Sashe 122
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauti saboda azaba, bata cikin hankalin ta gaba aya, azaba ce take ratsa jijiyoyin jikinta. A lokacin Omar ya shigo wajan, suna ha a ido da ita ya sakar mata banzar harara wacce ta saka ta sake fashewa da kuka. Nurse in da yake mata dressing in ya ce, "Ciwon ya yi zurfi, dole ayi mata inki." Omar ya sauke numfashi yana kallon yadda take hawaye, hijjab in ta duk ya lalace da jini dan sai yanke hannun hijjab in aka yi aka fito da ciwon. auke kai yayi daga kallon ta, yana jin zuciyarsa kamar zata fito saboda tashin hankali da tausayinta. Zama ya yi a kusa da ita fuskarsa a aure ya ri e ta a jikinsa, ta kwanta a jikinsa tana kuka mai sauti. Kanta yaji da zafi sosai alamun ciwon kai, ya sauke numfashi bai ce komai ba saboda bazai iya magana. A haka aka yi mata inki tana kuka, kwantar da ita aka yi a asibitin saboda zazza in jikinta aka saka mata ruwa. Yana zaune a gefenta yana kallon ta tana sauke ajiyar zuciya cikin rashin nutsuwa, allurar da aka yi mata ya rage mata ra in da hannunta yake mata. Tk ne ya shigo akin cikin sanyin jiki ya kalli Omar ya ce, "tuba nake Tiger, na gaza bata kariyar da ya kamata." Omar ya kalle shi da jajayen idonsa ya auke kai. Bai ce komai ba, kai ya girgiza yana ha iye yawu mai aci, ya aga masa hannu kawai dole Tk ya fita. A haka baccin ya auke Nayla, ya yi ajiyar zuciya ya mi e ya dafa goshinta zuciyarsa cike da jin haushinta da kuma tausayinta. Tausayinta yake ji dan ya san bata ta a tsintar kanta a wannan yanayin ba, sannan haushinta yake ji akan laifin da ta yi masa. Ba jimawa Didi ta zo asibitin, ganin yanayin yadda hijjab in Nayla ya lalace da jini ya saka ta kuka, ya kalle ta da idanunsa da suka ance saboda acin rai ya ce, "ki daina kuka kar ta tashi, ki zauna da ita zan je na dawo" ya fa a muryarsa a dashe saboda damuwa. Didi ta goge ido ta ce, "me ya faru haka Omar? Waye ya ji mata ciwo haka?." "Ki zauna, zan je na dawo" ya fa a yana sake dafa goshin Nayla. Hijjab in jikinta ya cire mata ganin tana gumi, ya kalli inda aka ji mata ciwon yaga tsahon yankan tun daga guiwar hannunta har tsintsiyar hannunta. Ya sauke numfashi ya fita bai kula Didi ba. Ya jima bai dawo ba, sai goma na dare sannan ya dawo ya ce Didi ta wuce gida zai kwana da ita. Didi suka wuce da mijinta bayan ya saka Bashir ya yi musu rakiya, dan a yanayin da ake ciki komai zai iya faruwa. A haka suka zauna shi da ita, sai cikin dare ta farka suka ha a ido taga irin kallon da yake mata sai ta auke kai dan ita wallahi tsoronsa take ji ba ka an ba. Sauka tayi daga kan gadon ta shiga ban aki. Alwala tayi tana so tayi sallah amma babu mayafi, shi kuma babu fuskar da zata yi masa magana. Ganin haka sai ya fita dan ya je gidan Didi tunda babu nisa, yana fita suka ha u da mijin Didi ya kawo masa abinci da kuma kaya a leda. Komawa ya yi ya ajjiye mata bai ce mata komai ba. A tsorace ta auka ta saka hijjabin tayi sallah. Wayarsa ya mi a mata ta kalle shi suka ha a ido, ya aure fuska ya ce, "ki yi blocking bank account inki." A sanyaye ta kar a da hannunta da babu ciwo ta yi ta ajjiye masa wayar. Bai sake ce mata komai ba sai abinci da ya nuna mata. A yanayin da yake ciki babu damar yi masa musu, dole ta auka taci ka an ta ajjiye. A haka suka kwana shi da ita, washe gari ba a sallame su da wuri saboda zazza in da ya rufe ta, sai gab da magrib suka wuce gida bayan an bata magani. Tana zaune a falo tana kallon hannunta, abinda ya faru ya dinga dawo mata cikin kanta tsoro ya sake mamaye mata zuciya. Jin ta take yi kamar ba ita ba, ji take kamar ta gudu Kaduna ta huta da tashin hankali. Gaba aya zaman Kano ya fita daga ranta, zama da Omar ya fita daga zuciyarta gida take so ta koma ko hankalinta zai kwanta. Omar ne ya shigo da sallama, ta amsa a ciki tana ago kanta. Kallo aya tayi masa gabanta ya fa i, abinda ya faru a daren shekaran jiya ya fa o mata a rai musamman yadda yanayinsa ya canja mata ya koma mata na wancan Omar in da ta sani. A hankali ya tako ya zo inda take, ya bita da kallo cike sa tausayi ganin yadda ta rame lokaci aya, duk ta firgice kamar ba ita ba. Ya auke kai daga kallon ta, ya daure ya kawar da tausayin ya ce, "Dan baki da hankali, baki da tunani zaki fita ki bar gidan nan ba tare da na sani ba? Ba sai da na ce miki kar ki je ko ina ba?." Nayla bata san ta mi e tsaye ba, jikinta ya cigaba da rawa tana jan numfashi da yar ta ce, "tsoron gidan nake....." wata irin zabura ya yi ya aga hannu kamar zai mare ta ya ce, "wallahi Allah ki ka arasa sai na mare ki!." uf tayi, numfashinta yana neman aukewa tana kallonsa a tsorace. "Uban meye a gidan da zai baki tsoro? Dah ba a cikin sa ki ke zama ba?. Dan kin raina min hankali sai ki auki afa ki bar gidan nan ba tare da na sani ba, a irin wannan yanayin da ake ciki da an kashe ki fa!?. Kalli ciwon da aka ji miki, da sun same ki a inda zasu kashe ki fa!?" Ya fa a cikin fa a yana nuna mata ciwon hannunta. Tsoronsa ne yake tsirga mata, jinin shekaran jiya kawai take gani a jikinsa, ga wanda ya nuna mata wu a ya wace mata waya, ga wanda ya sare ta har jini ya dinga zuba, sai abin yayi mata yawa. "Dan kinga ina sakar miki fuska shine raini zai shigo ko? In ba dan kin samu dama ba har kin isa ki bar gidan nan ba tare da na sani ba?. Kuma dan tsabar rashin hankali ki hau abin hawa na haya ki bar gidan nan ba tare da nace ki je ba. Yaushe ki ka raina ni haka?." Bakinta yana rawa tana kallonsa ganin ya canja mata gaba aya, soyayya da tausayin da take gani a idanunsa yanzu duk ya gushe. are masa kallo take yi tana tabbatar da wannan ba Rouhii ta bane, Omar Tiger ne na gidan Didi. Ganin ta i magana ya saka ya ce, "ba magana nake miki ba!." "Ni ban....rai....na.....ka......ba" ta fa a a rarrabe tana kallonsa "Iskanci ne kenan? Iskanci ne ya saka ki ka fita daga gidan nan ba tare da izinina ba ko?." "Na yi maka....text..." ta sake fa a murya na rawa. "Da ki ka yi min text na baki amsa?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "raina ni ki ka yi kenan?." Ta fashe da kukan da yake cin ranta ta ce, "A'aaaaaa!" Ta ja kalmar da arfi tana kuka mai sauti. Ya girgiza kai yana nuna ta da yatsa cikin jin haushin ciwon da aka ji mata ya ce, "in kika sake wannan gangancin mai raba ni dake sai Allah, wallahi duk ranar da ki ka kuma aikata wannan ganganganci sai na sa a miki kammani ta yadda babu wanda zai iya gane ki." Ya bita da harara sannan ya ce, "ki wuce ki auki abinci ki ci." A zabure ta nufi inda ya nuna mata ta auki robar abincin da ya yi order daga Leemars_delicious tana ci tana kuka. Yana tsaye a kanta dole ta dinga tura abincin ba dan tana jin da i ba, ya bi ciwon hannunta da kallo tausayinta yana sake shiga jikinsa. Bai nuna mata ba, sai da ta ci rabi sannan ya sake jan tsaki ya bar wajan. Yana barin wajan ta ora hannu a kai ta fashe da kuka ta ce, "Na shiga uku ni Nayla, na auri an daba!" Ta fa a cikin fitar hayyaci. KRB3P073 Nanahaleema. Nayla bata san lokacin da ta auka a wajan ba ta ji an ta a ta, wata irin zabura tayi ta mi e sai taji an ri e kafa arta Didi ta ce, "Nayla ni ce, nutsu." Nayla da take a gigice ta ce, "Didi!." "Na'am Nayla, ki nutsu. Kar ki fama ciwon hannun ki." Fa awa jikin Didi tayi ta rungumeta tana sake faahewa da kuka. Cikin tausayinta Didi take shafa bayanta ta ce, "Ki daina kuka Nayla, ki nutsu kin ji?.." cikin kuka ta ce, "Didi jini ne a jikinsa, da daddare aka zo aka dinga buga gidan nan ana cewa in ya isa ya fito" ta ago daga jikin Didi ta ce, "Shine....shine.....ya auki wu a ya fita. Ina zaune ya dawo jikinsa duk jini, Didi jini ne a jikinsa da alamun ya yi fa a da wani. Tsoro nake ji Didi, ki auke ni daga gidan nan, tsoronsa nake ji. Gaba aya ya canja, baya jin tausayina, sai fa a yake yi min, har ya aga hannu zai mare ni" ta fa a tana sake komawa jikin Didi tana kuka. A sanyaye Didi ta ce, "Ya isa, ki nutsu ki daina kuka. Kinga baki jima da dawowa daga asibiti ba." Zaunar da ita Didi tayi ta bata ruwa ta sha tana ri e da hannunta tana kallon ciwon da aka inke. Sai da ta nutsu sannan ta ce, "ki yi ha uri, ki dawo hankalinki." Nayla ta ce, "da naje gidan ki shine aka wace min waya, aka ji min ciwo a hannuna." "Ki yi ha uri, ki daina kuka" ta fa a tana dafa kafa arta cikin rarrashi. Nayla ta koma sauke ajiyar zuciya zuciyarta tana bugawa sosai. "Didi!" Omar ya furta cikin dashewar yana shigowa falon. Wani irin tsalle Nayla tayi ta fa a jikin Didi