← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 205

Sashe 57

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baki goyan baya akan Omar na tabbatar da son da take miki. Amma ki bani labarin abinda ya faru, na ta a tambayarki amma lokacin a ru e ki ke baki bani amsa yadda nake so ba, yanzu ki fa a min." Nayla ta ce, "shine ai na fa a miki Mama, ta bani goyan baya sosai har turo ni Kano duk Mama ce tace nazo. Ban san meyasa zuwa na Kano ya atawa Abiy rai ba, amma har message ta ce na tura masa na ban ha uri." Mama ta girgiza kai ta ce, "kuma kin tura in?." "Ma tura masa, daman ha uri na bashi ha urin tun a gida, na kuma ce na ha ura zan za i guda aya a cikin masu neman auren nawa. To ban san me ya yiwa Abiy zafi a kalamai na ba, dan ni dai na san iya message in na da nayi masa shine abu na arshe da ya ha a ni da Abiy." Mama ta ce, "Allah sarki Zeenatu, ai mutuniyar kirki ce tana sonki sosai. Amma kin gane Nayla, ko dan gaba ba a fa ar matsalar gidan miji Nayla, koda Ummanki tana raye in ta tambayeki matsalar gidanki ba a fa ar damuwa ko acin rai, farin ciki ake fa a a oye damuwa. In kin ga an fa i damuwa to tayi miki girman da baza ki iya warwareta da kanki ba, to a sannan sai iyaye su shigo ciki. Ki kiyaye daga yau kin ji?." "To ni da za a raba auren Mama?" ta fa a ido na cikowa da hawaye." Mama ta ce, "ai zaki sake wani auren ko?." Nayla bata ce komai ba Mama ta ce, "kar ki damu, ki yi abinda zuciyarki take so ki za i wanda yake sonki ba kike so ba. Nayla da ki zauna da namijin da baya aunarki gwara ki zauna da namijin da ke ce bakya aunarsa. Zai kyautata miki, zai baki farin ciki saboda yana hangen gaba zaki so shi. In kuwa kece ki ke so baya sonki ko wacce bola ya kwaso ke ce, babu daraja balle mutuntawa da farin ciki, duk abinda zaki yi baza ki burge shi ba dan ba sonki yake yi ba. Amma ki yi tunani ki kuma cigaba da addu'a, in akwai sauran zama tsakaninku Allah zai daidaita, in babu Allah ya ha a kowa da rabonsa. Kar ki tursasa zuciyarki yin abinda bakya son dan farantawa wani rai ba, rayuwarki ce, ke zaki zauna a ciki ba wani ba." Nayla ta aga kai cike da gamsuwa da maganar Mama ta ce, "to Mama." Mama ta ce, "Yauwa, Salma zauna da ita, Zahra zo mu je na baki sa on ki wuce dare ya yi" ta fa a tana tashi ta fita daga akin ita da Yaya Zahra. Nayla ta kifa kai a kafa ar Salma, Salma ta ce, "ki yi ha uri, ki ta addu'a kamar yadda Mama ta ce." Nayla ta ce, "Salma na rasa meyasa nake sonsa har yanzu, zuciyata ta kasa kar ar laifin da ya yi min." Salma ta ce, "kar ki yi kuka, na tabbatar da zai fahimci kuskurensa zai kuma zo kamar yadda su Daddy suka ce. Amma sai kin yi ha uri, hakan da ki ka yi shine daidai, ta haka zamu tabbatar da mahimmacin da ki ke dashi a wajansa. A haka zamu gane shin ya auke ki matsayin matarsa ko bai auka ba, ki yi ha uri ki ta addu'a." "Salma in kuma bai zo ba fa?." "Zai ma zo." "Hmmm baki san wannan ba, bana ji a jikina zai zo Salma, inda ace yana sona zai iya yin komai a kaina, dan yana girmama abinda yake so na gani akan Didi. Amma tunda har ya furta na tabbatar da bazai zo ba Salma, Didin ma da yake aunarta ba yaleta ya yi ba balle kuma ni." Salma ta ce, "Kar ki damu zai zo in sha Allah." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "In bai zo ba ma shikenan ai, ni dai bazan koma ba." Salma ta ce, "ki kwantar da hankalinki don Allah, gaba aya hankalin Hajja ya tashi da ta ji ance kina gida, in kina tayar da hankali haka ya ki ke so mu kasance? Kowa ya damu dake kina gani." Nayla ta ce, "shiyasa nake alfaharin kasancewata a familyn nan, kowa yana matu ar ji da ni. Har Ya Abbas da nake ganin kamar ala ar mu ta are bai canja min, duk ya damu da damuwata, dana motsa zai ce sannu Nayla, kina son wani abu." Salma ta ce, "to kin gani, ki yi ha uri damuwarki ce ba ma. Kuma Ya Abbas ai Yayanki ne, dan yace yana sonki baki aure shi ba kawai sai ya canja miki? A zamanin jahiliya ake wannan ai. Kira Twiny mu yi hira." Nayla ta ce, " yaleta kawai, Didi ma nake so na kira naga kiranta tun jiya, amma sai gobe zan kirata." Salam ta yi murmushi ta ce, "to na baki labari?." Nayla ta kalle ta ta ce, "Ina jinki." Ta yi dariya ta ce, "yarinya in baki wasa ba nan gaba ka an zaki fara kirana da Anty." Kallon da ta ga Nayla tana yi mata alamun arin bayani ya saka tayi dariya ta ce, "Yaya J, tun saudia da azumi yake ta shige min, ashe ashe" ta fa a tana yalwa da dariya. Nayla ta wara ido cikin tsantsar farin ciki ta ce, "Are you serious? Salma da gaske ki ke? Yaya J ina na Kaduna shine yake sonki?." Salma ta harare ta ta ce, "To aga min murya su Mama su ji, Ina fa a miki a sirrinace zaki yi min handsfree?." Nayla cikin farin ciki ta ce, "Salma na ji da i, na kasa oye farin cikina. Wayyo Allah, wallahi kun dace da Yaya J, Yaya j arshe ne wajan kirki Salma, please ki yi accepting insa." Salma tayi murmushi ta ce, "Iya excetiment in fuskarki ya bayyana min abinda yake zuciyarki. Zan yi tunani akan Yayan na ki na gani, Amma fa ke ka ai ki ka sani, kar ki fa awa aya munafukar anwar tasa." Nayla tayi dariya sosai mai nuni da farin cikin da take ciki ta ce, "Ai wallahi sai ta ji labari." Salma daman burinta ta saka ta farin ciki sai ta ce, "Babbar matsalar ma in na amince masa duk annensa sun raina ni, bazan ba ku umarni ku bi ba, taya zan amince bayan jira ku ke duk abinda ya faru bayan auren na fa a mu ku?" Ta fa a tana kashe mata ido aya. Dariya suka yi a tare suka tafa Nayla ta ce, " annen ango, aminan amarya." Salma ta mi e ta ce, "Ke na gudu, gobe zan dawo in sha Allah." Nayla ta ce, "To amaryar Yaya J." Ta harareta ta ce, "Don Allah kar ki fa a masa fa." Nayla ta ce, "bazan fa a masa ba, amma zan fa awa twiny." "Munafukai" ta fa a tana fita daga akin tana jiyo dariyar Nayla daman kuma abinda take so tayi in kenan. KRB3P32 Arewabooks@nanahaleemq11. Mama da Yaya Zahra tunda suka fita suke tattaunawa akan batun Maman su Nayla. Yaya ta ce, "Mama anya ba itace ta saka mahaifin Nayla ya yi fushi har ya aura mata yaron nan ba?." Mama ta ce, "baza ku yi zarginta ba Zahra, Zeena ta so Nayla, ta kuma raineta bisa amana da kuma zuciya aya. Ta yi mata tarbiyya irin wacce ta yiwa arta, ta aunace ta kamar yadda ta aunaci na ta, in ta so cutar da Nayla zata cutar da ita tun kafin ta kai girman haka. Bana shakku ko zarginta akan wani abun na cutarwa akan Nayla, abinda ya saka na dasa mata ayar tambaya akanta; meyasa take nuna mata zaman ta Omar shine mafita kawai?." Yaya ta ce, "Haka ne Mama, amma abinda ki ka ce in shine nima ya tsaya min a rai kenan." Mama ta ce, "share batun kawai, bara mu jira mu ga abinda zai faru." "Ni so nake ma auren ya mutu wallahi, Nayla sam ba ajinsa ba ce, ki duba wani gida da aka ajjiye ta kamar gidan kaji." "Kar dai ki fa a ta ji, wallahi tana son yaron nan har yanzu, kawai ya yi mata abinda ya karya mata zuciya ne shiyasa ta za i haka. Dan haka ki iya bakinki, in ta koma masa zata dinga tunawa da abinda ki ka fa a a kansa." Yya Zahra ta ce, "ikom Allah, ko meye abin so oho?. Ina jin kyaunsa ne ya auki hankalinta." Mama ta ce, "Barr Nass ar gidan Senator haka ta haukace a kansa, farin jini gare shi kawai." Ta yi dariya ta ce, "farin jini a wajan an daban? kuma farin jinin ma na yara kyawawa masu asali irin su Nayla?. Kuma sunayen su daga N ya fara." Mama ta yi murmushi ta ce, "Wannan hasahen naki ne, ki wuce ki tafi dare ya yi" ta fa a tana fita itama Yaya Zahra ta ha a kan yaranta suka wuce gida. Washe gari bayan Nayla ta kammala breakfast sai ga Salma, hakan ya yi mata da i dan tun jiya take farin ciki saboda labarin da ta bata, ganinta ya saka suka shige aki suna hira. Wayar Nayla ce tayi ara ganin sunan Didi ya saka tayi murmushi ta auka ta ce, "Tuba nake Didi, na so na kiraki jiya dare ne ya yi aallahi." Didi daga can angaren ta ce, "Nayla kin aga min hankali, na kira baki auka ba kuma baki kira ni ba. Lafiya dai ki ke ko?." "Lafiya lau Didi. Ina kwana." "Wallahi ba lafiya nake ba, amma yanzu da na ji maganarki lafiya lau." Murmushi Nayla ta yi ta ce, "Tuba nake." Didi ta ce, "Kina gida ne? Ina birkitaccen mijin na ki?." Nayla ta murmusa ka an ta ce, "Didi bana gida, Ina gidan Mama tun shekaran jiya." Didi ta ce,"Mama Sa'adatu?." Nayla ta ce,"Ita." "Amma dai lafiya ko?." Yadda tashin hankali ya bayyana a muryar Didi ya saka Nayla yin murmushi ta tausasa murya ta ce, "Lafiya lau Didi." Didi ta ce, "Lafiya lau zaki tafi gidan Mama har
Chapter 57 · 0% Book details