruwanta da shiga rayuwata, na fa a mata babu ruwanta da shiga abinda ya shafe ni meyasa take yi!?. Ya ru a Didi hakan ya saka ta ce, ka fa a min abinda tayi maka in mana. Ya haska mata fuskar wayarsa ya ce, ni na saka ta wannan aikin? Na saka ta na ce ta dinga yi min tallan kaya da jikinta!?. Ya juyo ga Nayla a fusace ya ce, Na saka ki!?. Nayla ta firgita sosai ta yi shiru bata ce komai ba. Didi ta ce, Haba Omar; kai fa mijinta ne tana yi dan taimakawa kasuwancin ka. Meye aibu dan ta yi maka talla?. asa ya yi da muryar sa amma a kausashe take ya ce, to na ce ina so ne? Ko na ce mata Ina bu atar ta aikata hakan?. Didi ta ce, Dan ta yi hakan ai ba wani abun ba ne ba Omar, taimako ne Tray in da Didi take shan kankana ya cillar a asa ya rabe gida biyu ya ce, To bana so! Bana so, na sake maimaita!. Kar a sake aikata abu ba tare da na sani ba, kar a sake shiga lamarina ba tare da na ce a shiga ba Ya juya ga Nayla ya ce, Kar ki sake aikata wannan kuskuren, ina ja miki kunne a karo na arshe kenan, ki tsaya a iya matsayinki! Ya fa a idanunsa a waje har ja idanun ya yi. Didi ta ce, to ka yi ha uri mana, amma dan an yi posting ai ba wani abun ba ne. A ganin ki kenan, amma a wajena wani abun ne, wani abu ne a wajena Didi. Na ce bana so a daina! Ya fa a hannunsa har rawa ya yake yi yana danna wayar yana kiram Bashir. Bashir yana auka ya ce, duk page in da ka san ka yi posting wannan video da ake auka ba tare da na sani ba a goge, a goge yanzu babu ata lokaci! Ya fa a yana sauke wayar a fusace tare da lumshe idanunsa cikin acin rai. Kai ya dafe yana yamutsa gashin kansa kafin ya shafa gashin fuskarsa yana furzar da iska mai zafi. Ya rasa abinda yake mu usar zuciyarsa har ya canja shi haka, zafi yake ji yana tasowa daga zuciyarsa yana ratsowa har fatar jikinsa. Didi karantar yanayinsa take yi sai ta yi murmushi, zata iya rantsuwa babu kaffara Omar kishin Nayla yake yi, kishi kuma ba an ba. A hankali ta ce, Omar dan dai ka nace ne, amma meye laifi dan ta yi video ko hoto ta ora? A ganina ai ba wani abun bane. Mata nawa ne suke yin hakan akwai abinda ya same su ne?. Kuma ta yi ne saboda a samu followers da masu siya kuma an samu. Kallon Didi yake yi kawai ya ma rasa abinda zai ce mata jin abinda take cewa. Wai ta yi ne dan a samu masu siya, haka yace mata hana da bu atar masu siya ne ta wannan hanyar?. Ido kawai ya zuba mata yana kallo kafin ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya, ya sake kallon Didi yana cize baki ya ce, ke ki ke zugata kenan ko? Ke ki ka saka take yin abinda ban sakata ba ko?. To na rantse da Allah na sake ganin makamanin hakan ke da ita baza ku kwana lafiya ba!. Zata iya kasuwanci da abinda mu ke yi ta siyar bai dame ni ba, amma wannan bana so!. In kuma aka sake sai ya girgiza kai alamun ku guji abinda zai faru ba tare da ya ce komai ba, ya kalli Nayla da tayi tsuru-tsuru ya ce, garga i na arshe! ya juya ya fita daga gidan gaba aya. Alhaji Omar kenan KRB3P018 Arewabook@nanahaleema11. Nayla tana tsaye tana hawaye, Didi ta araso kusa da ita ta rungume ta tana tapping bayanta alamun rarrashi. Nayla cikin kuka ta ce, Didi yanzu meye laifin a nan? Ni da zuciya aya na yi ba da wani abun ba. Amma naga ba yaso na dinga shiga lamarinsa, zan daina in sha Allah. Didi ta ce, ki bar kuka, ki yi ha uri. Nayla ta ago daga jikin Didi ta ce, yanzu ba dan kina nan ba da ban san ya zan yi ba, nayi shiru ya ce nayi masa banza, na yi kuka ya ce dukana ya yi da nake masa kuka. Kuma ni naga haka masu siyar da irin wannan kayan suke yi, sai na ce nima bara na yi saboda na taimaka ba dan wani abun ba. Didi ni aurena dashi bana aukarsa matsayin aure wallahi, Ina yi masa komai ne saboda yana matsayin aninki, zan iya yin komai dan ganin cigaban rayuwarsa. Didi shi na lura baya son haka, kawai baya sona shiyasa baya so na shiga lamarinsa. Didi ta yi murmushi ta goge mata hawaye ta zaunar da ita akan kujera ta ce, Ba haka bane ba Nayla. Tun farko na san ke kike yin wannan hotunan, Bashir ya fa a min da na tambaye shi, sai ya ce min kar na fa awa Boss kin ce bakya so ki sani. Ina sane na tayar da maganar har ki ka furta da kan ki, Ina so na ga reaction in Omar. Tun farko ni na bashi wannan shawarar tun kafin auren ku, sai yake cemin ina za a samu macen da za a dinga hoto da afarta? Sai na ce masa gani ba sai nayi ba. Nayla hararata ya yi ya ce bazan yi ba, kin san meyasa ya ce baza a yi ba?. Nayla ta girgiza kai alamun a a Didi ta ce, Saboda Yayarsa ce ni yana kishin hakan a kaina. Ko da Omar yana da anwa na tabbatar bazai bari ta aikata hakan ba, dan shi mutum ne da baya so a ra i abinda yake so. Nayla in muka fita dashi wani ya tanka ni har mu dawo ransa a ace yake, in na yi masa magana sai ya ce ban san me yake ji bane. Nayla ta ce, to laifi ne ni dan na yi kenan?. Didi ta ce, ni fa Yayarsa ce Nayla, ya nuna baya so nayi saboda yana kishina. Ke kuma matarsa ce, me yanayin Omar ya nuna miki a yanzu don Allah?. Nayla ta ce, ba yaso na shiga lamarinsa shine kawai. Didi tayi dariya tana mamakin autancin da yake damun Nayla har da ta kasa ganin kishi a idanun Omar ta ce, Nayla ba wannan ne a ran Omar ba, wallahi Omar kishinki ya ke yi, kishinki yake kishi mai tsanani ma kuwa!. Ki duba yadda ya fasa tray in nan ta fa a tana nuna mata yadda tray in ya tsage har gida biyar. Damm irjin Nayla ya buga ta kalli Didi ta ce, Didi Kishi fa ki ka ce?. Didi ta yi murmushi ta ce, azu maganar samarinki ake yi ya nuna baya son ji, yanzu hotunan afarki ake orawa ana talla da su ya hargitse har da fasa tray, Nayla in ba kishi ba meye?. Tsana ce mana Didi! Ta fa a kai tsaye dan ita bata yarda kishi ba ne ba. Didi ta yi dariya sosai tana girgiza kai ta ce, ashe kema irin sa ce, taurin kai gare ku. Yanzu baki yarda Omar kishinki yake yi ba?. Nayla ta ce, wallahi ko ka an ban ji hakan a zuciyata ba. Shikenan Nayla, zan tabbatar miki nan da lokaci ka an. Amma daman ora hotunan afarki ana talla dasu bai kamace ki ba, ke ai matar aure ce, ko ya wani yaga gani ya yabi afarki za a rubuta miki zunubi. Amma Didi da akace mace dukkanta al aura ce an ce