← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 205

Sashe 144

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

na fa a maka lokacin aukar fansa ta ya zo, lokacin da zan saka cikin jikin matarka ya bi rariya yazo, lokacin da zan saka maka ciwo a zuciyarka ya zo. Na jima ina dakon wannan rana, shekarun da na ata ina jiran wannan rana basu tafi a banza ba. Ko ta wuya ko ta arzu i sai na zama silar zubewar cikin jikinta, ina so ka ana ka an daga cikin abinda na ana a shekarun baya. Omar ya yi murmushi yana kallonsa, cikin dakiya da son oye ru aninsa ya ce, da bakin ka ka ce Damisa yana nan da halinsa, ka tabbatar da halina yana nan babu inda yaje. Amma saboda ganganci ni ka kake fa awa wannan maganar?. Zan kuma sake maimaita maka, sai na zama silar zubewar cikin jikinta, yadda baka bar nawa ya rayu ba nata ma bazai rayu ba wallahi. Nayi kwantan auna ne ina jiran wannan lokaci, gashi kuma yazo. Ka jira ka gani ya fa a yana hawa machine insa zai tafi Omar ya ce, In ka fasa baka aunar Allah. aura ya yi dariya ya ce, mu zuba ya fa a yana barin ofar gidan. Omar ya kalli su Bashir da suke nesa dasu, ganin ya tafi suka araso wajan, Bashir ya ce, Boss akwai matsala ne?. Omar ya ce, daman yana cikin garin nan?. Bashir ya ce, aura yana nan, wani lokacin kamar yayi wani hankali, wani lokacin ya sake lalacewa. Omar ya auke kai baice komai ba amma maganar ta daki zuciyarsa sosai, ya san waye aura farin sani, ya tabbatar tunda ya fa a sai ya aikata. Ya sauke numfashi ya aiki Tk ya siyo sa on Nayla yana tsaye ya kawo masa ya shiga gidan. Duk yadda yake jin zuciyarsa da rauni haka ya dake ya share maganar ya shiga kamar ba shi ba. Da kansa ya bata abinda ta ce ya siyo mata duk da apple in kawai ta ci. Da kansa ya canja mata kaya zuwa na bacci ya kwantar da ita a jikinsa. Ya saka hannu a rigarta yana shafa asan cikin ta kamar yadda ya saba ko yaushe. A haka Nayla ta yi bacci. Shi kuwa Omar ya kasa baccin, tunani yake yi kar a cutar masa da Nayla da unborn. Ya san waye wanda ya furta, tunda yace wallahi sai ya yi shiyasa yake jin maganar har zuciyarsa. Da yar bacci arawo ya sake shi, da ya motsa maganar ce take fa o masa. Razananniyar azaba ce ta farkar dashi daga bacci, ya tashi a firgice jin zafi da ra i ta ko ina a jikinsa. Yana bu e ido ya ga mutane sama da goma a kansa ko wanne da makami a hannunsa. Hannunsa ya kalla a na yaga aton saran da aka yi masa jini yana zuba sosai. Da gaggawa ya kalli Inda Nayla take ya ga bata nan, kallon akin yake yi a fircice ya hango ta a hannun maza guda biyu ko wanne ya ri e hannunta sun tala hannunta kamar zasu tsinka. Zabura ya yi zai sakko daga kan gadon ya ce, Dukan da aka yi masa a kansa ya saka ya koma ya zauna yana ganin biyu-biyu idanunsa suna kullewa saboda nauyi da azabar da take ratsa cikin walwarsa. aura yana kallom Omar ya ce, Ba na fa a maka ba? Daman ba nace maka sai na salwantar da cikin jikinta ba? Gani ka ke arya nake ko?. Bara ka gani, a kan idonka zan zubar da cikin sannan kuma na kashe ta, na kar o aikin aukar fansa a kan ka da yawa, kowa ya ce na kashe ta, kowa yace kashe ta shine ka ai fansar da za a auka a kanka wacce zata yi maka ciwo da ra i a zuciyar ka, tunda sun biya da ku i mai ni zan kashe ta in. Sai naga in zaka iya hana ni, in ka isa ka nuna min kai Damisa ne ka tashi ka hana ni! Ya fa a yana kallon Omar da idanunsa suke lumshewa saboda nauyin kai. Nayla kuka take yi sosai jikin ta yana rawa tana cewa, YaMar ka taimaka min, YaMar zasu kashe ni, YaMar zasu kashe maka ni!. Wanda suke ri e da ita aya ya tsinka mata mari ya ce, tunda ki ka aure shi ai kin san me kika aura, zaki ba unci lahira a yau in nan! Zaki biya bashin da mijinki ya ci yaci kafin ya aure ki. Ba tare da ata lokaci ba aka fito da atuwar wu a siriri mai kaifi, a lokacin Omar gab yake da suma saboda yadda kansa ya yi nauyi ga azabar da take ratsa ko ina a jikinsa. ago mana da kansa, dan ya shaida an kasheta. Ina so in ya farfa o ya ji ra i da ciwo a zuciyarsa. Suka ago da kan Omar a lokacin da ya nufi Nayla kai tsaye da niyar kashe ta. aura yana zuwa ya kar i wu ar ba tare da tausayi ko imani ba ya aga wu ar zai soka mata a ciki. Wani irin numfashi Nayla ta ja ta sauke, a daidai laokcin da Omar ya ce, Jiddaaaaa!. KRB3P087 Nana Haleema.
Chapter 144 · 0% Book details