← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 205

Sashe 73

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

motsa balle ta mi a hannu ta kar a. Hannunta ya ri o guda aya ya saka mata takardar ya ce, "ki bu e domin ki tabbatar." Yadda hannunta yake rawa zai baka tabbacin zuciyarta bugawa take yi fiye da a'ida,ta kasa ri e takardar ma balle ta bu e. Cikin muryarsa mai saka yara su shiga hankalin su ya ce, "ki bu e na ce" ya fa a yana bu e mata idanunsa. Kai ta girgiza tana hawaye, ya kulle ido ya bu e akan fuskarta ganin sai kuka take yi ta kasa bu ewa. "Ki bu e!." Da hanzari ta fara bu e takardar tana sakin kuka mai matu ar sauti. Ta bu w amma ta i kallon abinda aka rubuta, sai kuka take yi sosai ta koma kan kujera ta zauna idanunta a kulle. Hawaye sai sauka suke yi akan takardar da take hannunta ta kuma i bu e idon balle ta gani. Yana tsaye yana kallonta cikin tsananin auna da soyayya kafin ya ce, "bu e idonki ki karanta ina so ki tabbatar ne." Nayla ta dinga girgiza kai tana kuka tana cewa, "A'a don Allah, bana son ganin komai ka auke. Ka janye sakin bana so, wasa nake yi ba da gaske nake ba." Abinda ta ce ya saka shi ya yi murmushi amma da yake idanunta a rufe yake bata gani ba. Omar ya ce, "Ayya ban san wasa ki ke yi ba, amma ki karanta in." "Ni bazan karanta ba, daman da ka ce kana sona daman arya ne baka sona, in kana sona ai baza ka sake ni ba. Daman na san baza ka ta a sona ba, kamar yadda ka ce baka sona na san baza ka so ni ba. Yanzu ina ka ke so na tafi? In na koma gida na ce musu na dawo yau kuma ka sake ni yau?." Yadda take kuka sosai da zuciyarta da gangar jikinta ya saka shi ya tausasa murya ya ce, "ke kika ce ai ko?." "Ni na fasa! Daman arya nake yi!" Ta fa a da arfi tana kuka sosai. Omar ya yi murmushi mai sauti amma kukan da take yi bai bari ta ji ba. Shiru ya yi yana kallon ta, ya rasa ta ina zai fara balle ya saka ta yi shiru. Da yar ya daure ya ce, "ki bar kuka." Bata daina kukan ba ya ce, "ki daina kuka ki kalli takardar." "Ni bazan kalla ba, bazan iya gani ba." Omar ya ce, "to bara na karanta miki." Da sauri ta dam e takardar ta chakume ta a irjinta jikinta yana rawa tana dana sanin furta abinda ta ce. Murmushi ya yi mai sautin gaske yana kallonta kafin ya har e hannayensa a irji yana kallon ta cikin tsantsar so da shau "Daman ai na ce miki bazan rabu dake ba, babu saki a tsakanin mu har abada!" Ya furta a tausashe yana kallon ta. A hankali ta fara tsayar da kukan, cikin sanyin murya ta ce, "gashi ka aikata, gashi ka sake ni." "Na ce ki duba kin i ki duba, ta ya zaki fahimci abinda ya ke ciki?." "Ni bazan gani ba." "In baki gani ba baza ki fahimta ba, ki bu "Ni bazan bu e ba, bazan karanta ba!" Ta fa a cikin hawaye. So yake ya yi abinda zata daina kukan amma ya rasa ta ina zai fara. Takawa ya yi zuwa inda take zaune, bai zauna ba yana daga tsaye ya bu e hannunta ya cire takardar ya warwareta daga cukurku eta in da tayi ya ce, "ki kalli abinda na rubuta, na rubuta ina...." Da hanzari ta mi e ta rufe masa baki tana wara idanunta tare da girgiza kai hawaye na sakkowa. Kallon ta yake yi tana daga tsaye a kusa dashi tana kallonsa hannunta na fuskarsa ta rufe masa baki. Juya mata takardar ya yi ya haska mata ta kalla ta auke kai, sai ta sake kalla ta zubawa takardar ido tana kallo har lokacin hannunta na kan bakinsa. _Ni Ina sonki Jidda, bazan kuma rabu dake ba. Gwara ki zauna dani kawai._ Abinda ya rubuta kenan da manyan ba i, ta kalli fuskarsa ya an motsa girarsa da idanunsa yana kallon ta. Hannunta ta janye a hankali daga fuskarsa ta rufe fuska a hannayenta saboda kunyar da taji ta rufe ta lokaci aya. Murmushi ya yi yana kallon hannayenta da suke kan fuskata, henna hannunta ya kar i hannunta sosai abin ka da farar fata. Zama tayi akan kujera, ya koma nesa da ita shima ya zauna yana kallonta har lokacin fuskarta a kulle take. Shi dai Allah ya ora masa son wannan yarinyar lokaci aya ba tare da ya sani ba, yana matu ar jinta a zuciyarsa da gangar jikinsa, ya rasa abinda yake ji a kanta, ji yake kamar ya ha iyeta ya huta kawai. Ya zuba mata idanu ya kasa cewa komai dan bai san me zai ce mata. Ajiyar zuciya ya yi yaga ta bu e fuskar amma kanta a asa tana murmushi fuskarta a kwa e alamun shagwa a. Samun kansa ya yi da cewa, "Da gaske bana arya dan na burge wani, bana fa ar abinda ba shine a raina ba dan wani ya ji da i. In bani da ra'ayi zan fa a miki a gaban ko waye, Ki ri e wannan Jidda!." Nayla murmushi take yi tana kallon asa jin sunan da yake kiranta dashi. Duk da ta san sunanta Jidda amma da ya kasance shi ka ai ne mai kiranta da sunan sai ya zama na musamman. Omar ya kalli gefe bai ce komai ba, shiru ya sake ratsa tsakani yana jin zuciyarsa na bugawa sosai, an rufe ido yayi ya bu e kafin ya yi ajiyar zuciya ya ce, "kina ji......" Nayla ta ago ta kalle shi suka ha a ido ta auke ido saboda kaifin idanunsa, cikin murya mai da in saurare ya ce, "Ki saka a ranki Omar yana aunarki, yana aunar zama dake a matsayin matarsa. Duk abinda zan fa a miki daga zuciyata yake ba dan ki ji da i ba, Ki ri e wannan ma Jidda!. Omar ba ya fa arya dan wani ya ji da i, Omar ba ya fa ar akasimn abinda yake zuciyarsa. Jidda! Ina sonki, ina aunarki auna mai yawa..!." Nayla kulle ido tayi farin ciki na ratsa ko ina na jikinta, hawaye yana sake sauka daga idanunta. Hawayen farin ciki, hawayen jin da i, hawayen walwala da samun abinda zuciya take muradi a rayuwarta. Wai ita Omar yake furtawa yana so, wai ita Omar yake so har yake fa a mata ido da ido. Omar masoyinta da ta yi dakon soyayyarsa yana yi mata tsawa, Omar masoyinta wanda ko kallon kirki bata ishe shi ba, yau shine yake zaune a gabanta yana amsa sunan masoyinta kuma mijinta, To me zata yi in ba kuka ba?. Omar bai lura da tana hawaye ba, ya sake yin ajiyar zuciya ya ce, "zaki je aiki gobe?." Kai ya girgiza alamun a'a sai ta tuna baya son body language ta ce, "A'a." "Kuka ke yi? Na fa i wani abun da bakya so ne?" Ya fa a yana kafe ta da idanu jin muryarta na rawa. Shiru tayi bata ce komai ba, shiru ya sake ratsa tsakaninsu kafin ya an yi gyaran murya ya ce, "Nayla!." Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, abinda Nayla ta ji a zuciyarta sai da ya kai ta ga jan salati, wani irin shock ta ji har cikin ashin da tsokar nama ya lullu e sai da ya amsa. Fizgarta ake yi, ji take in bata ha a jikinta da nasa ba zata iya haukacewa, hawayenta ya ara yawa sosai ta rasa yadda zata sarrafa yanayinta. Ganin kamar jikinta yama rawa sai ya zuba mata idanu ya ce, "kina lafiya?." Nayla ta aga kai alamun eh, ya nuna hawayenta ya ce, "kukan fa?." Nayla ta goge idanunta amma bata ce komai ba. Shi kansa yanayin da yake ciki kenan, amma bai san ta ina zai fara ba, bai ta a ha a jikinsa da wata mace ba, ko a lokacin Narma itace take rungume shi ba shine yake yi ba. Shiyasa ya rasa ta wacce hanya zai yi hakan, amma tabbas yana so ta ji Nayla a jikinsa ko zai ji sau in bugun zuciyarsa. Omar ya daure ya ce, "Gobe in sha Allah zamu je wani waje da safe." Nayla ta aga kai ta ce, "to Allah ya kaimu." "Amin, ki je ki huta" ya fa a yana tashi tsaye. Inda son ransa ne tabbas bazai bar Nayla ta kwana ita ka ai ba, zai kwana tare da ita ya yi mata masauki a jikinsa, ya tallafota ya kwantar da ita a irjinsa ta yi bacci yadda take so. Zai fa a mata kalmai masu da i a kunnenta, ya rarrasheta ya tabbatar bata zubar da hawaye ba. Sai dai kash! shi bai san ya zai yi, baya son za ewa da yawa, baya so ya za e kar ta ga kamar daman ya saba yiwa mata haka ne shiyasa ya kama kansa. Nayla ta mi e tsaye, jiri da nauyin kai ya saka tayi baya kamar zata fa i, da sauri ya ri o hannunta ta tsaya cak ya ce, "baki da lafiya?." Ta girgiza kai ta ce, "lafiya lau." "Kin tabbatar?." "Uhum! Abincin da na dafa maka fa?." Omar ya ce, "na ci abinci kafin nazo, ban san kin dawo ba, amma zan ci wani lokacin." Nayla ta aga kai kawai bata ce komai ba. Ya ce, "ki je ki kwanta." A hankali ta juya tana takawa zuwa aki ya bita da kallo har ta shiga. Ya yi ajiyar zuciya a bayyane ya ce, "Omar anya kaine?" Ya fa a yana an dukan fuskarsa ka an yana murmushi. Shima akinsa ya shiga amma zuciyarsa gabadaya tana ga Nayla, da yana da yadda zai yi gashi gata zasu kwana amma bai san ta inda zai fara ba. Ya yarda da batun Didi ya kamata ya shiga ajin da za a koya masa yadda ake tafiyar da mace a wannan angare na soyayya. A jikinsa yake jin ya kamata ya aikata abinda zai gamsar da ita son da yake mata,
Chapter 73 · 0% Book details