Sashe 3
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi abinda zan cutar da kai ba Omar, duk abinda zai zamar maka alkhairi shi nake nema maka a rayuwa. Kai ya ke girgizawa ya kalli idanunta da nasa idanun da suka yi ja sosai ya ce, ji nake a zuciyata meyasa ma ban amince na warware auren nan ba? Didi dan ina girmama ki sai ki dinga yi kin dole? Ba fa haifata ki ka yi ba. Dan na amince na rabu da ke ai ba uwata ba ce ba, meyasa ma na saurare ki har na amsawa iyayenta na kar i auren?. Jin yadda kalaman sa suke fita ta san ya rasa control ne, ransa a ace yake sosai. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, ka tsaya ka saurare Dukan ofar ya sake yi ya ce, bazan saurare ki ba! Bazan saurare ki Didi, na gama sauraren ki akan wannan maganar!. Sai da gaban Didi ya fa i ta firgita, bata ta a ganinsa a acin rai kamar na yau, ko akan abinda ya faru da Narma bata ga ya shiga wannan yanayi ba. Ta an ja da baya kar ya maketa ta ce, Omar Ina sonka, bazan yi maka abinda zai cutar da mai ba. Ban saka ka kar i auren nan saboda na ata maka ba, na saka ka kar a ne saboda Wata irin zabura yayi ya zo daf da ita ya ce, saboda ki faranta min? Kina so ki ce kin saka kar a ne saboda ki faran ta min rai Didi? Ya girgiza kai ya ce, Auren nan bazai ta a faranta min ta rai, kin ha a kan ki da mi iyina a duniya kin aurar dani kamar wani ar tsanar roba. Yanzu zasu dinga ji a zuciyarsu sun zama kamar dole a rayuwata saboda su suka kar i aurena. Kuma wai kin san maganar amma ki ka yi min shiru, har ki ke cemin kar na baki kunya ashe akan wannan ne. Wallahil azim baki kyauta min ba, in na ce bana jin haushin ki arya nake yi, in ba dan ke in ba ce wallahi ko wacece yanzu tana gadon asibiti in ma ban zama silar barinta duniya ba. Amma kema in ma ki yi baya-baya a yanzu, yadda nake jin zuciyata wallahi zan iya sha e ki. Didi bata ta a jin tsoronsa ya shiga ranta kamar yau ba, yadda yake hayayya o mata lamarin ya firgita ta sosai. Ta dake bata nuna masa ba, ta ri o hannunsa ta ce, Ka tsaya ka saurare ni. Yanzu ka auka ni ce a matsayin Nayla, aka aurawa wani ni kamar yadda aka aura maka, zaka ji da i ace sake ni daga aura aure da kwana bakwai kawai?. Gwara ace auren ya mutu yanzu akan ace ya jima. Ai wallahi in kece sai an raba auren, babu wani a duniya da zai aurar dake ba da sanina ba kuma na amince ki cigaba da aurensa. To in ma wai kina yi min misali da kan ki ne dan ki saka min wani tunani ki daina, dan kina sake tunzura ni ya fa a tana janye hannu ta daga jikinsa dan wallahi haushi take bashi. Yarinyar nan itace wacce ta shiga ta fita aka kar o ka daga wajan Sen, ba dan ita ba da wata ila har yanzu kana can a hannunsu. Wanne irin karamci ne mahaifinta bai yi mana ba da muka je? Wanne irin tarba ce bamu samu daga gare shi ba ehe?. Da aka zo aurena a gidan kakarta aka yi komai, daga arshe ma kakarta ce tayi min kayan aki. Meyasa zamu saka musu ta hanyar sakin arsu Omar?. Kana da halin da zaka ri eta a yanzu, in da Omar in baya ne da bashi da aikin yi nima wallahi bazan amince ba, saboda na san baza ka iya ri e aure ba, amma Omar in yanzu daban ya ke da na dah. Ka ji matsalar, har an fara yi min gorin ba ni ne nayi miki kayan aki ba wata bare ce a gefe. Inda ni nayi ai baza ki kalle ni kina fa a min wannan har ki kafa hujja dashi ba. Kuma da ki ke zancen ita ta shiga ta fita aka kar o ni daga Abuja ni na saka ta? Na je na ce tayi min ne Didi?. Ba kai ka ro a ba ni na ro a, dan haka in na ro a abu kamar ka ro a ne. Banza ya yi mata ya juya mata baya yana jan numfashi. Didi ta ce, Auren nan itama ba a son ranta ya faru ba, babu wanda ya san dalilin mahaifinta na aura mata kai a aramin lokaci, Meyasa baza ka fahimta ba?. Jiyowa ya yi yana kallon ta ya ce, meye ma sunan garin su?. Kaduna. Daga Kaduna kawai ya auko afa ya zo Kano, da kuma yazo Kanon sai ya rasa inda zai je sai gida wa ancan munafukan mutanen nan, kuma kaf an da suke dasu ya rasa da wa za a aurawa arsa aure sai da ni. Fa a min in ba shirya abin nan aka yi ba me aka yi? Haka kawai zuciyarsa zata fa a masa ya aura mata Omar ne?, Na san arsa ne?, Ko na ta a zuwa gidan su nace Ina sonta?, Ko kuma magana mai arfi ta ta a shiga tsakanina da ita ne?. Amsa min Didi. Didi ta ce, addarar aurenku ce ta kawo hakan, kuma shi yayi haka ne saboda dalilinsa wanda bamu sani ba, wata ila hukunci ya ke yiwa arsa. Ya wara hannaye tare da har e su a irji y ce, Ni kuma gani mai ba in halin duniya wanda dani ka ai za a ha ata ya zama mummunan hukunci a rayuwarta ko Didi?. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, mun gama maganar nan da kai, Zaka ri e aurenta babu saki koda mahaifinta ne ya ce ka sake ta kar ka saketa, ka ri eta a hankali komai zai canja. Hmmm! Shine abinda ya ce kenan yana kawar da kansa gefe cikin matu ar takaici. Didi ta ce, Yanzu ka auko rigar ka da ka jefar, ka saka hular ka kazo mu je gidan da zaku tare kai da amar kallon da ya yi mata shine ya hanata arasawa. Ya ce, arasa mana Didi, Ina jinki. Omar Yayarka ce ni fa, ka dinga sanin irin abinda zaka yi min. Ai ina gab da daina kallon ki matsayin yayar tawa, dan babu abinda zaki sake saka ni nayi kuma a yanzu. Didi a raunane ta ce, ni dai don girman Allah ka saka kayanka mu je gidan da aka kai amaryarka, don Allah ka zo mu je kar ka ce min baza ka je ba. Au ni ne ma zan bita wani gida ba ma ita zata zo ba ko?. To bara kiji, na rantse da girman Allah baza ni ba, gwara na yi miki kankat ki ji, wallahi babu inda zan je. Ajiyar zuciya Didi tayi cikin damuwa, tunda har ya rantse ta san bazai je ba wallahi sai ta shiga damuwa fiye da wacce take ciki. Ta kalle shi ta ce, shikenan, naji baza ka je yanzu ba, amma in anjima sai mu je zan zauna har lokacin mu je tare. Kallon banza yayi mata dan bazai amsa ba, ya share ta ya cigaba da abinda yake yi. Omar in baka je yau ba babu da i, amarya ce fa Omar, amarya fa. Tunda ka rantse ka ce baza kaje yanzu ba, zan zauna na jiraka har zuwa anjima sai mu je ta sake fa a kamar zata yi kuka dan damuwar Omar tsaf zata sakata hawaye Bar mata wajan ma ya yi alamun bata bu atar amsa, har zai gota ya juyo ya ce, naji ana batun wani gwajin jini, Ina so ki sani babu wanda ya isa ya saka ayi min wani gwaji, gwara ki fa a musu kar azo ace za a auki jinina, dan wallahi sai na cakawa yaron da aka turo allurar yana fa a ya shige aki ya barta a wajan a tsaye cikin rashin sanin abinda zata yi. Didi cikin tsananin damuwa ta ce, Ya Allah ka kawo min mafita, rigimar Omar yawa gareta. Wayarta taji tana ara ta duba ta ga AbdulHamid ne ta san yana waje yana jiranta. Numfashi ta fesar ta fita daga gidan ba tare da ta auki wayar ba. A mota ta same shi ta shiga ta zauna tana sauke numfashi. Ya kalle ta ya ga yanayinta babu da i ya ce, Ya dai?. Sai da ta yi ajiyar zuciya ta ce, Omar gab yake da sakawa jinina ya hau Yalla ai, ka ga masifar da yake zazzaga min kamar shine gaba ni?. Ya yi murmushi ya ce, Ai dole yayi masifa fa, aure irin wannan baka shirya ba ai dole yaga kamar ba a kyauta masa ba. Yanzu maganar da nake maka ya rantse da Allah bazai je gidan amaryar ba, kuma daman na san bazai yi min alfarma biyu a yau ba. Na farko na tilasta masa ya furta ya amince da auren a gaban iyayenta, tunda har ya amsa musu ni kaina na san bazan iya ta wara shi ya je gidan ba a yanzu, sai kuma wani lokaci. Gashi suna zancen gwajin jinin da ake yi na aure, ya ce na fa a musu aka turo wani ya ebi jininsa sai ya chaka masa allurar. Dariya sosai AbdulHamid ya yi ya ce, Kai Omar yana da bin dariya wallahi. Dariya ma ya baka?. Dariya ya bani mana. Amma yanzu ya za ki yi? Ya kamata ace yaje gidan amaryar tunda har ya amince da auren. Ya ce wai ba ma ita zata biyo shi ba shine zai bita? Ashe ba za a je ba. AbdulHamid ya murmusa ya ce, Wannan amarya dai taga ta kanta, irin wannan miji mai zafin zuciya da zafin kai irin Omar zama dashi ai sai mai ha uri. Ga kuma yadda auren ya zo yana gani kamar an bashi ita sadaka, sai dai mu yi fatan Allah ya sa ya ri eta hannu biyu, amma zata sha wahalarsa na wani lokaci. Didi ta ce, wallahi tausayi take bani, sannan kunyar iyayenta nake