← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 205

Sashe 160

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take yini kullum tunda itace bata da aure a cikin su, ko yaushe kusan tana nan tana bawa Nayla irin ta ta kulawar ta mutanen Chad, musamman angaren turaren wuta da humra da gyaran jiki. Ranar suna aka ra awa yarinya suna Aisha ake yi mata la abi da Musliha. Shanu uku aka yanka na ranar suna, aka yi decoration a harabar gidan dan gidan babba ne no need a fita event center, aka auko masu hoto da masu video da masu ki warya. Abinci kuwa ba a magana, dan komai da komai leemars_delicious ce tayi, kowa sai yabawa yake yi saboda da in abincin. Taro aka yi gagarumi, tun daga farkon gidan banner hoton Musliha ne har arshe, a cikin wani gado na glass aka saka ta duk wanda ya zo ya ganta a ciki ba a aukarta tana ciki tana bacci. Kafin a fara taron Nayla ta takura masa akan za a yi musu hoto da video, ya nuna baya so ta dage da magiya har ya amince, aka kira mai hoto da videographer aka yi musu a cikin gida shida ita da Musliha kafin a fara taro. Kafin a gama taro tuni hotuna sun ya u a duniya, masu hoton wajan da masu video suna ta orawa a duniya ana saka c.e.o exclusive footwear with his wife on their daughter's naming. Mutanen suna ta tofa albarkacin bakinsu, musamman yanayin kyaun da suke dashi sun dace da junan su sosai. Omar bai gani ba sai bayan an tashi daga taron kowa ya watse sai an uwanta. Ran maxa ya aci, aljanun tijararsa da rashin mutunci suka motsa. Nayla tana zaune kawai ta ganshi a falon ta, kafin ta bu e baki ya nuna mata wayarsa ya ce, "meye wannan?." Nayla ta kalli wayar ta ga hotonsu ne, ta kalle shi zata yi magana ya ce, "da izninki aka yi posting kenan?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "A'a ban sani ba, kawai sun yi ne saboda aikin su ne." "Oh aikin su ne ora matan mutane ba tare da izni ba? Aikin su ne dan sun yi maka hoto sai sun ya a a duniya?." Ganin ya fusata ya fara fa a sai tayi asa da murya ta ce, "suna yi ne saboda advert, amma...." "Amma me!? Da hoton naki da na ata za a yi advert in Jidda!?." Tayi ajiyar zuciya jin yadda ya fara yi mata halin, tsawar da ya yi mata har tsakiyar kanta, bata so maganar ta yi nisa sai ta ce, "ka yi ha uri." Ya girgiza kai cikin fushi ya ce, "Dole ki ce na yi ha uri ai, dole ki bani ha uri tunda sun riga sun yi, blog sama da goma sun yi reposting dole ki bani ha uri Jidda." Nayla ta kalle shi da damuwa ta ce, "ban san zasu yi ba, da nace kar a yi." "Yanzu ma ki saka su goge, yanzu ba anjima ba su goge hoto da video, ai ba da iznina suka yi posting ba. Ni ba shashasha bane da zan bar hotunan ku a duniya suna yawo da sunan wayewa ba, bana ra'ayi, daman ni ba wayayye bane, dan haka bazan yi aikin wayayyu ba. Bana so a cire yanzun nan, in ba haka ba wallahi zan yi ararsu!. Ai ba ni na ce su saka ba, kema ba ke kika ce su saka ba. In ba su goge ba kotu ce zata raba mu!." Jin yadda yake yi mata fa a sosai harda zancen zai yi ararsu sai tayi sanyi dan ta san laifinta ne, da ta ce kar ayi posting da ba a yi ba. A sanyaye ta ce, "To zan ce musu." Ko kallon ta bai sake yi ba yana fita cikin unar zuci. Salma da take zaune ita da Jidda dan sun fito lokacin da ya fara fa an, Nayla ta kalle su da damuwa ta ce, "Yanzu ta ina za a fara goge hotunan don Allah?." "Kema laifin ki ne Twiny, kin san halin mijinki da sai ki ce kar su yi posting." Nayla ta kalli Jidda ta ce, "Wallahi mantawa nayi Twiny, ban auka abin nasa zai zo da haka ba." Salma ta ce, "ki kira su ki ce su goge." Nayla ta ce, "kin san adadin mutanen da suka yi reposting kuwa? Kuma ni tsorona an TikTok wallahi, gwara an Ig zasu iya gogewa, amma an tiktok sai a hankali." Jidda ta ce, "haka zaki yi musu magana tunda baya so, sannan sai ki je ki bashi ha uri." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Hmmm Twiny ke baki san shi ba ne, amma Salma ta san waye shi ai. Wallahi in ransa ya aci wanda ku ka sani a baya yake komawa, baya aga min afa ko ka an." Salma ta yi dariya ta ce, "Tiger yana dawowa kenan. Amma ki je dai ki bashi ha uri, Yayanki ma in ni ce aka yi posting pics ina na shiga uku, ba ya aunar posting a social media da hotunana, wai ba tallata yake yi ba." Jidda ta ce, "Nima dai bana so wallahi, ban auki nuna hotuna na da mijina da sunan wayewa ba sam." Salma ta ce, "mu dai zamu wuce, ki je ku arke da Tiger lafiya, Allah ya sa kar ya yi kaca-kaca da naman jikinki. Jidda mu je" ta fa a suna fita suka bar Nayla da ajiyar zuciya. KRB3P098 Nana haleema A zaune ta same shi a falo ya rufe ido, ko da ya ji shigowarta bai bu e ba daman ta san bazai bu e ba, ta zauna a gefensa ta ce, "Rouhi ka yi ha uri, nayi mata magana zata goge yanzu in sha Allah." Bai bu e ido ba ya yi mata banza, zata sake yin magana aka kira shi a waya. Ya bu e ido ya kalli mai kiran ya ga Farid China da haka ya yi saving, ya an yi tsaki sannan ya auka ya saka a a speaker. Daga can angaren ya ce, "Omar ashe yau ake sunan babyn ka shine babu labari? Yanzu na gani a tiktok, gaskiya matarka she is so cute wallahi, kun dace, damn....." it ya kashe wayar ya cillar da ita akan kujera. Nayla ta sake tsorata dan ta san an kuma tsokano shi, in bai yi niyar magana ba ma yanzu ta san sai ya yi. Ya kalle ta bayan ya tashi zaune sosai ya ce, "Hankalinki ya kwanta ko? Hankalinki ya kwanta kin ji da i a zuciyarki an ga hotonki an ce kina da kyau, sai ki je ki siyi abin sadaka ki rabawa yara." Nayla ta kalle shi a raunane zata yi magana ya aga mata hannu ya ce, "kar ki ce min komai, ban ce ki yi min magana ba. Ba hakan ki ke so ba? In ba hakan ki ke so ba meyasa ki ka aikata!?." Ta sunkuyar da kai tayi shiru dan bata aunar wannan fa an na sa, fa a ne wanda bashi da full stop in ya fara, bai san kara ba kuma baya aga mata afa. Omar ya cigaba ya ce, "iya afarki ce ta fita a duniya nace miki bana so aka daina, amma da yake kina so a ga fuskarki sai kika iro da za ayi hotuna. Na ce bazan yi ba, ki ka yi min magiya na tsaya aka yi saboda tarihi kamar yadda kika ce, amma sai ki ka bada dama aka ya a min hotunan matata a duniya. Ke kin san me nake ji kuwa? Kin san lokacin da na ga afarki ana yabonta a duniya me naji?. Ji nayi zan iya aikata komai a lokacin, zuciyata tana bugawa, gangar jikina tana rawa matu a saboda kawai an yabi afarki. Yau fuskarki da surarki ake yabo..." ya fa a yana watsa hannayensa cikin tsananin kishi da acin rai. "Har wan anda ba sa jin hausa abokan kasuwancina sun kira ni suna cewa sun ga matata. Hankalinki ya kwanta an ganki ko Nayla!? To ta shi ki tashi ki bani waje!." Nayla ta kalle shi da sauri jin da sunan da ya kirata, zata iya irga sau nawa ya kira ta da Nayla, dan baya fa a kwata-kwata. Kuma ta san baya ta a ce mata Nayla sai in ta ata masa rai, a lokacin ne yake mantawa da Jidda ko Ashiq ya kirata da sunanta. A raunane ta ce, "wallahi Rouhi ban ce ayi posting ba, na san laifina ne da ban yi magana na ce kar ayi ba, amma ban san zasu yi ba." Kamar zai dake ta ya yo kanta da fa a a hargitse ya ce, "Amma kin san babu ta yadda za a yi ayi mana hoto nida ke ace baza a yi posting ba ko!? Likers suke nema, kuma matu ar aka oraki dole a samu likers har da comments. Meyasa baki wannan tunanin ba!?" Ya fa a a fusace yana zare mata idanu waje. Sak ya koma mata Tiger, kallon Tiger take masa lokacin da ya ora mata wu a a wuyanta yana zare mata ido, kallon tiger take masa wanda ta ganshi da jini kaca-kaca a jikinsa. Jikinta ya yi sanyi sosai, a hankali ta sake cewa, "na yi kuskure ka yi ha uri, amma yanzu na yi mata magana zata goge in sha Allah." Ya kalle ta cikin hararar da ta saka ta yin shiru, ya yi wafa tare da jan tsaki ya girgiza kai bai ce komai ba. Nayla ta duba wayarta ta nuna masa ta ce, "ka gani har ta goge ma." Ya Harare ta da jajayen idanunsa ya ce, "Ko ki matsar da wayar nan daga kusa dani ko na fasata, kuma wallahi in na fasa bazan siyi wata ba, kema kuma baza ki siya ba, na kuma ce wallahi." Nayla ta janye wayar ta ajjiye a gefenta, ya bita da kallon up and down ya ce, "Dan ta goge mutane nawa ne suke dashi? Mutane nawa ne suka saka su ma? Ko duk zaki bi su ki ce su goge ne?." Yadda ya kafe ta da ido shine ya saka ta sauke ido asa bata ce komai ba. Yaja dogon tsaki ya ce, "Kawai kin riga kin cuce ni, kin yi min
Chapter 160 · 0% Book details