Sashe 16
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan Hajja ta tura gate in ta shiga da sallama. Daga falon aka amsa mata ta shiga. Ihun da Salma tayi ne ya bata matu ar kunya sai ta rufe ido da hannayenta tana dariya. Salma ta ce, Amarya!. Nayla bata bu e fuska ba kuma bata amsa ba ta zauna akan kujera. Salma ta fara arin bu e mata fuska tana cewa, ka ga wata gulma, yau kunyar mu ki ke ji?. e fuska ta yi suka ha a ido da Hajja da take kallon ta tana murmushi. Hajja ta ce, Hauwa u ke ce tafe da daren nan?. Nayla ta ce, Hajja Ina yini. Lafiya lau Hauwa u, kin sha ruwa lafiya?. Lafiya lau Hajja. Ya ibada?. Alhamdu lillah. Ya mijin na ki?. Nayla sai ta sunkuyar da kai ba tare da ta bata amsa ba dan bata san ma ne zata ce ba. Bata ma kula da Didi a zaune ba sai ji tayi ta ce, baki amsa tambayar ba, aka ce ya bau en mijin na ki?. Kallon Didi tayi ta ce, kai Didi! Ai ban ganki ba, Ina yini. Didi tayi murmushi ta ce, lafiya lau Amarya, an sha ruwa lafiya?. Lafiya lau, Ashe kin zo?. Na zo yiwa Hajja sallama. Nima yanzu na shigo. Nayla tayi murmushi tana wasa da hannunta gaba aya jinta take yi kamar ba uwa a gidan Hajjan. Kallon Salma tayi ta ce, Su Abiy ma sun tafi, azu Yaya J yazo ya kawo min mota shima na san yanzu ya kusa sauka. Salma ta ce, ai bana kina Nigeria, ki bani sa on abinda ki ke so ta fa a cike da tsokana. Murmushi tayi kawai bata ce komai ba ta kalli Hajja ta ce, Hajja an gama ha a kayan ne?. Hajja ta yi murmushi ta ce, na gama Hauwa u. Wai daga yin azumi uku ne naga har kin rame Hauwa Nayla ta wara ido ta ce, Hajja yanzu har kin ga na rame? Hijjab ne fa a jikina. Hajja ta ce, Nayla ai ba jiya na san ki ba. Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta kalli Didi da take kallon ta tace, Didi gobe zan koma aiki. Didi ta ce, anyi miki transfer zuwa nan in kenan?. Eh, shine abinda Yaya J ya kawo min azu. Hakan yana da kyau, Allah ya taimaka ya bada nasara. Amma zaki sha wahala ga azumi ga aiki. Amin Didi. Akwai wahala kam sosai. Hajja ta ce, Ina mijin naki? Shi bazai zo ya gaishe ni ba ko? Lallai Ummaru, zamu gamu dashi. Murmushi kawai tayi bata furta komai ba dan bata san ne zata cewa Hajjan ba. Warmers ta gani a ajjiye a gaban Didi sai ta tashi ta ce, meye a ciki? In akwai abin da i na ci. ewa take yi ganin duk abincin bai mata ba sai ta an yi tsaki ta ce, bai yi min ba ma. Didi ta yi dariya ta ce, ke da ki ke amarya daman ta ya abincin tsohuwa zai burge ki?. Hajja ta ce, a mata dai. Nayla bata ce komai ba sai murmushi da ta yi kawai. Didi ce ta mi e tsaye ta ce, Ina zuwa ta fa a tana fita daga falon. Hajja ta kalli Nayla da kulawa ta ce, Hauwa u matso kusa dani. Nayla ta matsa kusa da Hajja ta ri e hannunta ta ce, Anya kina jin da in zaman auren nan? Ni ban ga canji ko ka an a tare dake ba, sai rama da naga kin yi har a fuskarki. Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, Babu komai Hajja, kawai tun ramar baya ce har yanzu ban koma yadda nake ba, amma babu komai. Hajja ta ce, kar ki yi min arya fa Nayla, ni idona ba haka yake gani ba. Nayla ta ce, Hajiya Hajja ba arya nayi miki ba gaskiya na fa a miki. Babu komai, kawai ki taya ni addu a Allah yasa Abiy ya daina fushi dani. Hajja ta ce, ba fushi yake yi dake ba in sha Allah, Kar ki damu da wannan. Salma ta ce, Yaushe rabon da ki yi azumi kuwa a Nigeria?. Nayla ta ce, nima bana ce ba Salma, amma an jima gaskiya. Hajja ta ce, wannnan zaman da zata yi ai yafi ta je saudia, ga aure ga ibadar azumi. Ladan da zata samu Allah ne ya sani. Nayla murmushi kawai tayi amma bata ce komai ba dan ita tasan babu wani ladan aure da zata samu. Hajja ce ta tashi ta shiga aki Nayla ta koma kusa da Salma ta ce, Salma don Allah kar ki manta dani a addu a, ko yaushe da kin fara addu a nazo zuciyarki. Ban san me yake damuna ba, amma ko me zai yi min bana jin haushinsa, har gobe ina son shi ta fa a murya na rawa tana ri e hannun Salma. Salma ta ora hannunta akan nata ta ce, kar ki yi kuka mana, ni ban san meyasa hawaye bayabyi miki wahala ba, in Hajja ta fito taga kina kika ai sai a samu matsala. Addu a zan yi miki in sha Allah Nayla, wallahi zan miki addu a kamar ke ki ka je da kan ki, ba dan kar nayi arya ba da nace zan yi miki addu ar da ko ke kika je baza ki yiwa kanki kamar ta ba. In sha Allah kafin ramadan in nan ya fita sai komai bani ya warware. Ta goge ido ta ce, Allah ya sa Salma. Salma ta ce, Amin. Wai babu wani cigaba a zaman nan na ku?. Hmm ko magana bata ha a ni dashi, yau ma da nace masa zan zo wajan Hajja gobe kuma zan je aiki cewa ya yi in ma duniyar zan bari ina ruwansa, sannan kar na sake shiga sabgarsa. Amma Omar in nan bashi da mutunci wallahi, dan ya samu ma mace kamar ki tana zaune dashi matsayin matarsa kuma tana sonsa shine zai dinga yi mana wula ancin da ya ga dama?. Bar ni dashi, addu ar mallaka zan miki, in sha Allah sai kin juya shi kamar waina Dariya Nayla tayi sosai harda dukan Salma ta ce, Allah ya shirya ki, wai addu ar mallaka. Wallahi kin bani dariya. A lokacin Hajja ta dawo sai Salma itama tayi dariya kawai suka tafa bata ce komai ba ganin Hajja. Didi kuwa lokacin da ta fita gidan su ta kalla ta ga ofa a bu e da alama Omar yana ciki. Bata shiga ba sai ta kira shi a waya yana auka ta ce, kana gida ne?. Katse kiran tayi alamun an bata amsa ta nufi gidan. A zaune ta same shi yana shan tea gefe ga slices bread guda biyu, sai kankana da apple da banana da suke ajjiye suma. Didi ta bishi da kallo shima ya kalle ta ya ce, Kwana biyu ana yawan ganin ki, kin sha ruwa lafiya?. Lafiya lau. Da yake na zo yiwa Hajja sallama ne gobe zasu tafi umra. Okay ya amsa a ta aice yana cigaba da shan tea insa hankali kwance. Didi ta ce, ba dai sai yanzu ka ke cin abinci ba?. Yanzu na ke ci. Baka ci a gidanka ba ne?. Ya kalle ta da mamaki jin ta kira gidansa ya ce, gidana kuma? Ina da gida ne?. Gidan da matarka take ciki fa?. Oh! gidan haya zaki ce ai ba gidana ba. To gidan haya! ta fa a a a fusace dan ya fara fusatata akan zancen gidan hayar nan. Omar ya sha tea a hankali kafin ya ce, bana ci, a gidan mu nake ci. Didi ta kalle shi cikin matu ar takaicin halinsa ta ce, meye amfanin matar ka?. ora afa kan aya yana kallonta ya ce, Amfaninta zama a gidan da aka kama hayar dan ita mana. Didi ta tausasa murya ta ce, Omar! Wai me yake damun ka don Allah? Abincin ma baka ci kenan? Wannan wacce irin a ka aukarwa kanka?. Wallahi na tabbatar Nayla baza ta i dafa abinci ta baka ba, kenan wula anci ka ke yi mata baka ci ko?. Ya kalli Didi ya ce, ni ban yiwa kowa wula alanci ba, to har wacece ita da zan tsaya na saurareta balle wula anci ya biyo baya? Wanda ya isa ai shi ake wula antawa. Abinci ne bazan ci ba daman dan ita aka kai ko? To sai ta dafa ta ci kayanta ai ba ni na kai mata ba. Didi ji take kamar ta zabga masa mari saboda takaici kawai yake ura mata a zuciyarta, ta danne fushinta tana girgiza kai ta ce, Omar na fa a maka abincin da aka kaita dashi daga gidan su al adar hausawa ce ba wani abun ba, gara ake kiranta, kuma yawancin hausawa masu ku i da sarauta duk haka suke yi, ba an kai maka gara dan ka gaza bane ka fahimta mana. Omar bai ce komai ba shayinsa yake sha hankali kwance dan maganar ba shigarsa take yi ba. Didi ta sake kallonsa ta ce, Omar ha in yarinyar nan zai bibiye ka fa. Ya ajjiye kofin shayin ya kalle ta ya ce, ni ban ce ha ina zai bibiya ta ba sai ita za a ce ha inta zai bibiye ni? Dole aka yi min babu yadda zan yi na kar a na amince har nake kwana gida aya da ita. Ban ta a kwana a gida aya da ko wacce mace ba in ba ke ba sai ita, iya rashin sakewar da bana samu shima shiga ha ina ne. Meyasa ko yaushe ki ke maimaita min ha inta a kaina ni bakya tuna nawa?. Ba fa sonta nake yi ba, dole aka yi min na zauna dan babu yadda zan yi. Gaba aya kin canja alaka, kamar itace jininki bani ba, ko yaushe cikin tausasa harshe ki ke a kanta. Ni ga banza bare ko tani bakya yi, ko tausayina bakya yi sai ita tunda ga ar diamond ya fa a yana ta e baki yana kallonta Didi ta ce, ko kana sonta ko baka sonta matar ka ce, kuma kula da ita dole ne a kan ka. Zancen na canja alaka a kanka ai dole na canja Omar, ita