← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 205

Sashe 62

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wannan." aramin tsaki yayi ya ce, "ni kewarta na ce ina yi ba so ba, bana sonta kamar yadda na fa a miki a baya. Na yarda ina kewarta kamar yadda ki ka ce, amma ba wai so ba." Didi ta sake yin murmushi mai sauti ta ce, "Omar kana sonta, so ba an ka an ba, soyayya mai yawa ka ke yi mata." Sai ta fusata shi ya mi e a firgice ya ce, "na ce miki bana sonta, bana son aurenta dole ki ka yi min na kar a! Meyasa ki ke maimaita ina sonta bayan ni ba haka nake ji zuciyata ba?." AbdulHamid ganin yadda Omar in ya birkice sai ya arasa kusa dashi ya dafa kafa arsa ya ce, "Kwantar da hankalinka, koma ka zauna." Omar ya zauna yana cewa, "matarka ce take son tarwatsa min walwa, na ce mata ba sonta nake yi ba dole sai ta ce ina sonta ne?" Ya arasa fa a a sanyaye yana kallonsa. KRB3P034 Arewabooks@nanahaleema11. Didi ta bishi da kallo sannan ta yi dariya tana oye farin cikin ta ta ce, "to meye na fusatar dan na ce kana sonta?." Dafe kai ya yi da hannunsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Didi ta tausasa murya ta ce, "Na san ka so Narma a baya ko? Sannan....." katse ta ya yi ya ce, "Shiyasa na ce miki ba sonta nake yi ba, saboda abinda na ji akan ar Senator daban itama na ta daban. Kuma ke kika tabbatar min da ina son Narma, kinga kenan ita wannan ba sonta nake yi ba." Didi ta ce, "Ka nutsu ka bani amsar tambayar da zan yi maka don Allah." "kar ki tambayi abinda zai ata min rai." "To YaMar" ta fa a tana kallonsa dan ta ga reaction insa. Ai kuwa da sauri ya kalle ta ya ce, "Maimaita abinda ki ka ce." Didi ta ce, "cewa na yi YaMar." Lumshe ido ya yi ya bu e yana kallon wani wajan daban ya ce, "meyasa ke ban ji komai a raina ba da kika fa i wannan sunan nan? Ita kuma duk sanda zata fa a sai gabana ya fa i" ya juyo ya zubawa Didi ido tare da zaro su waje ya ce, "Na shiga uku! Anya Didi ba da aljanna kika ha a ni zama ba?." AbdulHamid da yake kallon dramar Omar ya yi dariya Didi ma murmushi ta yi ta ce, "ta ya gabanka zai fa i dan na fa i sunan da matarka take kiran ka dashi? ni fa jininka ka ce ba mata ba, taya zaka ji irin abinda ka ke ji a lokacin da matarka ta fa a?." Shiru ya yi yana sauke numfashi a hankali, a tausashe Didi ta ce, "Omar na san ka so Narma a baya, abinda nake so na tambayeka shine; lokacin da ka ke tsakiyar sonta ka ji irin abinda ka ke ji a yanzu a kan Narma?." Kai ya girgiza alamun a'a yana kallonta, ta ce, "lokacin da ku ka rabu ka ji irin wannan yanayin a zuciyarka?." Nan ma ya girgiza mata kai alamun a'a. "Ka yi kewarta kamar yaddaka yi kewar Nayla?, zuciyarka ta buga a lokacin kamar yadda yanzu take bugawa? Ka ji rauni a lokacin kamar yadda ka ke ji yanzu? Ka yi zazza i kamar yadda ka yi yanzu?. Ka jure zama da Narma kamar yadda ka jure zama da Nayla? Ka ji zafi a zuciyarka in wani ya yabi wani abu na Narma kamar yadda ka ji zafi a lokacin da aka yabi afar Nayla?." Omar ya yi tsitt yana sauraren Didi yana kuma kallon ta. Ajiyar zuciya Omar ya yi ya girgiza kai ya ce, "A'a duk ban ji ba." "Amma ka ji kishi da wani ya biyo Nayla ya ce yana sonta, ka ji zafi da ka ga afarta na zaga social media ana yabonta, ka ji babu da i a lokacin da nake hirar samarinta. Ka damu da rashin lafiyarta har jikinka ya yi sanyi kana so kaji ya take, ka jure zama da ita sama da ko wacce mace a duniya, zuciyarka ta karye akan rashinta har ka ke jin kanka kamar kwalin da babu komai. Haka ne ko Omar?." Omar ya yi aramin tsaki cikin gajiya ya ce, "Haka ne Didi, ki kai arshen maganarki na gaji da wannan tambayiyon." Didi ta ce, "Omar ba son Narma ka yi ba." Ya ago ya sake kallonta kafin ya musa ta ce, "Ta ya zaka ana karayar zuciya bayan Narma itace take sonka ba kaine ka ke son ta ba? Itace mace ta farko da ka samu kusnaci da ita shiyasa a lokacin ka auka sonta ka ke yi amma ba so bane. Zaka ana karayar zuciya da rauni ne in ka rasa wacce ka ke so Omar!" Ta fa a tana kallonsa kamar yadda yake kallonta. Abdulhamid ya ce, "hakan yana nufin kana son matarka so mai yawa Omar, duk abinda ka ke ji a yanzu shi ake kira da tsananin so. Baza ka ta a dawowa daidai ba in dai baka je ka dawo da ita ba." Omar ya yi shiru yana sauraren su, jin maganarsu yake yi kamar film ko kuma tatsuniya. Ta ya zasu ce masa wai Nayla yake so ba Narma ba? Bayan ya san Narma ita ce akace ya so ta? Shi abinda yake ji akan ta daban, abinda ya ji akan Nayla daban. Ta ya zai banbance soyayya da kuma abinda Didi take fa a? Shi gaba aya sun saka shi a tsaka mai wuya. Omar ya kalli Didi ya ce, "Didi ba sonta nake yi ba, na yarda dai ina kewarta kamar yadda ki ka ce, ina kewarta sosai na yarda da wannan amma ba wai ina sonta ba, ki bar zancen nan don Allah." Didi ta ce, "shikenan na bari Omar, ka yi tunanin maganar da na fa a maka, in ka tabbatar ba haka bane tana gidan anwar mahaifiyarta ka je ka sallame ta." Ya lumshe idanu ya ce, "Na fa a miki ki daina yimin zancen nan amma kin i ji." Didi ta ce, "kai da ka ce baka sonta meye na damuwa dan ina znacen zaka sake ta? Kaga....." jajayen idanunsa ya zuba mata hakan ya saka ta yi murmushi kawai bata arasa ba. AbdulHamid ya ce, "Ka yi tunani Omar, in kana bu atar shawara ofa a bu e take zaka iya kirana. Wata shawarar namiji yana da bu atar tattaunawa da an uwansa namiji, na san baka da aboki shiyasa nake so na zamar maka aboki Omar." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "to" ya kalli Didi ya ce, "na gode, ku je g da kawai" ya fa a yana jingina da kujera yana tunani. Didi bata sake cewa komai ba dan ta riga ta gama dashi gaba aya. Ta san ko ya zai motsa sai ya tuna da kalamanta, a cikin kalamanta kuma dole ya samo gaskiya. Omar kansa ya kulle ya kasa tunanin hakan ya saka ya tashi shima ya fita daga gidan saboda in ya zauna tunani zai saka kansa ya yi bindiga. Nayla ta kwashe sati biyu cif a gida, duk kauce-kaucen Omar ya tabbatar da maganar Didi gaskiya ce. Abin ya wuce gizo da take yi masa mafarkinta kawai yake yi, indai zai kwanta ya tashi sai ya yi mafarkinta. Zuciyarsa na bugawa a kanta ya kan rasa inda zai saka kansa, sai ya ru e ya rasa inda zai je ya samu sassauci. Gaba aya ya susuce yana gab da zama zararre akan Nayla. Ya yarda da Nayla yake so ba Narma, sai yanzu ya tabbatar da inda ace abinda yake akan Nayla shi yaji a lokacin Narma da babu halittar da ta isa ta raba shi da ita, kamar yadda ta nemi ya gudu da ita tabbas zai iya aikata hakan. Sai dai kash! Ba akanta yake jin wannan yanayi ba, akan Nayla yake jinsa!. Babban abinda yake aure masa kai shine in dai son Nayla yake yi ita Narma me ya yi mata a baya? Sonta ya yi ko tausayinta yaji ko kuma meye bai sani ba. Hankalinsa ya gama kaiwa arshe wajan tashi, ya tsayar da tunaninsa waje aya ya kuma yarda da gaske dai Nayla yake so ba wai da wasa ba. Abin ka ga soyayyar farko, in yana tunaninta jikinsa har karkarwa yake yi saboda azabar da zuciyarsa take yi masa, fatar jikinsa har aukar zafi take yi saboda yanayin da zuciyarsa take ciki. Nauyi irjinsa yake yi masa sosai, har ya kai ya kawo in ya motsa yana jin zafi a asan zuciyarsa. In ya yi tari sai ya ji numfashinsa yana neman tsayawa cak, sai ya ja numfashi da arfi sannan yake samun sassaucin nauyin da yake yi. Ranar asabar bayan sallar azhar ya kasa jurewa, ya rasa ya zai yi ya kasa cin abinci tun safe. Ya ha a tea amma ya kasa sha ruwa kawai yake zubawa cikinsa. Ya kasa cin komai, baya sha'awar cin komai balle ya nema ya zuba a cikinsa, duniyar yake ji ta yi masa zafi tana juya masa. Nayla ka ai yake so ya gani, itace abincin da idanunsa da zuciyarsa take marari, muryarta yake so ya ji ta furta sunan da ta saba fa a masa. Ya tabbatar da ya ji wannan suna daga bakinta duk abinda yake ji a zuciyarsa zai daina ji. Ganin yana neman kashe kansa da tunani sai ya kira Didi a waya dan tunda tazo basu sake magana ba, tana auka kafin su gaisa ya ce, "Didi meye abu na gaba?." Didi ta ce, "Ya naji magnarka haka, Omar ko ka je asibiti a duba ka?." "Didi gab nake da zaucewa wallahi, tafasa jinina ake yi kullum" ya fa a a sanyaye." Didi ta ce, "Allah ya kawo mafita Omar." "Ina tambayarki, meye abu na gaba?." "kamar me kenan?." "A ina zan sameta?." "Ita wa kenan?." "matata!" Ya fa a kansa tsaye ba tare da wani tunani ba. Didi ta yi dariya mai sauti ta ce, "ban gane abu na gaba ba." Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Me aka ce zan yi?." Didi ta ce, "akan dawowarta?." "Uhum." "Gidan iyayenta zaka je." "Ina ne gidan? Ki tura min
Chapter 62 · 0% Book details