← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 205

Sashe 121

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jan numfashi cike da tsoro da tashin hankali, ya nuna mata kan gado ya ce, "wuce ki kwanta!." Jikinta rawa yake yi sosai, ta kasa motsawa daga inda take saboda tsoro da firgici. Cikin tsawa ya ce, "ki wuce ki bani waje!." A firgice ta motsa zata bar wajan tsantsin aman ya kwashe ta tayi baya zata fa i ya taro cikinta ta tsaya cak, ya sake tamke fuska ya nuna mata kan gado ya ce, "wuce ki kwanta!." Muryarta na rawa ta ce, "Sallah.....zan......yi...." Ya nuna mata ban aki ya ce, "shiga, in kuma na sake jin bakin ki sai na sa a miki." Da sauri ta wuce ban akin. Dogon tsaki ya ja ya fita ya auko abinda zai gyara inda tayi aman ya gyara wajan har lokacin bata fito ba. arasawa ban akin ya yi ya bu e, wata irin zabura tayi ta ha e jikinta waje aya tana kallonsa alamun tsoronsa take yi. are mata kallo yake yi da alama tunda ta shiga ba akin babu abinda ta yi. Fuskarta ya kalla suka ha a ido, ta ha iye wayu jikinta yana cigaba rawa. "Alwalar kenan?." Kamar wacce ya tunawa, ta yi firgigit ta arasa gaban sink ta bu e fanfo ta fara wanke hannunta. Jikinta rawa yake yi har ta gama ta fito, ta shinfi a sallaya ta saka doguwar riga da hijjab ta tayar da sallah. akin ya shiga ya yi wanka ya fito ya canja kaya, yana kallon ta tana sallah a firgice, kana ganin ta ka san babu nutsuwa a jikinta. Bashi da nutsuwar da zai iya yin sallah shiyasa bai gwada yi ba, ya auki waya ya sake kiran Bashir ya ce, "Ya jikin na sa?." Shiru ya yi kafin ya ce, "Okay" daga haka ya yanke wayar. Cillar da wayar yayi cikin acin rai, wai shi Tiger aka zo har gida ana yiwa ihu, shi ake cewa yaji tsoro, shi ake cewa ya ja da baya, shi ake agawa murya. Ya yi wafa a bayyane ya ce, "Bazai kwana da rai ba" ya fa a yana lumshe ido yana tuna baya. Nayla jin wannan kalmar sai gabanta ya fa i, ta fa i tana fa awa Allah kukan ta cikin sujjada hawaye. Har aka yi sallar asuba yana a haka, ko fita bai yi ba a gida suka yi sallah shi da ita. Tana idarwa jiki yana rawa ta ce, "ina kwana." Kallon ta ya yi y auke kai, ya manta rabon da su yi irin wannan gaisuwar. Da ya dawo daga masallaci take rungume shi sannan su gaisa, amma yau itace take ja baya kamar ta ga dodo. Bai nuna mata ba ya ce, "ki tashi ki kwanta" ya fa a ba tare da ya amsa ba. Jikin ta yana rawa ta mi e ko hijjab in bata cire ba ta kwanta, sabon tsoronsa take ji yana ratsa ilahirin jikinta. Numfashi ya ji tana ja alamun mai kuka, ya juya ya kalle ta ya ce, "ki daina kuka, ki yi bacci." Kamar wacce ya bawa umarni ta rufe ido ruf tare da toshe bakinta da hannunta. Yana zaune a wajan har baccin tsoro ya auke ta sannan ya tashi ya fita daga akin. Da safe ko da farka baya nan, haka ta tashi a gigice ta fita daga akin dan bata da nutsuwar gyarawa. Wanka tayi ta haye gado ta rufe jikinta saboda zazza in da take ji yana ratsa jikinta. Har azahar tana kwance, jin yunwa ta dame ta ya saka ta mi e ta fito da yar ta sha tea a lokacin aka fara ruwan sama mai arfi. Gidan shiru sai ita ka ai, kuka take ta yi in ta tuna abinda ya faru jiya sai taji kuka ya tawo mata wanda bata shirya ba. Ta rasa abinda yake yi mata da i, ko ganin Omar in ma bata taso, saboda tsoronsa da ya gama zagaye jininta. Waya ta auka tana kallon agogo ta ga arfe uku a lokacin kuma ruwan ya tsaya, hannun ta yana rawa ta shiga lambarsa ta kira shi bai auka ba, sai ta rubuta masa text na zata je gidan Didi. Tana gama tura masa ta saka hijjabi ta auki ku in mota dan baza ta iya jan mota ba, ta auki wayarta ta fita daga gidan. Tana fitowa daga gidan taji wani irin i ya mamaye ta, gaba aya gidan tsoro yake bata shiyasa take so ta fita ta bar shi. Napep ta tara ta hau sai bayan ta shiga take yi masa kwatancen uguwar da Didi take dan bata san sunanta ba. Tunda Nayla ta fito wani da yake can gefe a kan machine yake kallon ta, tana shiga napep ya kunna machine in ya aukar waya ya saka a kunne ya ce, "Matarsa ta fita a adaidai sahu" shiru ya yi alamun ana bashi amsa kana ya ce, "An gama, yarinya kwananki ya yana gama fa ar hakan ya saka wayar a aljihu yabi bayan napep KRB2P072 Nanahaleema. Nayla tafiya ake jikinta yana rawa sosai, sai da aka fara shiga cikin unguwar su Didi taji tsoro, dan unguwar shiru gashi an yi ruwa ko abin hawan babu sosai. A daidai gidan ya sauke ta, ta fita daga napep in hannu na rawa ta bashi dubu biyu ya kar a. Ganin wajan babu jama'a kuma a tsorace take sai ya fito mata da wu a ya ce, "Kee! kawo wayar hannunki." Nayla jiki ya cigaba da rawa, tsoronta ya ninka na baya, ba shiri ta bashi wayar ya shiga napep in da hanzari ya bar wajan. A guje ta kwasa zuwa ofar gidan Didi, buga gate in take yi a haukace cikin firgici da fitar hayyaci. Bata ji alamun motsin kowa ba ta cigaba da dukan gidan tana neman auki amma shiru. A lokacin wata ma ociyar Didi ta zo wucewa, ganin Nayla a tsaye tana buga gidan sai ta kalli ta ce, "Sannu baiwar Allah, ai Aisha bata nan ta fita tun safe." Nayla ta ja numfashi mai tsaho, bata iya bawa matar amsa ba saboda tashin hankali. Kalle-kalle ta fara yi tana kuka a tsorace, babu kowa a akan titi kuma babu inda ta sani a wajan balle ta je, kuma gashi ba mota a hannunta, ku in hannunta ma su kenan ta bawa mai napep. Jiri aukarta yake yi cikin tsoro da fargaba, bata ta a shiga cikin yanayin da take ciki ba tunda take a duniya. Machine ta gani daga gefenta an ajiiye, kai tsaye aka yo inda take ana zaro atuwar wu a mai kama da adda. Ba zato babu tsammani aka kaiwa wuyanta sara, cikin ki ima da tashin hankali ta kare da hannunta wu ar ta shiga cikin naman hannunta take jini ya fara zuba. Wata irin ara Nayla tayi saboda azabar da ta ratsa jikinta har walwarta. Ganin bai same ta a inda zai yi saurin kashe ta ba ya saka shi ya ce, "Au ban hallaka ki ba kenan" ya sake fa a yana aga wu a zai soka mata a ciki. Cak ya tsaya sakamakon ri e hannunsa da ya ji anyi, juyowa ya yi a firgice yana kallon wanda ya ri e shi. Ganin waye ya saka ya kai masa bugu da afa a ciki, Tk ya yi baya ya dafe cikinsa saboda dukan ya shige shi sosai. Ya sake yin kan Nayla da ta zube a wajan kamar mara rai jini ya ata hijjabin jikinta. Cikin azama Tk ya sake ri e shi suka fara kokawa, ya kaiwa Tk sara ya kauce, ya sake kai masa sara ya sake kaucewa. Jijiyar wuyansa Tk ya daka da arfi, take ya tafi luuu ya zube a asa a wajan. Tk ya auki waya tare da aukar hoton fuskarsa ya kai kallonsa ga Nayla da take yashe a wajan numfashin tana yana sama da asa. Da sauri ya ara kusa da Nayla ganin yadda jini yake tsiyaya daga hannunta ya ce, "Antyn mu, taso na kai ki asibiti." Nayla jin maganar take yi a sama, irjinta yana bugawa tsoro ya gama dabaibaiye mata zuciya. Jikinta rawa yake yi, ga azabar da hannunta yake mata ga tsoro da tashin hankali. Tk ganin bata cikin hankalin ta ya kalli hanyar, har lokacin babu kowa sannan ga wanda ya sumar a sheme a wajan. Ya du a ya ce, "Antyn mu ki taso mu tafi, kina zubar da jini sosai, kina bu atar ganin likita." "Wayyo Allah! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku, hannuna, jini ne yake zuba" ta fa a a firgice dan maganar Tk kamar farkar da ita tayi daga mafarki. Tk a gigice yake, so yake ya kaita asibiti saboda jinin da take zubarwa, in wani abun ya same ta ya san mai gidansa bazai aga masa afa ba. Ganin haka sai ya ce, "Antyn mu Didi bata nan, ki zo na kai ki asibiti, zaman ki a nan babu tsaro, komai zai iya faruwa dake a wajan nan. Ki nutsu mu tafi asibiti don Allah." Nayla kuka take yi cikin azabar ciwon da take ji, ta nuna masa hanya ta ce. "sun wace min wayata, wu a ya auko yana nuna min. Sun....sun....cire min hannu." Tk ya runtse ido, ya uka ya ri o hannunta duka biyun zuciyarsa na bugawa, ji yake kamar yaci amanar Tiger da ya ri e hannun matarsa, amma babu yadda zai yi, taimaka mata yake so ya yi, ri e ta in yafi barinta a wajan. Ya ce, "Antyn mu ki nutsu don Allah, ki zo mu tafi asibiti" ya fa a yana bu e mata motar. Kasa tashi tayi, sai da ya agota sannan ta iya tsayawa tana jiri, kamar mai ta in hankali haka ta shiga motar ya ja da sauri suka bar unguwar. Yana so ya bata waya tayi blocking bank account inta amma ya san bata cikin nutsuwarta. Kuka kawai take yi tana ri e hannunta da yake zubar da jini dan ba aramin yanka suka yi mata ba. Asibitin da Didi ta haihu ya kai ta, ganin yadda aka ji mata ciwo sai yace masu wacen waya ne suka ji mata ciwo. A take aka kar e ta aka yi mata allurar TT. Ana dressing wajan tana kuka mai
Chapter 121 · 0% Book details