Sashe 32
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya fa a yana yanke wayar. Narma ta kalle shi bayan ya yanke wayar ta auke kai bata ce komai ba, ko murnar zuwan iyayen nata ma bata ji ba dan a ganin ta duk su suka saka ta a cikin wannan hali da take ciki. Da sun amince ta auri wanda take so duk da ba haka ba ai. Ashraf bai nuna ya wani damu sosai ya turawa Dad location in inda suke. Ya juyo ya kalle ta ya ce, Ko da su Dad sun zo babu wanda ya isa ya raba ni dake wallahi, sai na gama fanshe wahalar da ki ka bani kafin na rabu dake ki je ki auri an daba. Narma bata ce komai ba ta auke kai dan gaba aya yanzu ta zama shiru-shiru, duk rashin kunyar nan da take ji da ita ta gudu. Kusan mintina ashirin da tura musu location in aka fara danna door bell, Ashraf ya mi e ya bu e suka fara ha a ido da Mum. Kallon da take yi masa ya saka ya auke kai daga kallon ta, Dad ya yi hugging insa ya ce, Ashraf mun zo babu notice ko?. Babu komai Dad, ku shigo. Shiga suka yi falon Narma na zaune a kan kujera ko motsawa ma bata yi ba. Mum ce ta kalle ta ta kalli Dad da shima ya kalleta ta ce, Narma baki gan mu ba ne?. Kallon su tayi ta sake auke kai bata ce komai ba. Dad ya wara idanu ya ce, Narma me yake damunki? Kin yi rashin Lafiya ne?. A guje suka taho inda take kawai sai ta fashe da kuka. Dad ya zauna a gefen ta Mum ma haka, suka sakata a tsakiya suna tambayarta abinda ya same ta. Bata ce komai ba kuka kawai take yi Mum ta kalli Ashafe ta ce, Asharaf me yake damunta ne? Me ka ke yi mata da ta koma haka duk ta rame uhum?. Meyasa ko yaushe ba a samun ta a waya?. Ashraf ya ce, Mum ta samu miscarriege ne fa. Dad da mamaki ya ce, miscarriege! Yanzu Ashraf miscarriege ta samu baka kira ka sanar da mu ba? Meyasa ka oye mana?. Mum kallon Narma take yi ta ri e hannunta ta ce, yaushe hakan ya faru?. Ashraf ya ce, Dad na so na sanar da ku itace ta ce bata so na fa a mu ku kar hankalin ku ya tashi. Dad ya kalle ta ya dafa kanta sai ya ce, har yanzu jikinta da zafi sosai. Narma cikin kuka ta ce, Dad kun raba ni da Faruk in, kun aura min wannan. Na tsane shi bana sonsa na gaji da zama dashi. Kuma ba miscarriege na samu ba, he aborted my baby! Ta fa a tana hawaye. Mum a razane ta ce, What! Abortion?. Narma ta ce, Yes Mum, da kansa ya saka aka cire cikin ya ce he s not ready to be a father shiyasa ya zubar da cikin. Ya mayar da ni s*x machine, always on it. Ya wace wayata, ya canja mana estate, ya canja password na ofa saboda kar na fita. Rayuwa nake kamar a prison, na gaji! ta fa a tana kwanciya a jikin Mum tana kuka. Mum ta kalli Ashraf da yake zaune ya wani basar kamar ba laifinsa ake fa a ba, ta kalli Dad da yake kallon Ashraf in shima cikin unar rai. Mum ta ce, na fa a maka daman jikina yana bani Narma tana cikin matsala ka ce min ba haka ba. Kana ji ai yanzu, har zubar mata da ciki ya saka anyi, baiwa aka kawo masa ko kuma sonta ne baya yi?. Dad ya kalli Ashraf cikin acin rai ya ce, Ashraf duk abinda ta fa a kana aikatawa?. Asharaf cikin rashin damuwa ya ce, Dad har yaushe muka yi auren da za a ce an samu ciki? Ni ban shiryawa hakan ba shiyasa aka zubar da cikin. Kuma da take zancen na mayar da ita s*x machine, to dan me na aure ta?. Mum ta bu e baki tana kallonsa jin da yadda yake magana, ta kalli Dad da shima shi yake kallo cikin tsananin takaici da mamaki. Dad ya ce, Ashraf sakamakon aunar da na nuna maka kenan? Sakamakon yarda da amince maka da nayi na baka amanar ata kenan? Yanzu abinda zaka saka min dashi kenan ko?. Ka ajjiye min yarinya kana wahalar da ita shine daidai a wajan ka?. Ashraf ya ce, Dad ni ban wahalar da ita, itace take wahalar da rayuwarta. Kuma ko yaushe cikin yi min zancen wancan banzan an daban take yi, ta kalle ni ta ce ta tsane ni shi take so ba dole raina ya aci ba. Narma ta sake kallonsa ta ce, na tsane ka, bana sonka Omar nake so. Kuma Allah ya isa virginity ina, Allah ya isa babyna da ka zubar min. Ka jira sai na yi shari a da kai!. A firgice ya taso yazo inda take, ba zato ba tsammani suka ga ya tsinke ta da mari ya ce, ko wacce irin shari a zaki yi dani baki isa na sake ki ba, ban gama amfanar jikinki ba, ki bari duk sanda na gama sai na Marin da ya sauka a fuskarsa ya hana shi arasawa. Ya juyo ya kalli Dad da yake wuci cikin acin rai ya sake marinsa. Kafin ya dawo daidai Mum ma ta mare shi a aya angaren cikin tsananin tasafar zuciya. Kallon su yake yi su duka biyun cikin mamakin da ya hana shi magana. Dad y ce, Ashe baka da mutunci ban sani ba? Ashe baka da tarbiyya?. A gabana ka ke aga hannu ka mari Narma? Har kana cewa baka gama amfani da jikinta ba?. Ashraf ya ce, Dad Narma itace mara tarbiyya ba ni ba, bata girmaman ni a matsayina na mijinta, shiyasa raina yake aci ko yaushe. Mum ta kalle shi da dan ita ta kasa magana, takaici da ba in ciki sun yi mata yawan da ta kasa bu e bakinta tayi magana. Narma ta ce, ba yau ya fara mari na ba Dad ya saba, ya mayar dani kamar slive insa ko yaushe abinda yake so yake yi. Dad ya ce, Tunda abin naka haka ne ka sake ta yanzu, auren ya are gaba aya ai babu dole. Ashraf ya kawar da kai gefe ya ce, ni bazan iya sakin ta ba, kuma babu wanda zai saka na sake ta. Mum zata yi magana Dad ya hana ta ya kalli Narma ya ce, Ina passport inki?. Narma ta ce, yana wajan shi. Ya kalle shi ya ce, auko min passport inta. Ashraf ya ce, bazai yu na auko ba, haka kawai ku zo ku auke min mata ba, bazan iya aukowa ba. Dad ji yake kamar ya dinga dukan Ashraf har sai ya fitar masa da jini. Ya danne zuciyarsa ya ce, Ashraf in baka auko min passport in nan ba sai nayi reporting inka a asar nan bisa cin zarafin ata da ka ke yi. Ya san Dad zai iya, kuma in hakan ya faru abin bazai yi kyau ba dan a asar America yake ba a nigeria ba, tsaf zasu aure shi bayan tara da zasu saka ya biya. Hakan ya saka ya shiga ya auko ya mi a masa har wayar Narma. Dad ya kalli Najwa da ta kasa magana ya ce, auko abinda ki ka san nata ne ku zo mu wuce. Ashraf yana ji yana gani aka ha a trolly bag in Narma suka ri e hannun arsu suka fita da ita. Da kallo ya bisu yana girgiza kai cikin takaici da ba in ciki, dan yayi alwashin bazai sake ta ba sai ya gama morar surarta yadda yake so, sai ya gama lalata komai babu abinda zai rage mata wanda zata cigaba da bayyanawa har wasu mazan su shiga irin halin da ya shiga lokacin da suke soyayya, sai ya tabbatar da ya gama lalata komai nata sannan hankalinsa zai kwanta. KRB3P016 ArewaBooks@nanahaleema11. Tunda suka koma hotel in da suka sauka babu wanda ya iya cewa komai. Mum tana zaune kusa da Narma an ha a mata tea tana bata a baki, duk suna zaune kowa ya zuba mata ido cikin tausayi da soyayya. Sai da ta shanye tea in sannan ta kalli Najwa ta ce, kin auko maganinta?. Najwa ta amsa da eh ta bawa Mum maganin nata ta bata ta sha. A kafa ar Mum ta kwantar da ita tana shafa kanta a hankali. Mum ta ce, ki yi ha uri Daughter, ba mu san rayuwar da ki ke yi a wajan Ashraf ba kenan, mun auka rayuwar soyayya ce ashe wahala yake baki. Ki yi ha uri. Narma ta ce, ai na ce muku bana sonsa tun farko amma ku ka i saurarena, aka aura min shi ba tare da yarda ta ba, aka turo ni nan ba tare da na amince ba. Ni gaba aya ba a kyauta min ba, an lalata min rayuwa gabadaya Mum. Dad ya ce, ki yi ha uri my love, bamu auka haka abin zai zama ba, mun turo ki nan saboda ki samu peace of mind ba mu auka haka lamarin zai lalace ba. Muna ganin Ashraf yana sonki shiyasa mu ka ha a ki dashi, a ganin mu zai baki fari mai yawa. Ashraf baya sona Dad, baya sona. Ya fa a min da kansa, satisfying lust insa kawai ya ke yi kaina. Ba sona yake yi ba, ya aure ni ne saboda ban bashi goyan bayan abinda yake so kafin ya aure ni ba shiyasa kawai. Dad ya ri e hannunta ya ce, calm down, muna tare dake a yanzu babu abinda zai sake faruwa dake. Za a raba auren tunda haka abin ya zama. Narma ta mi e zaune ta ce, Da gaske zaka raba auren Dad?. Da gaske nake Narma, za a raba auren ko da baya so. Zaka bar ni na auri Faruk?. Dad ya kalli Mum da take kallonsa ta ri o Narma jikinta ta ce, Ki nutsu mu koma gida sai mu yi wannan maganar. Za ku yarda ya aure ni? I love him so much, da shi na aura bazai min haka ba,