Sashe 33
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
he loves me zai kula dani da rayuwata sosai. Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, ki nutsu mu gama maganar nan, yanzu ke matar aure ce ki daina maganar Faruk, ki jira ya sake ki sai mu ga abinda za a yi. Kwanciya tayi jikin Mumta rufe ido a hankali har ta yi bacci. Mum zare ta tayi daga jikinta kwantar da ita suka fito zuwa falo su ukun. Najwa ta ce, Gaskiya Dad bai kamata a yale Ashraf ba, ya kamata a auki mataki a kan sa. Ka duba halin da ya saka ta a ciki. Mum ta ce, ya zama dole ya sake ta, kuma ka kira mahaifinsa ka sanar da shi abinda ya aikata. Dad ya ce, Tunda har mun zo mun auko ta duk magana ta are, zamu samu lokaci a nan dan ta huta tare da mu daga nan sai mu koma gida. In mun koma zan kira mahaifinsa domin ya saka ya sake ta. Mum ta ce, Hakan ya fi wallahi. Najwa ta ce, Yaya Nabil yana ta fa a, ya ce da ya san haka ne sai ya biyo mu. Dad ya ce, kar ku damu, ai komai ya are. Amma Dad ya batun Faruk in? Tana sonsa sosai, zaka amince mata ta aure shi?. Mum ta ce, kar na sake jin maganar nan a bakin ki, hauka ake yi an fa a miki ko wasan yara ake yi?. Dad ya ce, Najwa auren ta da Tiger ba abu ne da zai yu ba, beside shi ya ma yi auren sa, bana so a sake dawo da maganar nan. Itama zata manta da batun komai zai wuce. Mum ta ce, duk ba shine ya jawo komai ba? Da bai yi mata asiri ya shiga rayuwarta ba ai da duk ba haka ba. Wajan Narma Mum ta koma dan gani take yi kamar wani abun zai same ta. Nayla da Omar haka suka cigaba da zama irin yadda suka saba, babu magana mai arfi ganin sa ma sai tayi sa a tunda in ta fita bata dawowa sai yamma shi kuma baya shigowa sai dare. A haka su Hajja suka dawo, da yake shigowar dare suka yi washe gari da Nayla ta tashi saga aiki kai tsaye gidan Hajjan ta wuce. A nan ya tarar da su Mama Sa adatu sun zo barka da zuwa, ana ta ba i a gidan ana yi mata barka da dawowa. A nan tayi zaman ta ita da Salma suna hira har dare sannan ta koma gida da tsarabar ta harda ta Omar ma Hajja ta bayar. Da ta koma da Tk ta ha u shi ya shigar mata da motar ita kuma ta shiga cikin gidan da sallama. Abinda bata saba gani ba ta gani, shine a zaune a falo amma lissafi ya ke da alama kuma lissafin ya sha kansa sosai. Sallamar da ya amsa ma bai ago ba lissafi yake bugawa da wayarsa yana sake duba littafin da take tunanin a ciki yake rubuta komai. arasowa ta yi ta kalle shi ta ce, Ina yini. Bai kalle ta ba ya ce, lafiya. Daga nan ya auka zata yale shi ganin abinda yake yi sai bai sake cewa komai ba. Nayla ta ce, Na je gidan Hajja na yi mata barka da zuwa. Yayi mata banza bai ce komai ba, Nayla ta ce, ga sa o ta ce a baka. Bakya ganin abinda nake yi ne!? Lallai sai kin yi magana!? Ya fa a a fa ace yana kallonta. Nayla da ta firgita a sanyaye ta ce, yi ha uri, Hajja ce ta ce na baka ta fa a tana ajjiye masa ledar ta tashi ta koma ciki. Tsaki ya yi ko kallon ledar bai yi ba ya cigaba da abinda yake yi yana mita a zuciyarsa. Sai da ya gama ya lissafa ribar da aka samu daga fara aikin zuwa yanzu, da abubuwan da aka kashe, da wanda aka siya ya ga an samu riba fiye da tunaninsa. Ku in sun ninka sun sake ninkawa, domin kuwa tabbas sai ya fitar musu da zakka, babu abinda zai cewa Allah sai godiya domin kuwa lokaci ka ai ya kai inda bai yi tunanin zuwa ba. Ya kamata na samu Didi na ji abinda ya kamata ayi ya fa a a bayyane cikin tsananin jin da i, ko a mafarki bai auka zai mallaki abinda ya mallaka yanzu ba. Shiyasa yake arin kyautatawa ma aikatansa ko yaushe, shiyasa suke son aiki dashi dan bayan albashi haka kawai zai yi musu kyauta. A bayyane ya sake cewa, Zan tambaya naji ku in sun kai tsahon lokacin da za a fitar da zakka. Kallon abinda ta ajjiye ya yi kamar bazai auka ba sai kuma ya auka bai bu e ba ya tashi ya shiga aki zuciyarsa cike da farin ciki. Bayan Kwana biyu. Ranar ta kama rana asabar, Nayla tana gida babu aiki tana kwance a aki ciwon kai ya dameta. Mai aikinta ce tayi mata komai har tea ita ta dafa mata sannan ta tafi tunda ba kwana take yi ba. Bata san yana gidan ba har azahar ashe ranar bai fita ba yana cikin gida yana hutawa. Ta fito falo tana shan tea ta ganshi ya fito daga aki suka ha a ido. Tunda ya yi mata tsawa ranar da ra dawo daga gidan Hajja basu sake ha uwa ba sai yanzu. Nayla ta ce, Ina yini. A iya lalla ansa ya amsa, ba dan kallon sa take yi ba baza ta fahimci ya amsa ba. Fita ya yi bakin gate, lokacin rana ta bu e sosai har sai da ya kare fuskarsa da hannunsa saboda ranar, hango Didi yayi a cikin adaidaita sahu a zaune tana jiransa, ya araso inda take ya ce, wai baza ki shigo ba?. Didi ta ce, sauri nake yi, bani key in gidan mu Me zaki yi a ciki?. Didi ta ce, Yalla ai ne ya yi tafiya, ka san kuma yanayin unguwar ta mu bazan iya zama ni ka ai ba, shine ya ce na taho cikin gari in ya dawo sai na koma. Bani key in na tafi na tsayar da mai mota. Ai su Bashir ba a nan suke kwana ba ko? Na ji kwnaaki ka ce min sun daina zama a gidan. Wani irin kallo yake yi mata na ta ma raina masa hankali ya ce, wai kina nufin a can zaki dinga kwana?. Didi ta ce, eh mana. Omar ya harare ta ya ce, Meye amfanin nan da baza ki zo ba?. Didi ta wara ido da mamaki ta ce, Omar ni fa Yayarka ce ba anwa ba, kawai sai nazo gidan ka da ka ke zaune da matarka na zauna? Haba wannan ai bai dace ba. Ka bani key in naje na gide na zauna, in kuma baza ka bani ba na tafi gidan Hajja. Ya girgiza kai cike da jin haushi jin amsar da ta bashi ya ce, Oh! zaki iya zama a gidan Hajja, Hajjan da babu dangin uwa da uba amma baza ki iya zama a gidan da nake biyan ku in hayarsa ba ko?. Dariya Didi ta yi tana tunanin wannan wacce irin a Omar yake da ita, wato bazai ce gidansa ba sai dai gidan da yake biya ku in haya zai ce. Didi ta ce, Gaskiya bazan zauna ba, tunda muna da na mu gidan zan je can na zauna. Omar ya aure fuska yana girgiza kai ya ce, wallahi indai baki shiga gidan nan kin zauna ba bazan sake kwana a cikin sa ba har abada. Kin ji kuma na ce wallahi, babu wata halitta da ta ta a karya min rantsuwa a duniya. Kin san kuma zan iya yin abinda na ce, amma in kina ganin bazan iya ba ki tafi Didi ya fa a yana bar wajan. Didi ta ce, Innalillahi wa inna ilahir raji un! Wannan wanne irin yaro Allah ya ha a ni dashi?. Hajiya sauri nake yi ki sallame ni mai adaidiata sahun ya fa a yana kallonta. Didi ta ce, yi ha ta fa a tana auko ku i ta bashi ta fito daga ciki ta rasa mafita. Allah ya sani bata son kwana a gidan dan gani take yi zata takurawa Nayla ita kuma bata son faruwar hakan. Matsayin uwa take a wajansa, haka kawai sai ta shiga gidansa ta ce zata kwana bayan tana da inda zata iya kwana?. In kuma bata shiga ba tunda ya ce ya daina kwana a gidan wallahi ya daina, ta san halin kayanta in and out, ita kuma so take aurensa da Nayla ya daidaita, in bata shiga ba yadda ya rantse ya kenan?. Ajiyar zuciya tayi ta auki aramar jakarta ta arasa bakin gate in. Ashe yana tsaye daga ciki yana kallonta, iris yake jira ta tafi ya shiga ya tattaro kayansa dan bazata karya masa rantsuwa ba. Kafin ta arasa sai gani tayi ya bu e mata gate in tare da kar ar jakar hannunta dan cikin jikinta ya fito sosai. Harararsa ta yi ta ce, Wallahi ka cika rigima, ina ni ina zama a gidan nan don girman Allah? Wannan arfa- arfa da me tayi kama?. Wato a nan ka ja tunga kana jiran tsammani ko?. Shi dai bai kula ta har cikin falon. Nayla tana tsaye a Inda take har lokacin tana goge dining glass Jin muryar Didi ya saka ta juyo ta ce, Didi! sannu da zuwa ta fa a da fara a tana takowa tazo inda Didin take. Didi ta bi ta da kallo ta ce, Nayla baki da lafiya ne?. Nayla ta yi murmushi ta ce, Eh Didi, ciwon kai ne yake damuna sosai. Ga fuskarki nan har ta an kumbura kamar wacce ta yi kuka. To ki je asibiti mana wannan ciwon kai yan damun ki. Ranar Monday kafin na tafi aiki zan biya in sha Allah. Sannu da zuwa. Didi ta ce, Yauwa Nayla, Zauna kar jiri ya auke ki. Nayla ta zauna kusa da Didi ta ce, Sannu da zuwa Didi. Didi ta amsa ta kalli Omar da yake tsaye ta ce, Bata da lafiya shine baka fa a min ba?. Kallon Didin ya yi ba tare da tunanin komai ba ya