← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 205

Sashe 18

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yaketa kar i number su sannan ta nufo gida a matu ar gajiye ga azumi. Tana zuwa ofar gidan ta hango Omar shida Bashir da kuma Tk suna tsaye da alama magana suke yi. Motar ta faka a wajan ta fito daga motar tana ji kamar zata fika asa saboda gajiya da nauyin da kanta ya yi mata. Bashir ya ce, "Antyn mu barka da zuwa." A gajiye ta ce, "yauwa Bashir, na gode." Tk ma ya yi mata sannu da zuwa ta amsa ta bu ofar ta shiga gidan ta bu e gate in ta cikin gidan ta shiga da motar. Bashir ya ce, "Antyn mu ki huta, bara na shigo miki da motar." Nayla ta bashi key inta ce, "ai kam na gode sosai." Daga haka ta rufe ofar dan ta gaji sosai. Shigar mata da motar ya yi ya tarar da ita a tsaye daga can gefe ya bata key in tayi godiya ta araso ta bu e gaban motar ta auki jakarta da wayarta da laptop ta kalle shi yana niyar fita ta ce, "Bashir yaushe ku ke available gidan tv zasu zo aukar video na wajan na ku, na gama magana dasu gaba aya." Bashir ya ce, "Ai ko yaushe ma muna nan, amma ki ce musu gobe su zo." "Ka tabbatar gobe kuna nan?." "Na tabbata Antyn mu." "Shikenan zasu zo gobe in sha Allah" ta fa a tana shiga ciki shi kuma ya fita. Nayla wanka tayi ta canja kaya ta zauna tana sauke numfashi saboda ta gaji sosai. Kanta har sarawa yake yi saboda ciwon da yake yi mata. da yar ta iya samu ta mi e ta dafa tea ta ji tana son cin bread amma kuma babu, gashi bata da an aike balle tayi aike a siyo. Tsaki tayi a bayyane ta ce, "ko meyesa ban taho dashi ba yanzu oho min." ura tayi ta soya doya da wai ta dawo falo ta zauna lokacin shan ruwa ya kusa. Da yar ta iya addu'ar gab da shan ruwa saboda ciwon kai, ana shan ruwan ta sha ruwa ta yi sallah ta zauna tana shan tea a hankali duk da kanta da yake ciwo. Motsi ta ji bata motsa ba dan ta san shine ka ai yake shigowa ba tare da an buga gate ba, ta tabbatar da key in gidan ya cire yake amfani dashi wajan fita da dawowa. Daman ta san ba shigowa inda take yake yi ba hakan ya saka bata motsa ba tana zaune tana shan tea in kamar an yi mata dole saboda ciwon da kan yake mata. Kamar tsayuwa taji a bayan ta hakan ya saka ta juya ta ganshi a tsaye amma kuma waya yake dubawa ba ita yake kallo ba. Fuskarsa take kallo ta ga yayi mata kyau musamman idanunsa da suke kallon waya hasken wayar ya haske idanunsa sai ya bada haske na musamman. auke kai tayi zuciyarta na bata umarnin yi masa barka da shan ruwan, wani angare na zuciyarta na hana ta saboda abinda ya ce mata ta san kuma bazai amsa ba. Kallon ta ya yi kafin ya yi magana ta ce, "An sha ruwa lafiya?." Kamar ba zai amsa ba sai ya ce, "lafiya. Ehemm akwai wanda ki ke so?." Da mamaki ta kalle shi ta kasa bashi amsa saboda mamakin tambayarsa. Kallonta yake yi yana ganin mamaki a kwance a saman fuskarta ya wara idanunsa a kan fuskarta ya ce, "kin ji abinda nace ko?." Saurin auke kai tayi Allah ya sani in ya bu e ido ba aramin tsoro yake bata ba. Nayla ta girgiza kai ta ce, "babu komai." "In akwai zaki iya sanar da ni." "Yanzu dai babu." Ya aga kafa a alamun ban damu ba yana niyar fita. Ta kalli abincin da yake gabanta ta ce, "Bismillah ga abinci." Kallon abinda yake gabanta ya yi ya ta e baki ya girgiza kai ya fita daga gidan. Nayla ta dafe irji ta ce, "wannan mutum kamar wahainiya ko yaushe canjawa yake yi, wai akwai abinda nake so ka ji fa." Sai kuma ta yi murmushi a bayyane ta ce, "Ko babu komai ya nuna min ya san ni matarsa ce, hakan ya yi min." Da wannan murmushin ta gama ci ta sha magani aka kiran sallah ta tashi ta tayar da sallah. Tun daga ranar magana bata sake ha a su ba dan ba bama ganinsa take yi ba, in ta fita tun safe sai yamma shi kuma baya dawowa sai dare wata ila sai tayi bacci. Kamar yadda suka tsara da Bashir an zo an yiwa company su video ta biya ku in tayi komai a dan a fara haskawa a arewa24. Takalman da aka kai Kaduna gaba aya sun are har an sake kai wasu saboda yadda ake rubibin su sosai. Ita kanta wanda ta saka afar ta a wajan aiki mutane da yawa sun siya mata da maza, har na yara an siya saboda sallah. Video afarta kuwa da take yiwa ko wanne sample Bashir ne yake kawo mata sample tana yi tana tana posting dan tayo log in a dukkan account in su. Videon yana aukar hankalin mutane sosai, ko baza ka siyi takalmin ba in ka ganshi a afarta da yadda take aukar video sai ya burge ka saboda kyaun da yake yi mata. Sun ja hankain masu siya sosai da wannan advert in da take yi, komai yana tafiya daidai yadda Nayla take so. Cikin aramin lokaci suka sake wuce matsayin da suke kai saboda bu in da Allah ya kawo musu ta dalilin Nayla. Bashir ne kawai ya san me yake faruwa sai su Tk dan tayi musu magana akan don Allah kar su fa a masa. Omar kuma da yake ba kallo yake yi bai ma san ana yin tallah a tv ba, kwana biyu dai ya san yana samun customers sosai daga inda bai yi zato ba amma bai kawo komai a zuciyarsa ba. Manyan mutane daga gari gari suna siyan takalman ana kai musu inda suke. Cikin lokaci ka an takalmin ya yi suna a social media da kuma tallata shi da ake yi kullum a arewa24 daga arfe shida na yamma zuwa shida na safe. Watan azumi ya raba har an kusa shiga goman arshe, Nayla da Omar basu cika ha uwa ba sai dai taji motsin sa amma magana ko ganin sa bata yi. Da yake ta saka addu'a a gaba tana kuma zuwa aiki hakan bai dame ta ba, in ta dawo suna waya da su Salma yana rage mata abinda take ji sosai. Ranar da aka shiga goman arshe aka fara sallar tahajjud kamar yadda ta saba ko wanne watan azumi arfe uku ma dare ta ke tashi ta fara sallah har sai an yi asuba. Bayan ta yi alwala ta shinfi a sallaya sai ta fiton dan ta auki ruwa. Kallon ofar akinsa tayi tana nan a kulle kamar ko yaushe, bata da tabbacin yana ciki ko baya ciki tunda ba jin motsinsa ake yi ba. Zuciyarta ke bata umarnin ta gwada wasa masa ofa saboda tunasar dashi lokacin sallar tahajjud. A bayyane ta ce, "Tsoron masifarsa nake ji." yar ta daure a hankali ta taka zuwa bakin ofar ta kasa kunne wai ko zata ji motsi amma shiru babu motsin kowa. Hannu ta kai da niyar wasawa kawai aka bu ofar. Baya ta yi da sauri yanayin da ta ganshi ya saka gabanta ya yi mugun fa uwa. Farar singlet ce a jikin sasai brown in wando three quater wanda bai zo arasa guiwa ba, Gaba aya farin jikinsa a bayyane yake, fatarsa har aukar ido take yi gashi ya lullu e ko ina na jikinsa. Ganin ta ru e tana rawar jiki ta sunkuyar da kai ya saka yake kallon ta. Ita bata yi gaba ba kuma bata yi baya ba, ta tsaya cak kanta a asa kamar munafuka. Bakin ta ya fara rawa tana son yin magana tana jin tsoro, shima bai motsa ba kallonta yake yi yana mamakin dalilin zuwan ta wajan har take niyar wasa ofar. Nayla ta daure ta ce, "lokacin Tahajjud ne ya yi shine nazo na sanar da kai." Gira ya age guda aya yana an girgiza kai ya ce, "oh haka aka ce miki bana sallah sai kin zo kin tashe ni?." Ta girgiza kai ta ce, "tunasarwace." "Bani da bu ata, ko kabarin mu aya da ke?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "to ware." "Ba a yi masa abin arzu i, kullum zuciya a wuya kamar ba musulmi ba" ta fa asa- asa tana juyawa. "Me ki ka ce?." Da sauri ta juyo ta ce, "A'a ban ce komai ba." Bai ce komai ba ya wuce ya auki ruwa ya koma ya rufe akin. Murmushi ya yi a bayyane ya ce, "Wai kamar ba musulmi ba, yarinyar nan naci gare ta." Kallon sallayar da ya shinfi a yake yi kana ya ce, "tunasarwa ce" ya fa a cikin kwaikwayon muryarta. Sake murmushi ya yi ya kalli jallabiyar da ta bashi tsaraba ya auka ya saka ya tayar da sallah yana murmushi shi ka Nayla kuwa sai mita take a zuciyarta ta kuma yi alqawarin baza ta sake tashin sa ba komai zai faru. A haka tayi sallah har aka yi asuba, bacci ka an tayi ta tashi ta yi wanka ta shirya ta tafi wajan aiki. Shi kuwa Omaar bai fita da wuri ba yana jin fitar ta da mota da yadda take wahalar bu e gate da rufewa, yana tsaye yana kallonta ta window da take akinsa yana kallon yadda take kiciniyar rufe gate in kamar zata yi kuka. Tsaki ya yi ya ce, "shagwa iyar banza, kalli yadda take ta e fuska kamar wani ne ya sakata zuwa aikin." Tsaki ya sake yi ya bar wajan shima wanka ya yi ya shirya ya fita saboda yanzu aikin yawa yake masa. Yana fitowa falon gidan ya tarar dashi yana ta hamshin turaren wuta, ya girgiza kai yana kallon falon dan ya burge shi sosai a shirye tsaf dashi. Wayarsa tayi ara ya auko daga aljihunsa yana kallon wayar, ganin ba uwar number ce sai ya auka saboda kwana biyu ana yawan kiransa da sabuwar number. Bayan
Chapter 18 · 0% Book details