Sashe 4
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ji. In ba addara ba wallahi tafi arfin Omar nesa ba kusa ba, yanzu haka aikin gwamnati take yi duk da dukiyar da mahaifinta yake da ita. Ga kyau masha Allah kamar ita tayi kanta. Shi ba abin farin cikinsa bane ya tsinci dami a kala? In aurota zai yi ina ya ga abinda zai kashe ya aureta?. AbdulHamid ya ce, Ki bar zuciya da abinda take so, haka ki bar zuciya da abinda bata so. Ita tana sonsa, shi kuma baya sonta, kowa shi ka ai ya san abinda yake ji a ransa. Shiyasa take baki tausayi, inda ace bata sonsa da kaina zan saka ya saketa kawai a warware auren, amma tana sonsa sosai tana burin mallakarsa a matsayin mijinta. Shiyasa na i bashi damar sakinta, ba dan na ba anta masa nayi hakan ba sai dan saboda soyayyar da take yi masa. An ce iyayyar namiji tafi ta mace zafi, har gwara ace itace bata so akan ace shine baya so. Aka yi rashin sa a namijin ma irin Omar! Karkataccen mutum mai shegen ri on tsiya. Tunda nayi masa fa a a gabanta yake jin haushinta, ashe itace matarsa dukkan mu bamu sani ba. Wallahi lamarin Omar yana damuna sosai. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, kar ki damu, ki tayi masa addu a komai zai zama daidai. Kuma zancen iyayyar namiji duk zance ne kawai wuyarta dai ya fara sonta, daga lokacin da Allah ya saka masa sonta a zuciyarsa wallahi duk wannan wahalar da yake bata sai ta fanshe cikin ruwan sanyi. Ke ai kin fini sanin komai, kin san halin ku na mata da lagon maza da ku ka haddace a kan ku. Ki yi masa addu a kawai, in yaso gobe sai na dawo dake mu kai shi gidan amaryar. Yanzu ita da wa zata kwana?. To bana ce ba, amma muje gidan yanzu nayi magana da ita, gwara na fa a mata gaskiya kawai kar na oye mata ai ta san halin Omar Eh ki fa a mata, amma kar ki yi amfani da kalaman da zata ji babu da i. Ki yi magana yadda zata fahimta, in yaso ko gida zamu wuce da ita ta kwana sai mu tafi, in yaso goben in kika rarrashi Damisar sai mu dawo. Didi ta ce, Damisar gaske, in ji Hajja tace carbin wai janka sai mai nutsuwa, to shi Omar mai nutsuwar ma hargitsa shi yake yi. Murmushi yayi ya ja motar zuwa ofar gidan dan babu nisa sosai, in da afa ne yafi nisa, in a mota ne gidan babu wahalar zuwa. ofar gidan ya ajjiye motar tare da kashe motar, Didi ta kalli gidan tana sauke numfashi. Gate in gidan fari ne mai aukar ido, ofar gidan da haske sosai gidan ya yi kyau kana gani kasan sabo ne. Wajan bashi da jama a sosai duk da aya unguwar ne amma wajan gidan su Didi ya fi mutane akan wajan gidan Nayla. Bu e motar Didi tayi ta shiga gidan zuciyarta sam babu da Gida yana da wajan ajjiye miota guda aya sai hanya mai girma wacce za siya ajjiye babura har gida biyu. Kana ganin gidan ka san sabo ne ba a jima da gama shi ba, komai sai aukar idanu yake, ga wasu flowers da suka fara tasawa daga gefe an zagaye su anyi musu ado da ananun fitila a ciki. Sai ka hau steps guda biyar wanda aka zagaye su da staircase silver, ga chandelier light da ta haske ofar falon mai kyau. Falon ta bu e ta shiga, yana girma amma ba sosai can ba sai dai ya yi kyau matu a, kai kana ganin falon kasan ku i da masu ku i ne suka ha a shi. Ya sha kujeru na alfarma, ga 85 inchs plasma an orata akan tv stand mai kyau da girma, ga turkish carpet da ya mamaye tsakiyar falon an ora masa center table a kai. Daga can gefe ga dining room an saka dining table mai guda shida, ya sha adon show glass cabinet, an saka plates, mugs da glass cups. Kusa da dining in fridge ne babba mai tsaho da girma. Daga can arshen falon an saka cabinet in da aka yi ado turaren wuta da humra, an yi ado da fitila a ciki sai kawowa suke suna aukewa. Didi da yake ta san gidan bata tsaya are masa kallo ba kai tsaye aya aramin falon ta shiga. Shi da yake bashi da girma kujerun sa basu kai wa ancan girma ba, shima akwai tv da carpert komai ya fito tsaf gidan an gayu. A zaune ta tarar da Nayla da Salma da kuma Jidda suna ta rarrashin Nayla da take zubar da hawaye. Sallamar Didi ya saka suka kalle ta tare da amsawa, ta zauna kusa da Nayla ta dafata ta ce, Nayla har yanzu kukan ne? Jikinki da zafi, Salma ki yi mata allura. Salma ta ce, na yi mata, sai tayi bacci zata ji da Sannu kin ji Nayla, Allah ya ara miki lafiya. Kiyi ha uri kin ji?. Hawaye ya sakko daga idanunta ta share hawayen tana numfashi. Didi ta kalli Salma da take kallon ta itama, kafin Didi ta ce wani abu Salma ta ce, Ina angon? Ya i zuwa ko?. Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, a yanzu zai araso shiyasa nazo, kin san hali basai na fa a ba, zuma ne sai da wuta. Salma ta murmusa kawai bata ce komai ba. Nayla jin zaizo sai ta mi e kawai ta shiga bedroom bata ce komai ba. Didi ganin ta shiga ciki ya saka Didi ta sauke murya asa ta ce, Tsakani da Allah Omar bazai zo yau ba, ya ce ya kar i auren a yau bazai kuma yin wani abun a yau ba. Salma kin dai san halinsa kema, ni in ma ba barina yayi ba. Na fa i haka ne akwai saboda bata da lafiya, kar na fa i abinda na fa a miki taji babu da i a zuciyarta. Yanzu ya za a yi? Ko zata bi ni mu je gidana ta kwana? Kin ga ai babu da i a ce ta koma gidan Hajja ko gidan Daddy ko?. Jidda cikin damuwa ta ce, gaskiya babu, ko mu tafi gidana ta kwana kawai?. Didi ta ce, a Jidda, mijin ki zai yi mamakin ganin amarya a tare dake. Masalaha kawai ta bi ni in muje ta kwana, ba a barta ta kwana ita ka ai ba ko?. Salma ta girgiza kaita ce, gaskiya Omar bai kyauta mana ba Didi, ki yi ha uri da abinda zance. Omar ya daina ganin kamar sadaka aka bashi Nayla, Allah na tuba ba dan wannan abin da ya faru ba wallahi Nayla ba sa ar aurensa bace, Nayla matar manya ce ba ta ananu ba wallahi. To addara ta riga fata, da kuma sharrin so. Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, na sani Salma, na sani ki daina bani ha uri gaskiya ki ka fa a ai ba arya ki ka yi ba. In ba dan sharrin soyayya ba ina Nayla Ina Omar? Ba tsarar aurensa bace, tazarar su na da matu ar yawa. Nayla in ce ya kamata ace tana wannan abinda yake yi ba sai shi. Gaskiya ni haushinsa nake ji wallahi, meyasa bazai kar addara a yadda tazo ba? Ita Nayla ba addarar ta arba ba har take zaune a gidan nan? Salma ta fa a a an fusace dan haushin Omar take ji sosai. Jidda ta ce, duk ba wannan ba, meye mafita?. Didi ta ce, Ku lalla ata tazo mu je gidana mu kwana, ni kuma zan saka Omar ya dawo gidan nan gobe in sha Allah. Salma ta ce, Didi babu tabbacin dawowarsa. Gaskiya babu tabbas Salma, za a kai ruwa rana dashi a wajan dawowa gidan nan, musamman in ya san daga hannun waye gidan nan ya fito. Amma zan yi maganinsa, zai zo in sha Allah. Salma ta ce, Ku je kawai ni zan kwana nan, zan fa awa Hajja bata da lafiya ne shiyasa akace na kwana saboda zan saka mata ruwa. Daman kamar na san hakan zai faru na ce Mima ta kwana a gidan Hajja, dan haka ba wata damuwa. Didi ta ce, kina ganin hakan ya yi?. Ya yi Didi, kar ki damu. Kema duk ya saka ki a damuwa da zullumi da fargaba. Didi ta ce, Hmmm bari kawai Salma, b aza ki gane ba kawai, amma ni ka ai na san waye Omar. Amma in sha Allah silar wannan auren shine silar canjin halayyarsa. Ina so ya so Nayla fiye da komai a duniya, ita kuma duk wannan hawayen da yake sakata a lokacin nake so ta fanshe. Suka yi dariya Jidda ta ce, Wallahi nima Didi Ina ji a raina auren nan nasu ba mai mutuwa bane, haka Allah ya addarar zuwansa shiyasa hakan ya faru. Amma dai zama da Omar in ne sai an shirya. Didi ta murmusa ta ce, Allah ya sa hakan, in hakan ya tabbata ba wani shirin da zata yi, a hankali zata mayar dashi yafi ruwa sanyi. Suka amsa da amin suka fito ita da Jidda. A harabar gidan suka tsaya Didi ta ce, Salma kwana ku biyu babu hatsari?. Salma ta ce, unguwar su Tiger ce fa, kuma matar tiger in ce a gidan kar ki manta. Amma waye ya san ita matarsa ce? Ko na yiwa su Bashir magana wani yazo yana zagawa?. Salma ta ce, kar ki damu, babu abinda zai faru in sha Allah. Didi ta amsa suka fita ta shiga motar AbdulHamid, Jidda ta shiga ta mijinta suka bar cikin unguwar. KRB3P003 Arewabooks@nanahaleema11. Salma a sanyaye ta koma bayan ta rufe gidan yadda ya kamata, tana shiga falon ta kulle falon ta shiga bedroom in da Nayla ta shiga ta kwanta. Tana shiga Nayla ta ago kai ta kalle ta ta ce, Baki wuce ba?. Salma ta zauna ta ce, a na zan Kwana ai. Hajjan fa?. Na tura Mima ta fa a tana zare ankwalin kanta. Nayla tayi ajiyar zuciya tare sa lumshe idanunta. Gata daina gidan wanda take matu ar so take kuma aunar rayuwar dashi a matsayin matarsa amma shi baya nan yana