← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 205

Sashe 128

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuciya ya ce, "To yaushe zaki yi cikin? Da Didi ta fa a sai na ji ina so ki yi cikin, sai ta saka min sha'awar ace kina da ciki Jidda. Yaushe zaki yi?." an kawar da fuska bata ce komai ba, ya ce, "Allah ki ka sauke ido asa zamu yi fa a dake, ke komai kunya yake baki? Maganar ma kunya take baki?." Nayla ta yi dariya dan ta san yana adawa da wannan kunyar, baya sonta ko ka an, ita kuma tana arin ta rage amma wani lokacin bata sanin ta nuna masa ta ji kunya. Nayla ta ce, "Allah ya baka ha uri Rouhii, ba kunya naji ba. Dariya ka bani da ka ce yaushe zan yi ciki." Ya harare ta ya ce, "ni zaki fa awa ba kunya ki ka ji ba? Wanne hali ne naki ban sani ba Jidda?." Ta sake yi murmushi ta ce, "Allah dariya ka bani." "Dole na baki dariya ai, ni ba wasa nake ba da gaske nake yaushe zaki yi ciki?. Yaushe zaki kar i ajiyar ana ko ata Jidda?. Ina so na ga kin haihu, kin ga nida Didi kawai iyayenmu suka haifa, abinda zan haifa da wanda zata haifa shine ahlin mu." Nayla ta karyar da kai tana kallonsa ta ce, "To YaMar samun ciki ai sai lokacin da Allah ya yi." Ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "haka ne....amma komai da niya ko?" Ya fa a yana bu e idanunsa yana kallon cikin nata ido. Ya bata kunya sosai, amma bata so ta nuna masa sai ta daure ta ce, "To na kusa." "Yauwa, ki da gagagwa kin ji? Yara nake so da yawa in Allah ya bani, kamar guda goma haka." Ta wara ido waje ta ce, "goma zaka haifa?." "Zaki haifa min dai." "Duk ni ka ai?." "A'a ni da ke." "Ka san wahalar haihuwa kuwa Rouhii?." "Ke kin sani ai, tunda kin haihu in" ya fa a yana kallon ta. Sai tayi dariya sosai shima kansa murmushi yake yi ta ce, "Goma fa da yawa, in na haihu goma ai na tashi aiki." "Baki tashi aiki ba, ai ni kika haifarwa kuma tare da ni zamu zauna." Nayla ta girgiza kai ta ce, "To YaMar Allah ya bamu masu albarka." "Amin Ashiq!. Zan yi arin ganin na baki ajiya ke kuma sai ki yi gaggawar kar a, in na mi o miki ki kar a a wannan karon kar ki i kin ji?." Nayla ta ce, "Me zan kar a?." "Cikin Mana." Ta rufe ido ta ce, "Allah ka bani kunya." Ya ta e baki ya ce, "to bani kayata." Ta bu e ido ta ce, "me?." "Kunyar mana, kin ce na baki kunya shine na ce ki dawo min da ita." Murmushi ta yi tana jan gashin fuskarsa a hankali ta ce, "Babu wanda zai ce kana magana haka, in aka ganka sai a auka baka da baki nan kuwa saura ka an ka kai parrot. Sai an zauna da kai ake fahimtar waye kai. Duk da a zama da kai in sai kaso a fahimta in, in baka so ba baza a gane ba. Duk da akwai ka da fa a da zare idanu, amma ka aro wani class shiyasa an mata suke maka layi." Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "kece an matan ai." "Don Allah ba a cewa ana sonka?." Ya kalli idanunta ya hango tsantsar kishinsa a ciki sai ya ce, "kema kin san matashi kamar ni ai dole a gani a yaba" ya fa a yana juya idanu kamar mace. Sai kuwa ta auke fuska zata bar jikinsa ya ri ota yana dariya ya ce, "wasa nake miki, ni bani da farin jini ai balle ace ana so." "Kai in? Kana kallon kan ka a madubi kuwa?." Ya kwaikwayi muryarta ya ce, "bana gani, ni ai kece madubina Jidda." Ta kwanta a jikinsa ta ce, "ni dai kar ka dinga kula su, kuma kar ka yi min kishiya, in ka yi min kishiya Allah mutuwa zan yi." Dariya ya sake yi ya ce, "Kina cemin yara goma sun yi miki yawa ba dole na fara tunanin wata ba." Da sauri ta kalle shi ta ce, "zan iya, ko ashirin ka ke so zan yi, amma kar ka ce zaka yi min kishiya aka ji" ta fa a zata fara kuka. Ya yi dariya ya ce, "wasa nake miki, kar ki yi min kuka, shagwaa iya sarkin kuka. Wasa nake yi, ki kwantar da hankalinki kin ji?." Kai ta aga kamar mara lafiya ta lafe a jikinsa tana sauraron bugun zuciyarsa, itama ta ta tana bugawa saboda kishinsa. KRB3P077 Nana haleema. A washe garin ranar kamar yadda ya ce suka ce aka yi international passport, a ranar aka yi aka basu, Nayla ta fa awa Abiy abinda ake so ya ce a tura masa visa page in Passport in. Kamar yadda ta fa a cikin kwanaki ka an aka samu visa ta fito, ya siyi ticket in ta tafiya duk da taimakon Nayla ake komai tunda itace ta saba.. Ana e gobe zai tafi da daddare ta ishe shi da rigima da shawaga a, sai rarrashinta yake yi duk ta ru a shi. Shi kansa sai ya ji tafiyar ta fita daga ransa, dan baya so ya yi nisa da ita kamar yadda bata so. Tana jikinsa tana jan numfashi a hankali alamun ta yi kuka ta gama, cikin sigar rarrashi ya ce, "in kina kukan nan ni ya ki ke so na yi? Tafiya zan yi fa, in na tafi ina tunanin na bar ki kina kuka bazan yi abinda ya kai ni ba. Sati uku kawai zan yi, kuma kinga biki za ku yi zaki ga lokacin ya yi saurin dawowa tunda kina cikin an uwanki." Nayla ta ago ta kalle shi suka ha a ido ya yi mata kiss a goshi yana shafa fuskarta a hankali, ta ora hannunta a fuskarsa tana shafa gashin fuskarsa ta ce, "Ni ba cikin an uwa nake so na zauna ba, tare da kai nake so na zauna Rouhii. Zan yi kewarka, sati uku fa da yawa, Zan yi sati uku babu kai" ta sake fa a hawaye na sakko mata. Omar cikin damuwa ya ce, "kukan ne bana son gani kin san da haka, ki kwantar da hankalinki zan dawo ai." Ganin ta i yin shiru sai ya sakata shirun ta dole dan kukan na ta yana tayar masa da hankali sosai. Ta yi matu arin bada gudunmawar da zata tsaya masa a rai ya dinga tunawa koda baya nan, ai kam ta yi nasara, dan ya ji yayi tafiyar ta fita daga ransa duk ya bi ya damu baya so ya tafi ya barta. Sai tattalinta yake yi, da ta motsa ya dinga tambayar me ya same ta ko me take so, a haka suka wayi gari. Da kanta ta yi breakfast duk fuskarta da damuwa, a haka suka ci tare yana sake rarrashinta amma ta kasa sakewa yadda yake so. Bayan sun kammala cin abincin ne ya ri e hannayenta yana kallon ta ya ce, "Ki yi ha uri ki kwantar da hankalinki, da na tafi zaki ga lokacin dawowata ya yi." Ta aga kai ta ce, "Allah ya kiyaye hanya." "Amin Ashiq. Ta so mu je ki taya ni ha a kayan kin ga lokacin tafiya ya kusa." Babu yadda ta iya tare suka ha a kayan dan jirgin arfe biyu zai hau. Karfe sha biyu na rana Didi ta zo gidan yi masa sallama, da ta shigo ya yi murmushi ya kar i Marmerh da tayi wayo sosai yana yi mata wasa tana dariya. Ya kalli Didi ya ce, "Gidanki nake niyar zuwa sai ga ki." Didi ta ce, "Dole na fito ai na yi maka sallama." Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Nayla, ya kalli Didi ya ce, "ki rarrasheta Didi, sai kuka take yi, kukan ne ni kuma bana so wallahi." Didi tayi murmushi ta ce, "To ai dole ta yi Omar, tafiya zaka yi har na sati uku fa, ta saba da kai dole ta damu." Ya kalli Nayla da ta sake rau-rau da ido, ya sake kallon Didi a tausashe ya ce, "Ya zaki dinga zuga ta Didi? Yanzu sai ta fara kuka." Didi ta ce, "yanzu zaka tafi?." Omar ya ce, "Sai na yi sallar azahar, zuwa arfe aya in sha Allah." Didi ta kalli Nayla da take tsaye har lokacin ta kalle shi ta ce, "Allah ya nuna mana lokacin." "Amin, Zan je wajansu Bashir na dawo." Didi ta ce, "to sai ka dawo." Ya kalli Nayla ya ce, "Don Allah ki daina aure fuskar nan ko kyau bakya yi" ya fa a da tsokana yana kallon ta. an kawar da kai tayi bai ce komai ba ya fita da Marmerh a hannunsa. Didi ta dinga rarrashin Nayla da kalamai masu da i har ta sake suka cigaba da hirar bikin Salma da Jawad. Ba jimawa ya dawo Marmerh tayi bacci a kafa arsa ya kwantar da ita ya shiga cikin aki. Nayla ta tashi ta bi bayansa ta samu ya shiga wanka ta dawo wajan Didi ta zauna. Ba jimawa ta sake komawa ta tarar ya shirya cikin ananun kaya wanda suka yi masa matukar kyau sosai. A tsaye ta tsaya a bayansa tana kallonsa shima yana kallonta ta madubi, a sanyaye ta tako ta araso inda yake ta rungume shi ta baya. Juyowa da ita ya yi ya ri eta ta gaba ya lumshe ido yana ji kamar ya tattara ta su tafi. Sun jima a haka a tsaye kafin ya ago fuskarta ya yi kissing lips inta na an mintina kafin ya kalli idonta ya ce, "Zan yi kewarki Ashiq!." Ta kalle shi ta ce, "Nima zan yi kewarka Rouhii! Zan yi kewar ka sosai." Cike da tsokana ya ce, "ki fa a min gaskiya ni zaki yi kewa ko aljanun dare?." Dariya ta yi ta ce, "Duka biyun." Ya an bu e ido ya ce, "Ki ce Jidda itama ta zama ar hannu, itama yanzu ta zama always available." Kwanciya ta yi a jikinsa cikin kunya, ya yi dariya ya shafa bayanta ya ago da ita daga jikinsa yana kallon ta.
Chapter 128 · 0% Book details