← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 205

Sashe 61

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ce, "Wallahi babu, ko lokacin yarinyar nan Narma bai koma haka ba, ya cigaba da rayuwarsa normal kamar komai bai faru ba, amma ita kaga harda ciwo. Shine nake tunanin a tsakanin Narma Da Nayla in wa yake so?." "Wacce tunaninki ya baki." "To abun ne da aure kai, na farko ka ga Narma itace wacce ya furta min yana sonta, amma ko kusa bai shiga irin wannan damuwar ba. Ita kuma Nayla itace ya ce baya so amma ya shiga damuwa mai tarin yawa har ta haifar masa da rauni da ciwo. Kamata ya yi ace akan Narma ya shiga damuwa tunda ita yake so ba wai Nayla ba." Didi ta yi shiru ta sake cewa, "Kenan dai Nayla yake so da gaske ba Narma ba, amma meyasa a baya ya ce yana son Narma?." Ya ce, "Wata ila wani abun ne daban ba soyayya ba." Didi ta ce, "Bayan ni a duniya Narma itace mace ta farko da Omar ya samu kusanci da ita, magana da ita a waya da komai ma a duniya. Amma meyasa ko lokacin da ya ce yana sonta ko waya tayi masa sai ya ga dama yake auka? ko da suka rabu ban ga alamun ya damu ba, sai ma mayar da hankalinsa da ya yi akan sana'arsa. Amma ita kuma Nayla...." Sai kuma tayi shiru bata arasa ba. AbdulHamid ya ce, "ki bar wannan lissafin, Omar yana sonta kawai ki yarda, ita waccan labarinta ya wuce ta shigo rayuwarsa ne dan ta zama silar canja shi, amma asalin wacce yake auna wannan ce. Labarin zuciya ai a tambayi fuska, kina kallonsa kin san tsananin kewarta da son da yake mata ne ya mayar dashi haka, har rama yayi ga ciwo da yake fama dashi. ina shiga falon muna ha a ido dashi na san Omar ya fa i a asa warwar wallahi" ya fa a yana murmushi. Didi ta yi murmushin farin ciki ta ce, "Naji da in wannan abun abun wallahi, Omar na son Nayla. Na rasa inda zan saka kaina saboda farin ciki." Abdulhamid ya yi murmushi yace, "ke dai kawai ki tabbatar da ya je gidan su." n sha Allah" ta fa a cikin zumu i tana murmushi. Yadda ya ke zaune zai tabbatar maka da ransa a matu ace yake, ya zubawa waje aya ido yana kallo kafin ya daki table in gabansa ya ce, "Wallahi sai Narma ta dawo wajena, babu wanda ya isa ya saka na sake ta wallahi." Abokinsa da yake gefensa ya ce, "calm down maza, haba wannan ba ajinka ba ne." A fusace Ashraf ya ce, "har ni Dad inta yake cewa wai in ban sake ta ba zasu kai ni court, ka ji rainin hankali. Ai zama da Narma yanzu na fara shi wallahi, ban gaji da zama da ita ba, a bari duk lokacin da na gaji da morarta sai na saketa. Amma yanzu ban kammala ba tukunna." Dariya sosai abokin nasa ya yi ya ce, "To wai kai ka san baka son Narma meye na damuwa kuma haka?." "Saboda ban gama abinda na aure ta dan shi ba. Yarinyar nan ta wahalar dani, babu ta hanyar da ban biyo mata ta amince dani ba ta i. Ban ta a jin sonta a zuciyata ba, haka ban tana jin ina qaunarta ba. Da fari dai na auka soyayya ce, amma daga baya na tabbatar da sha'awarta kawai nake yi. Har gobe ina da bu atarta wallahi, sai yanzu ma tabbatar da Ikky itace wacce nake so ba Narma ba." Sharif ya murmusa ya ce, "To na ga ai ka samu abinda ka ke so har na watanni da yawa, har yanzu baka kashe ishin da kake ji a kanta ba?." "Sharif na kashe, sam bata wani burge ni sai in amfanin ta ya tashi, amma ni ka ai a san abinda yake jikinta. Ni ne mutum na farko da tayi tarayya dashi, ina da tabbacin har gobe babu wani ni sai ni in kawai. Ban gama da ita ba har yanzu, ban gama da mallakarta ba har yanzu, babu wanda ya isa ya aureta sai na gama abinda nake so." Sharif ya ce, "to ai matarka ce har yanzu." Ashraf ya ce, "iyayenta sune suke so su raba mu kuma wallahi ba su isa ba." Sharif ya ce, "Mtsw! Ni fa tun daga kan ka da Narma shikenan mata masu shiga half niked in nan basa burge ni, da zarar na ji sun burge ni zan saka a raina ba soyayya bace jikinsu ne kawai ya burge ni. Ka duba Ikky da ka ke magana yanzu, yarinya mai hankali ko yaushe cikin shiga mai mutunci da rufe jikinta take, amma ka rufe ido ka ce kai sai Narma saboda surarta da ka ke gani a bayyane. Yanzu gashi ka tabbatar itace wacce ka ke so, Narma kuma jikinta kawai ka ke so kuma ka samu." Ashraf ya ce, "Kai ka san sau nawa Narma ta karya min alwala? Ka san sau nawa Narma ta saka ni wanka ban shirya ba?. Haka zata saka kaya jiki a bayyane ta zo tayi hugging ina, don Allah wanne yanayi ka ke tunanin zan shiga?" Ya arasa fa a yana dariya. Sharif ya yi dariya sosai ya ce, "i'm sorry, she's your wife dole zaka ji kishi, but yarinyar nan she's too sexy." Ashraf ya ce, " Sorry for what? Do you think i have been jealous of what you've said about her? Mtsw shirme. Wallahi sam bana kishin Narma, ban jin wani abu a zuciyata a kanta in dai ba sha'awa ba. Yadda ka yi maganar Ikky yanzu na fi jin haushi a kanta." "Ita Ikky kana sonta ne ba surarta ka ke so ba, ita kuma Narma ba ita kake so ba jikinta ka ke so. Na tabbatar iri ka ma su son jikin Narma suna nan da matu ar yawa saboda Narma she's too hot. Wacce ka ke so ita zaka yi kishi ba wacce ka ke sha'awa ba daman ai" Sharif ya fa a yana kallon sa. Ashraf ya ce, "ni yanzu zan sake komawa Abuja, dole a dawo min da matata, in na ara ko da wata biyu ne tare da ita sai mu rabu na dawo wajan Ikram ina." "Ka san Sen bazai baka wanna damar ba." "Nima kuma bazan sake ta ba wallahi, sai dai ayi bala'i da masifa." "Kar ka yi haka Ashraf, da mahaifinka da mahaifinta abokai ne matu a. Kuma mahaifinka gov ne, kar ka yi wani abun da zaka ata masa harkokinsa. Ko yanzu ka rabu da Narma ai ka ci riba." Ashraf ya ce, "Yadda take ta ama da bata sona so nake na nuna mata ikona a kanta, wallahi so nake sai tayi shekara biyu sannan na saketa." Ya yi dariya ya ce, "Wannan ai mugunta ce, tunda ka samu abinda ka ke so ba sai ka share ba kawai." Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "za dai mu ga abinda ya kamata ayi" ya fa a yana aukar wayarsa ya cigaba da dannawa. Kamar yadda AbdulHamid ya bawa Omar shawara ya yi nazari ya tabbatar da Nayla ce abinda ya rasa a lokacin da ya fara jin wannan yanayi, kenan dai ita yake so meye?. Shi dai ya san ba haka ake jin so ba tunda ya ta a son Narma a baya, amma ba haka ya ji a kanta ba gaba aya yanayin bai kai haka ba. To in har abinda ya ji akan Narma shine so meyasa bai shiga yanayin da ya shiga a yanzu ba? Sannan ita Nayla me yake mata kenan? inta yake yi ko kuma wani abun ne daban?. Babu mai bashi amsa sai kawai ya share maganar ya danne zuciyarsa yana arin cigaba da harkokinsa amma ya gaza hakan. Bayan kwana biyu da zuwan Didi da daddare suka sake zuwa, yana gidan shi ka ai a zaune amma yanzu aikin yanka fatar takalmi yake yi. Tunda suka gaisa da su Didi yana yanka takalmin sai ya ma rasa ta yadda zai yi kawai ya ajjiye. AbdulHamid ya ce, "Ya jikin?." Omar ya ce, "na samu sau i." AbdulHamid ya ce, "Ka samo abinda ka rasa in kuwa?." Omar ya sauke numfashi ya ce, "Ni babu abinda na rasa balle na ce shi nake so, kawai ina jin mutuwa zan yi shiyasa nake jin wannan yanayin. An ce daman in zaka mutu kana ji a jikinka, wata ila ita in nake ji" ya fa a cikin gaskiyarsa. AbdulHamid ya ce, "A'a Omaar, ka dai sake tunani, akwai wani abun bayan wannan." Omar ya ce, "to meye? Na rasa gane me nake ji in." Didi ta kalle shi a nutse ta ce, "Meyasa ka ke zaune a gidan nan? Na auka kana gidanmu ne ai." Omar ya ce, "kawai ina so na zauna a nan ne." "Kana kewar matar gidan kenan?." Kallonta yake yi ko kiftawa baya yi kafin ya janye ido ya ce, "amma meyasa ki ka ce haka?." Didi ta ce, "Wanda ake kewa shi ake zama a inda yake saboda a dinga tunawa ana ganin kamar yana tare da kai. In kana kewar mutum kana kallon hotosa in baka dashi har inda yake zama kana gani, kana zuwa ka zauna inda mutum yake zama dan ya rage maka abinda ka ke ji a zuciyarka. Shiyasa nake tunanin ko kewarta ka ke yi." Omar ya aga kai sama ya sauke, ya kalle ta sai ya sauke kai asa ya furzar da iska ya ce, "indai har haka ake jin kewar wani tabbas ina kewarta, in ba a akin da take kwana na kwanta ba bana jin da i ko ka an. Ina kewarta Didi, ina kewarta sosai!" Ya fa a yana girgiza kai alamun tabbatarwa. Didi ta yi murmushi mai nuni da zallan farin cikin da ya mamaye mata zuciya, ta kalli mijinta shima ita yake kallo. Ta sake kallon ta ce, "in dai har kana kewarta kenan kana sonta?." Kallon Didi ya sake ya yi yana juya wayar idanunsa akan fuskarta kamar mai neman wani abun a kan fuskar tata. Ganin ya zuba mata yana are mata kallo sai Didi ta ce, "Eh Omar, sai kana son mutum ka ke jin kewarsa irin
Chapter 61 · 0% Book details