Sashe 63
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
address in gidan zan je." Didi ta ce, "Da gaske ka ke?." Omar ya ce, "kin san ba wasa nake yi ba ai, zan je ina bu atarta tare dani. Na yarda da duk abinda ki ka fa a, da gaske ina matu ar sonta Didi, Ina yi mata son da bana yiwa kaina. Didi ko abinci na kasa ci, kamar ana gasa zuciyata haka nake ji. Kullum da zazza i nake kwana, damuwa ta yi min yawa, zuciyata ta kasa jure wannan yanayin. In na sake na kai gobe ban ganta ba wallahi zaki iya zuwa ki auki gawata, ni ka ai na san yanayin da nake ciki Didi, na kasa jurewa!" Ya fa a a hankali kamar zai yi kuka. Didi ta yi ajiyar zuciya cikin farin ciki tace, "Alhamdu lillah! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, ko yau Allah ya auki raina ya cika min burina. Omar yana son Nayla, Allah na gode maka." Shiru ya yi bai ce komai ba Didi ta ce, "Yaushe hakan ya faru? Yaushe ka fara jinta a zuciyarka?." Omar ya yi ajiyar zuciya shima ya ce, "Ban sani ba Didi, ni kaina bazan ce ba. Abinda na sani kawai soyayyarta ba yanzu bace, Didi ta jima a raina, ban fahimta bane sai yanzu. Wallahi Didi ina sonta, ina aunarta sosai." Didi cikin zumu i ta ce, "To yanzu yaushe zaka je?." "In anjima, amma ina so mu je tare dake, Ina jin nauyin mutanen nan sosai, ban ta a jin nauyin mutum kamar yadda nake jin nauyinsu suda mahaifinta ba, lokacin da mu ka je Kaduna kasa magana nayi saboda girmansa da naji a idona da zuciyata." Didi ta ce, "bazan je ba, kai ka ai zaka yi fa an ka, in har da gaske kana sonta kai ka ai zaka je ka dawo da ita. Amma ka kwana da sanin babu lallai ta dawo a zuwan farko." Omar ya an murmusa ya ce, "Hmmm Didi kenan. A yadda nake ji a zuciyata ko da za a shekara bata dawo ba indai zata dawo zan iya jira." Didi ta yi murmushi ta ce, "Gaskiya ne Omar, Allah ya tabbatar da alkhairi ya daidaita ku." "Amin Didi. Ki tura min address in." "An gama angon Nayla." Murmushinsa ta ji mai matu ar sauti kafin ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Kin san an kawo min motar da na siya? Kwanan ta hu u kenan, da yake bana cikin nutsuwa ban ma ganta ba sai jiya da daddare." Didi ta ce, "ma sha Allah Omar! Allah ya sanya alkhairi. Wallahi shigowar Nayla rayuwarka alkhairi ne, daga lokacin da ta je Saudia na ce ta yi maka addu'a daga lokacin Narma ta shigo rayuwarka. Shigowar Narma rayuwarka kamar farkar da kai daga dogon baccin da ka ke yi ne." Murmushi ya sake yi ya ce, "Didi!." "Na'am angon Nayla." Murmushi ya sake yi wanda ya nuna mata ya ji da in sunan har cikin zuciyarsa ya ce, "ina jin da i in kika fa i sunan nan, amma yanzu dai ki fa a min inda zan je kin san bana son ata lokaci." Didi ta yi dariya ta ce, "To yanzu kuwa." "Basai na siyi komai ba?." "Zaka iya siya mana, koda kayan marmari ne zaka iya siya ka kai musu duk girmamawa ce." "To" ya amsa a ta aice. Kwatancen gidan Daddy tayi masa ya yanke wayar da niyar in an idar da sallar la'asar zai je ya samu Daddy dan ya dawo da matarsa. Omar zai je bikon Nayla KRB3P035 Arewabooks@nanahaleema11. Omar cikin arfin guiwa da karsashi ya shirya cikin manyan kaya, ya saka shadda kalar golden mai kyau sai aukar ido take yi, sabuwa ce dal bai ta a sakata ba, tana cikin wanda ya inka gab da Nayla zata tafi dan shi mutum ne mai son inka suttura. Bayan ya kammala shiryawa ya saka hula ya tsaya yana kallon kansa. Samun kansa ya yi da murmushi cikin mamaki wai shine yake wannan zumu i akan wata mace, tabbas ya amince da maganar Didi ba son Narma ya yi ba, dan a cikin kashi goma na abinda yake ji yanzu ko kashi aya bai ji ba a lokaci Narma. Wayarsa ce tayi ara ya san bazai wuce Didi ba yana dubawa yaga itace ya auka ya saka a kunne. Da to kawai ya amsa sai ya kashe sai ga video call in Didi ya shigo. auka yayi daga can angaren Didi ta ce, "kai ma sha Allah angon Nayla, gaskiya ka yi kyau sosai, daman Ina ta fargabar kar ka ce zaka je da ananun kaya shiyasa na kira ka." Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Haba Didi! ya za a yi na saka ananun kaya?." "Ai na san hali ne." "Lokacin da bana so kenan, yanzu kuwa ai ina so." Didi tayi dariya ta ce, "Gaskiya ne Omar. Ka yi kyau wallahi, Allah ya dawo da kai Lafiya. Duk abinda ya faru ina jiran labari, Kuma don Allah kar ka je ka ce zaka zauna akan kujera ka yi area- are, gidan sirikan ka ne dai." Fuska a sake ya ce, "To Didi. Baki zo kin ga motar ba." Didi ta ce, "kai zaka kawo min ai, kai kuma yanzu hankalin ka baya jikinka, ka gama da dawo mana da Nayla in ya so komai ya biyo baya." Murmushi ya sake yi ya ce, "yaushe zaki haihu ne?." Didi ta ce, "na kusa, ka cigaba da yi min addu'a Allah ya sauke ni afiya." "In sha Allah." Didi ta ce, "ka je ka dawo." Yanke wayar ya yi ya fito daga akin yana kallon falon. Zuciyarsa ya ji tana bugawa sosai ya dafe saitin zuciyarsa yana jan numfashi, bai san me zai tarar ba in yaje shiyasa yake fargaba. A bayyane ya ce, "Allah ka bani ikon iya sarrafa kaina koda wani abun zai ata min rai." Ya furzar da iska ya fito yana kallon sabuwar motarsa da take ajjiye. Motar mai kyau ce a wuluk zubin matasa an kwalliya kamarsa sai aukar ido take yi. Tunani yake ya je a motar ko kuma ya kira Bashir ya kai shi a machine?. Katse tunanin ya yi ya kira Tk ya ce yazo gate in gidan. Ba jimawa yazo yana ganin Boss in na su sai ya yi murmushi ya ce, "Allah ya biya Damisa, irin wannan kyau haka, gaskiya ka yi kyau sosai." Murmushi yaga ya yi amma bai ce masa komai ba. Tk ya yi mamaki sosai dan kwana biyu ko fuska baya saki balle murmushi, lallai yana cikin tsananin farin ciki sosai. Motar ya bu e ya kalli Tk ya ce, "Bu e min gate in." Tk ya bu e gate shi kuma ya fita da motar bayan ya bawa Tk key in gidan dan ya kulle, Tk bayan ya kulle ya dawo masa dashi sannan ya ja motar da bismillah ya bar unguwar. Kasancewar ranar babu aiki Nayla suna gidan Daddy ita da Salma da Ummimi. Ta ware sosai tana harkokinta duk da akwai abinda yake damunta daga zuciya amma bata bari ya yi tasiri, musamman da aka auki wannan lokacin Omar bai zo ba sai ta sake arin kawar da tunaninsa dan ta san bazai zo ba. Daman ta san ko number ta bashi da ita balle ta yi tunanin in bai zo ba zai yi mata waya, wannan ya saka ta daure ta danne zuciyarta ta cigaba da addu'a tana shiga cikin an uwa ana hira da ita. Suna zaune a falon Daddy har da Daddyn kasancewar ranar asabar ce yana gida. Hira kawai suke yi tana cikin su tana dariya, Mummyn su Salma tana basu labarin uruciyar baban yayan su Salma wanda ya kasance mai tsare gida baya son raini. Abba ne ya yi sallama ya shigo falon yana cewa, "Nayla tun daga bakin ofa nake jin muryarki." Dariya tayi a tare suka ce, "Abba sannu da zuwa." Ya amsa suka gaisa gaba aya. Abba ya kalli Daddy ya ce, "na je gidan Hajja sai take shaida min kwana biyu baka da lafiya, shine na shigo mu gaisa." Daddy ya ce, "Hajiya Hajja kenan, mura ce fa kawai take damuna, amma kowa sai da tace masa bani da lafiya.Yanzu Sa'adatu ma ta shiga ciki." Abba ya ce, "Ai mura ciwo ce babba Yaya." Ya kalli Nayla da take yiwa Salma ra a a kunne ya ce, "Nayla kina da aure fa, meyasa ki ke yawo ne haka? Jiya ma na ga motarki a kan titin maiguuri road, ki daina yawo ba tare da izinin mijinki ba, har yanzu da aure a kanki." Nayla ta tsayar da dariyar da take yi ta sunkuyar da kai ta ce, "Abba gidan Twiny na je jiya." Abba ya ce, "amma a satin nan kin je gidana ai, sannan ga aiki da kike fita kullum, yau kuma ga ki a gidan nan, gobe kuma ki ce kin tafi gidan Khabir. Matar aure ce ke ki daina biyewa su Salma." Nayla ta ce, "To Abba." Daddy ya kalli Salma ya ce, "ke wai Salma me yake fito dake kina barin Hajja ita ka ai ne?." Salma ta ce, "Daddy duba ka nazo yi fa." "To ki yi gaggawa ki gama ki koma gida." Abba ya ce, "Ku shiga ciki Salma." Duk gaba aya suka tashi daga main falo suka shiga ciki gidan. Bayan fitar su Abba ya kalli Daddy ya ce, "har yanzu mijin Hauwa bai yi magana ba? Ni fa na gaji da jira wallahi, kawai a raba auren nan kowa ya huta." Daddy ya ce, "Bai zo ba Ali, abinda yasa bana so ayi gaggawa saboda Nayla tana son mijinta har yanzu, babarta Sa'adatu ta ce tana son mijinta wani dalili ne ya saka take cewa a raba auren." Abba ya ce, "Zancen banza kenan, meye amfanin soyayyar da take masa ana irin wannan abum?." Daddy ya ce, "mu bi komai a hankali Ali." "Assalamu alaikum, Alhaji barka da yamma" aka fa a daga bakin ofar falon. Daddy ya ce, "Wa'alaika Salam, Aminu shigo mana." Aminu ya shigo ya dur usa ya ce, "Alhaji ba o ka yi, ya ce don Allah nazo na sanar da kai." Daddy da mamaki ya ce, "Ba