← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 205

Sashe 169

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yanayi da take ciki da rarrashi ya kamata ayi mata magana ba da yadda Omar ya yi ba. Narma ta tsayar da kuka cak ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa a guje, cikin tsananin rauni da sanyi ta ce, "Da gaske baka soni ba? Da gaske baka sona?." "To wacece ke da zan miki arya har ki ke so ki tabbatar? Amsa min wacece?." Narma ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai, ta ago a hankali taga ita dai yake kallo alamun ta bashi amsa sai ta ce, "matsayin wacce ka fara so a rayuwarka." Dogon tsaki ya ja ya kawar da kai yana girgizawa, haushi yake ji wata banzar bazawara tana cewa wai ita ya fara so, ya sake juyowa ya ce, "Ni Omar bana sonki, ban so ki ba, kuma bazan so ki ba. Kin shiga rayuwata kuma kin fita, shigarki rayuwata ya jawo canji a cikin ta ina gode miki a kan hakan. Wata ila da ban san mahaifinki ba da haka bai faru ba, wata ila da baki zo Kano an ha a ni dake ba da haka bai faru ba, wata ila da baki ce kina sona ba da hakan bai faru ba, wata ila da ban amince har na je gidanku ba da hakan bai faru ba. Ke! Kina jina...?" Ya fa a yana ora afa kan aya ya ce, "A katse wannan maganar a wajan nan, bani da ra'ayin aurenki kawai ki ha ura ki yale ni, bana son yawan maimaita magana guda aya, tun muna shaida juna a ha ura kafin a tunzurani." Narma hawaye ya sakko mata, cikin rauni da sanyin murya ta ce, "Ni na kasa tabbatarwa, da gaske baka sona?." Wani irin kallo ya yi mata alamun ta ishe shi ya zuba mata ido kawai yana kallo. Didi ta fahimci wannan kallon, yanzu zai birkice ya fara masifa ya firgita kowa. Didi zata yi magana ya ce, "Ke! ni zan zauna ina yi miki arya? Wacece ke da zan miki arya?. Ina fa a miki magana kina sake dawo dani baya, dan ma kin samu lokacina da maganar!?" Ya fa a cikin fa a sosai yana kallon ta. Didi ta ce, "Don Allah ka yi mata a hankali......." "Bazan yi a hankalin ba, yarinya ce ita da za a tsaya ana yi mata dabara ko magana cikin magana?. Sak nake magana ke kin sani, bazan aureta ba, ta kuma daina takura min, ta je tayi rayuwata ta nayi tawa. Kar ta sake zuwa inda nake!. In na sake ganin fuskarta a kusa dani ban san abinda zan aikata mata ba" Ya fa a yana zaro idanu waje yana kallon Didi, sai kuma ya yi tsaki ya mi e ya bar falon Didi ta kalli Narma da take jikinta ta ri e hannunta cikin rarrashi ta ce, "Narma ba komai ka ke so ka ke samu ba a rayuwarka ba, wani abun zaka so shi matu ar so amma in ba rabon ka bane dole ka yi ha uri dashi. Wani abun zaka i shi matu i amma kuma sai ka mallake shi ba tare da ka yi tunani ba. Shiyasa Allah ya ce abinda ka ke tsananin so wani lokacin ba shine alkhairi a gareka ba, abinda ka ke tsananin i kuma shine alkhairi a rayuwarka. Allah shine ya san abinda ba mu sani ba Narma. To ki auka Omar ba alkhairi bane a cikin rayuwarki shiyasa baki mallake shi tun farko ba, kuma tun farko da Omar mijinki ne da sai kin aure shi, amma ba mijinki bane shiyasa baki aure shi ba har ki ka auri wani ki ka fito daga gidansa. Baza ki ta a mallakar abinda ba na ki ba, baza ki auri mijin da ba naki ba. Abinda ya kamata ki yi addu'a, ki tsaya akan addu'a ki manta da komai sai komai ya wuce." "Kamar yadda ya fa a miki kin shiga rayuwarsa dan ki jasa zuwa gidanku ya zama silar canjawarsa haka ne, amfaninki a rayuwarsa kenan, haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canja. Baki kasance matarsa a cikin addarar ku ba, shiyasa Allah bai yi ma kin aure shi ba. Tunda har Omar ya ce baya so wallahi baya so in ne, Omar baya magana biyu, haka zakila baya fa arya ya oye gaskiya dan wani ya ji da i. Shiyasa kalamansa suka yi miki zafi dan shi bai iya oye- oye ba. A lokacin da yake tunanin yana sonki ba so bane, ya samu kusanci dake ne a karo na farko a rayuwarsa. Bayan ni babu macen da wani abu ya ta a ha a su sai ke, wannan abinda yake ji a ransa shine ya auka soyayya ce. Amma yanzu da ya mallaki wacce yake tsananin so ya banbance tsakanin so da kusancin. Ki kwantar da hankalinki, ki yi ha uri, ki fuskanci rayuwarki Narma." Narma kuka take a jikin Didi a hankali. Didi ta ce, "ina fa a miki gaskiya ne a matsayina na yayarki, gwara ki san abinda zaki yi ki daina ata lokacinki, sannan kuma daina tunanin Omar. In ki ka kuma zuwa inda yake gamuwar ku baza tayi kyau ba Narma. Zai yi miki abinda zaki ji ina ma baki san fuskarsa ba, duk yadda ki ke tunaninsa wallahi ya wuce wajan, gwara ki kama kanki ki cigaba da addu'a." Narma ta yi ajiyar zuciya tana sauke numfashi. Didi ta ce, "Sannan Narma ki yi hankali ki daina shigar da take nuna jikinki. Shigar banza ba wayewa ba ce a ganina jahilce ne, nuna surar da Allah ya yi miki ba komai bane face tsantsar rashin sanin ciwon kai. Duk yadda zaki kasance wajan fidda saraici ai baki kai tunkiya ba, ita tunkiya yadda aka haife ta haka take yawo, kin ga kenan duk abinda zaka yi akwai wanda ya fi ka, kafin ka yi aya an yi dubu. In kina nuna tsaraicinki baza ki samu wanda zai so ki tsakani da Allah ba, zasu so ki ne saboda abinda yake gani a zahiri a tare dake, da zarar ya aureki ya mallaka shikenan sai komai ya fita daga ransa, daman ba sonki yake yi ba sha'awa ce, ita kuma sha'awa tana gushewa ne da zarar gangar jiki ta samu abinda take maradi. Ba wai sai an neme ki a waje ne yake nuna illar shigar banza ba, ba sai anyi yun urin yi miki fya e ko abinda ya yi kama da haka shine yake nuna illar fidda tsaraici ba, wani lokacin sai kin yi aure zaki fahimci illarta, domin auren sha'awa maza suke yi da masu irin wannan abi'ar ba na soyayya ba." "Shiyasa nake baki shawara akan ki daina, tun kafin na san ki ni masoyiyarki ce, ina bibiyarki sosai saboda kina burge ni. Amma a ko yaushe ina cewa da Narma ta san illar nuna surarta a duniya da bata yi ba, a lokacin bani da matsayin da zan fa a miki gaskiya dan baki sanni ba, amma a yanzu na fa a miki na sauke nauyin da ya kamata ace na sauke. Surar da Allah ya yi miki ya yi miki ita ne dan ki yiwa mijinki kwalliya ba ki bayyanata ga duniya, in mijinki ya kalle ki ya yi farin ciki lada za a rubuta miki, wanda zaki je har abarinki ki tarar dashi. In akasin mijinki ya kalli surarki ya yi farin ciki zunubi za a rubuta miki, wanda zaki je abarinki ki tarar dashi." Didi ta kuma cewa, "sannan ki daina wula anta mutane shima ba abu ne mai kyau ba, Bazan ce kin yiwa Omar ba, amma wanda ya yiwa Omar saboda yana ganin rayuwarsa ta baya a yanzu ya ga yadda Allah ya mayar dashi, baka sanin abinda zai faru a rayuwar wani tunda ba kai ka tsara masa ba." Didi ta yi ajiyar zuciya ganin Narma ta nutsu tana saurarenta, jikinta yayi sanyi alamun maganarta tana ratsa zuciyarta. Didi ta ce, "Ki je gida Narma, ki zauna ki tsara rayuwarki yadda ya kamata, amma ki manta da Omar. Ki dage da addu'a, na tabbatar da ace kina addu'a abin bazai yi muni haka ba. Ina baki shawarar yin addu'a Narma." Narma ta kalli Didi ta girgiza kai tana goge idanunta ta ce, "Tabbas ina sakaci da addu'a Didi, ban ta a ro on Allah akan ya kawo min sau i a soyayyar Faruk ba." "Ashsha! Kin ji matsalar, ta inda aka samu kuskure kenan Narma. Tun farko da kin mi awa Allah kukan ki da yanzu kin manta da Omar, da yanzu kin cigaba da rayuwarki cikin farin ciki da annushuwa, da yanzu rayuwarki tayi gaba fiye sa tunanin ki. Indai kana ro on Allah kana fa a masa abinda ya fika sani a kai zai shiga lamarin ya kuma sassauta maka. Shiyasa hausawa suka ce in so cuta ne ha uri magani ne. Ki ri e addu'a, a akan Omar ka ai ba, akan komai na rayuwa ki dinga addu'a a kai." Narma ta girgiza kai ta ce, "Na gode Didi. Amma na tabbatar babu lallai na rayu a duniyar nan in babu shi." "Kul, kar ki sake fa ar haka. Babu wata halitta da in babu shi baza ka rayu ba, in har zaka rayu babu iyayenka a duniya babu wanda zaka ce dan babu shi baza ka yi rayuwa ba. Zaki manta da Omar in kin so hakan. Ki ri e addu'a kiga in komai bai canja ba, ina nan zaki zo ki bani labari." Narma tayi murmushin takaici, dan ji take abinda Didi take fa a ba yuwa zai yi ba. Ta mi e sai ta tafi zata fa i Safna tayi sauri ta tarota ta ce, "Yi a hankali." Narma ta kalli Nayla da bata ce komai ba amma kallonsu take yi, ta yi murmushi ta ce, "Ki yi ha uri Nayla, Allah ya raya Musliha, na gode." Daga haka Safna ta ri e ta suka fita daga falon. Didi ta kalli Nayla da fuskar take a aure matu a ta ce, "Ki yi ha uri Nayla, na san dole ki yi kishi, amma ki auka komai ya wuce." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta kalli Didi ta ce, "Babu komai Didi. Umma Saroot ta
Chapter 169 · 0% Book details