← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 205

Sashe 116

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai jima ba ya tashi ya kashe hasken akin ya kwanta bai kalle inda ta ke ba. Yana jin duk motsinta da kukan da take yi ya bai saurareta ba duk da tarin kewarta da ya yi. Itama ganin yana share ta ba tare da ta san laifin da ta yi masa ba sai ta daure ta yi baccin ta bata sake ce masa komai ba. A haka ta yi bacci cike da takura shima haka. Ko da asuba daga gaisuwa ya amsa mata da yar bai kuma yi mata magana ba sai ta shiga damuwa amma ta yi arin oyewa. Washe gari asabar, abincin da ta dafa masa a daren jiya sai zubarwa tayi dan ya lalace, tana so ta dafa wani tana tsoron kar ya i ci a sake yin asara. Sai ta dafa tea da abincin ka an yadda ko bai ci ba zata iya cinyewa. Bai ma fito falon ba gaba aya, yana ciki aki yana aiki ba tare da ya neme ta ba. Ganin bai fito ba ya saka ta shiga akin da sallama ya amsa a ciki. arasa ta zauna tana ri e da mug in tea ta ce, "Ga tea." Zata ajjiye ya ce, " auke kayan ki, ai ban ce ina so ba ko?." Nayla ta bishi da kallo ce, "wai me nayi maka haka don Allah? Ka fa a min abinda nayi maka sai na baka ha uri. Tun a Kaduna bani da kwanciyar hankali ka aukar wayata, nayi messsage ka i ka yi reply. Haka kawai ka fara fushi dani ba tare da na san laifina ba? At least kafin ka fara fushin ya kamata ace na san laifin da na yi maka, ban san me nayi ba ka daina aukar wayata, na dawo ka i kula ni kuma baka ce min ga kuskuren da na yi ba" ta fa a cike da jin haushi tana kallonsa. Yana jin abinda take fa a yana mamaki, sai ya fa a mata ma zata gane kuskuren ta kenan. Ya girgiza kai ya ce, "in kika cigaba da yin magana ba tare da na baki izini ba sai na watsa miki tea in nan!. Ki auke kayan ki bana sha!." Ya sake fa a ba tare da ya kalle ta ba. Ajjiye masa tayi a gabansa ta ce, "duk da ban san abinda na yi ba, ka yi ha uri." an ture mug in ya yi ya an ta a hannunta, ta auke da sauri tana yarfe hannu tare furta, "Washhh!." Da hanzari ya ri e hannun yana cewa, " onewa ki ka yi? Na gani, amma babu zafi ko?" Ya fa a a tare yana kallon ta ya manta ma fushi yake da ita. Ganin ta samu kansa sai ta fashe da kukan shagwa a, sai lokacin ya kula ya kwafsa ya saki hannun nata ya koma ya zauna yana jinta tana kuka bai ce komai ba. Mamaki take yi ganin ya share ta kamar ba shine in tana kuka yake damuwa ba, ta sake ara volume in kukan nata sai ta ga yana dube-dube a aljihunsa. Abinda ya auko ya bata mamaki ta har ta bu e baki tana kallon sa, ya ma ala AirPort a kunnensa alamun ta cigaba da kukan shi baya jin ta. Nayla ta bishi da kallon mamaki tana kuka. Gajiya tayi da shariyar tasa ta taso ta dawo jikinsa ta zauna ta kwantar da kanta a irjinsa tana kuka mai sauti wanda yake ratsa kunnensa har zuciyarsa dan babu abinda yake ji. Gajiya ya yi da jin kukan nata, a hankali ya cire abinda ya saka a kunnensa ya ce, "to ya isa haka, kukan ya isa ki bari." Numfashi take ja ta ce, "ban san me nayi maka ba ka ke fushi dani." "Jiya da ki ka dawo kin kira gida kin ce musu kin sauka lafiya kuwa?." Nayla ta aga kai ta ce, "tun kafin na shigo gidan nan ma na kirasu saboda kar na manta." Murmushin takaici ya yi kafin ya ha e rai matu a cikin kaushi ya ce, "ni ne wanda ki ka raina da ki ka kasa kirana ki ce min kin sauka lafiya ko? Ni da yake na damu dake da na kira ki sai ki ka auka, kuma baki tashi kirana ba sai dare. Ni ne wanda bashi da mahaimnaci a rayuwarki, baki damu da ki fa a min kin sauka lafiya ba, ko ya na kai ga son sanin ya kika sauka ke bai dame ki ba." Sai a lokacin ta fahimci dalilin fushin nasa, zata yi magana ya ce, "kar ki ce min komai, tashi ki bani waje." Zata sake magana ya bu e idanu ya ce, "na ce ki tashi!." A firgice ta mi e daga jikinsa ta ja ta tsaya ba tare da ta fita ba, dan yanzu ba ko yaushe fa ansa yake bata tsoro ba, amma yanzu kam a tsorace take tana oye tsoron ne kawai. Shi kam bai kalle ta ba ya mi e ya shiga ban aki. KRB3P069 Nayla jiki a sanyaye take a tsaye har ya fito tana kallonsa, tana so ta fa a masa uzurinta amma ya i bata wannan damar. Kallonsa ta tsaya yi tana matsar walla, tana so tayi masa magana tana tsoron kar ya yi mata tsawar da bata so. Shi ma yana kallon ta hankalinsa yana kanta, amma baya so ya nuna mata ya yi kewarta sai ta fahimci kuskuren da yake ganin ta yi masa. Inda ya biyewa zuciyarsa da yanzu ya kar i ha urinta saboda bugawar da zuciyarsa take yi. Allah ya ora masa aunarta a lokacin da bai shirya ba, zuciyarsa bata ta a bugawa akan komai ba sai a kanta. iris ya rage ya kasa jurewa share ta in da yake yi, shiyaasa ya ke so ta fita ta bashi waje amma ta Ganin ta i fita ta ja ta tsaya tana masa kukan shagwa a sai ya tashi ya auki wayarsa ya fita ya bar mata gidan gaba aya ko tea in da ta ajjiye bai sha ba. Nayla ta bishi da kallo har ya fice tana hararar bayansa ta ce, "mutum sai masifa, ya tsaya ya ji uzurina ma bazai tsaya ba" ta fa a tana fita daga akin. (Lallai Nayla kin waye aki ta koma ta zauna ba tare da tana yin komai ba, sai ta gaji da zaman sannan ta taso ta dawo falo duk zaman gidan ya isheta. Salma ta yiwa waya ta ce don Allah ta zo, Salma ta ce mata tana gidan Daddy bata gidan Hajja. Kamar ta kurma ihu haka take ji, tunda suka fara shiri ana soyayya bai ta a fushi da ita kamar haka ba shiyasa duk ta damu. Kamar wasa ta ji ana buga gate in gidan ta taso ta bu e. Ganin Didi ya saka ta fa awa jikinta kawai ta fashe da kuka. Didi ta shigo ta rufe gate in tana cewa, "Nayla lafiya? Me ya same ki?." Nayla bata iya magana ba suka shiga ciki Didi ta zauna ta ce, "Lafiya ki ke kuka Nayla? Wani abu ya faru ne?." Nayla cikin kuka ta ce, "Didi YaMar ne." Didi ta sauke Marmerh da take bayan ta tana bacci, ta kwantar da ita a gefe ta kalli Nayla ta ce, "meya samu Omar in?." Nayla ta ce, "Fushi yake tayi dani" ta fa a tana sake fashewa da kuka. Didi ta saki baki tana kallon Nayla cike da mamaki da kuma takaici, sai kuma ta yi dariya tare da yin tsaki ta ce, "Fushin Omar in ki ke yiwa kuka?." "Didi daga Kaduna na dawo jiya amma ko kallona bai yi ba, na rasa me nayi masa tun a can Kaduna baya aukar wayata, in na kira shi da wata number da ya ji nice zai kashe. Ashe fushi yake yi dana sauka ban kira shi na ce na sauka lafiya ba, kuma ya kira ni ban auka ba. Allah yana gani ban ji kiransa ba, kuma bacci na yi shiyasa ban kira shi ba." Didi ta bita da kallon takaici ta ce, "har yanzu wai baki rage tsoron Omar a ranki ba Nayla? Mijinki ne fa, in baki sake dashi ba da wa zaki sake?. Kuma na fa a miki tsoron nan nasa da ki ke nunawa nan gaba zai cutar dake wallahi, saboda zai dinga juya ki yadda yake so saboda ya san kina tsoronsa duk abinda ya ce zaki yi. Ban ce kar ki ji tsoronsa ba, ban ce kar ki yi abinda ya ce ba, amma ki dinga ja baya, wani abun ki daina nuna kin damu ko fushinsa yana gabanki, in ba haka ba zaki yi dana sani Nayla." Nayla ta ce, "na rage tsoronsa Didi, ni kaina na san yanzu bana tsoronsa kamar dah. Kawai na damu ne da yake fushi dani shiyasa." Didi ta ce, "ba sai ki bashi ha uri ba?." "Na bashi ya i ya ha ura, sai share ni yake yi." "Kema sai ki share shi, tunda kin bashi ha uri ba sai ki yale shi ya araci ba in halinsa ba?." Nayla ta langwa ar da kai ta ce, "Didi amma ai laifina ne." Didi ta yi dariya ta dafa Nayla ta ce, "ke kika san ta yadda zaki bashi ha uri ya ha ura, to meye na wannan kukan don Allah?." Nayla a sanyaye ta ce, "Didi tsawa fa yake yi min, ni na manta rabon da ya daina min magana balle tsawa." "Shiyasa na ce fushin Omar har kuka zai saka ki? Daman shi ba ka yi masa komai ba fushi yake yi balle kin yi masa. Fushinsa ya daina tayar miki da hankali daman halinsa ne. In yayi ki barshi ya araci uncinsa zai dawo kan hanya." Nayla ta goge ido ta ce, "Inaso dai ya ha ura Didi, ki bashi ha uri don Allah. Kuma ba sa yin aiki ranar asabar sai yamma, amma ya fita ya bar ni." Didi ta yi dariya tana mamakin shagwa ar Nayla ta ce, "babu ruwana, bazan bashi ha uri ba ke zaki bashi ha uri." "To ya i ya ha ura." "Ke kin san ta yadda zaki saka shi ya ha ura, kin san
Chapter 116 · 0% Book details