Sashe 75
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a nan, in ka huta sai mu je wajan Abiy in." Omar ya ce, "da dai mun fara zuwa wajan shi." "Shi ya ce sai ka huta, na tabbatar ka huta ka kuma ci abinci saboda gajiyar hanya." an murmushi Omar ya yi kawai Jawad ya kalli Nayla ya harare ta ya ce, "Sai ki yi ai" ya fa a yana fita ya bar su a falon. Zama Nayla ta yi tana kallonsa tana mamakin ya aka yi Abiy ya san da zuwan su? Sannan ya aka yi suka saba haka da Ya J har yake masa murmushi?. Ganin kallon da take masa sai ya aure fuska ya toshe duk wata ga ar da zata tambaye shi wani abu. Ai kuwa sai ya yi mata kwarjini, ta kasa tambayarsa amma jikinta ya gama yin sanyi sosai, bata san wacce irin tarba zata samu daga wajan Abi ba. Fitsari take ji sosai, amma bata son tashi shi kuma bai motsa ba ya dai auki ruwa ya sha daga nan bai sake ta a komai ba. Nayla jin fitsarin zai hanata sukuni sai ta mi e ta nufi ofar da take falon ta bu e, daman ta san empty room ne wanda ake cewa zai zama na Jalal, ta shiga tare da kullo ofar. Sai a sannan ya kalli inda ta shiga ya an murmusa ka an bai ce komai ba. Ba jimawa ta dawo ta zauna ta ce, "YaMar ka ci abincin, ka ga baka ci sosai ba a gida." ago idanunsa ya yi masu saukar mata da kasala ya ora a kan nata idanun. Sauke idanunta asa ya ji tana cewa, "in na kalli idonsa wani iri nake ji, amma baya ganewa ya yi ta kallon idona" ta fa a a hankali ba tare da ta yi tunanin ya ji ba. Bai nuna mata ya ji in ba ta ce, "ka ci abincin." Bai ce komai ba ya dai sauke ajiyar zuciya amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Nayla ta turo baki kanta yana asa amma bata yi magana ba. Yana lura da duk motsinta magana ce kawai bazai yi mata ba, bai shirya maganar ba ne sai sun je wajan mahaifinta sun dawo, daga lokacin duk ma abinda take so ya ce zai ce mata, amma yanzu bazai ce ba. Yadda ya yi shiru haka ta yi shiru itama tana kallon falon sai kuma ta an zame ta kwanta dan ta gaji sosai. Jawad ne ya shigo da sallama ya ce, "Omar zamu je masallaci?" Ya fa a da sigar tambaya. Omar ya mi e tsaye ya ce, "na ji ana kiran sallah." Jawad ya kalli Nayla ya ce, "Ke wai baza ki shiga cikin gidan ba? Jalila da Jalal suna nan, Mama ce bata nan." Nayla bata ce komai ba Jawad ya yi tsaki suka fita da Omar Tana nan zaune Jawad ya dawo shi ka ai ya ri o hannunta ya ce, "Sai wani ar ki ke yi kamar ba uwa, Omar in ma ya fi ki sakewa, meye haka ne wai?." Nayla ta ce, "Yaya J ni ban san nan zamu zo ba, Ina tsoron ha uwa da Abiy." Jawad ya mi ar da ita tsaye ya ce, "Wuce mu je, shi suna tare da Abiyn ma." "Da gaske ka ke?." "Mu je ki ga zahiri." Tare suka fito zuwa babban falon Abiy kanta yana asa. Abiy yana zaune akan kujera Omar yana zaune a kan carpet suka shigo, a hankali take takowa tana shigowa falon cikin sanyin jiki da fa uwar gaba. Abiy yana kallo ta yana murmushi ganin kanta yana asa kuma kuka take yi ya ce, "Mamana ke dai kin cika yawan kuka, ko gidan nan ne bakya son zuwa?." Nayla jin muryar Abiynta cikin salo na wasa ta ago da sauri ta kalle shi ta ga yana murmushi yana kallonta. Murya na rawa ta ce, "Abiy." Abiy ya ce, "Na'am Mamana." Da sauri ta arasa kusa da shi ta zube a gabansa ta ora kanta a akan afarsa tana kuka sosai. Abiy ya ora hannunsa akanta ya ce, "Haba Mamana to meye na kukan kuma? Tashi ki goge hawayenki bana son kuka kin sani." Kai ta girgiza ta ce, "Abiy fushi ka ke yi dani, Abiy na da e ban ganka ba." "Ni bana fusui da ke Mamana, kuma ba ga shi yanzu kin ganni ba? Ki bar kuka ki tashi mu gaisa ko?." Nayla ta ago kai tana kuka Abiy ya ri e hannunta ya ce, "goge hawayenki ki zauna sosai, kar kan ki ya yi ciwo kin ga kun yi tafiya mai nisa." Zama tayi amma bata saki hannunsa ba, Abiy ya yi murmushi ya ce, "to sakar min hannun mana Nayla." No e kafa a ta yi tana kifta idanu kamar yadda ta saba gashin idanunta da ya jike da hawaye. Kallon Omar Abiy ya yi ya ce, "Kana fama da Mamana da wannan shagwa ar ta ta." Murmushi ya yi kawai dan shi a duniya babu wanda ya ke jin nauyinsa da girmansa kamar Abiy, baya shi sai su Daddy. Abiy ya ce, "Ina fatan komai lafiya?." Omar ya ce, "Lafiya lau." "Haka ake so, Allah ya taimaka ya bada nasara." "Amin ya rabbi." Omar ya daure ya ce, "Abubuwa da yawa sun faru a baya, da yadda aka yi auren nan da yadda komai ya faru kusan duk bai yi da i ba. Alhaji na san kana fushi da ita, ka aura mata ni ne ba dan kana so ba sai dan dalilin da ni da ita bamu sani ba, Gata na dawo da ita Alhaji, koma meye ya faru ina ro on alfarma a yafe mata." Abiy ya yi murmushin jin da in kalaman Omar ya ce, "Omar kar ka sake kirana da Alhaji, ka ce min Abiy kamar yadda take fa a ita da an uwanta. Ko babu Nayla ni kamar uba nake a wajanka." Omar ya yi murmushi amma bai ce komai ba. Abiy ya ce, "Tabbas da farko na aura auren ku da Nayla a cikin wani yanayi na zafin zuciya, Nayla ta san halina in raina ya aci na kan aikata abinda ma ban san na yi ba. Amma daga baya na amince da auren ku da ita ari bisa ari, domin kuwa duk motsin ka kai da Nayla na sani, ko fita Nayla ta yi ta je gidan Hajja zan sani. Yadda ka ke bata tsaro da kulawa ya sa naji hankalina ya kwanta da zaka ri e Nayla hannu biyu, duk da baka sonta, kuma baka son aurenta." Omar ba tare da nauyin komai ba ya ce, "Abiy wannan duk labarin baya ne, tabbas a baya ban kar i aurenta da son raina ba sai dan an yi min dole. Amma a yanzu ko da ace babu aure a tsakanina da ita zan iya zuwa ko ina dan neman aurenta. Zan ata adadin lokacin da ya rage min a duniya wajan rayuwa da ita." Abiy ya yi murmushi cikin jin da i, daman Daddy ya bashi labarin duk abinda ya faru kuma ga zahiri shima ya gani. Abiy ya ce, "ma sha Allah, haka na ke fata kuma haka nake so na ji Omar. Alllah ya sanyawa auren ku albarka, Allah ya ba ku zaman lafiya mai orewa." Abiy ya kalli Nayla da take kusa dashi har lokacin ya ce, "Mamana." Nayla cikin shagwa a ta ce, "Abiy ka daina fushi da ni?." "Ni ba fushi nake yi dake ba Nayla, da farko na an yi fushin amma daga baya na fahimci komai da yadda komai ya faru. Sai na barki ki mallaki abinda zuciyarki take so, na tabbatar aurenki dashi shine zai baki farin ciki tunda har ki ka iya furta min kina qaunarsa. Abinda ya saka na ji na sare a game da lamarin auren lokacin da na tabbatar bai kar i aure ki ba, ko yaushe tunani nake yi a wanne hali ki ke. Amma daga lokacin da yake baki tsoro da arfinsa da zuciyarsa na san baza barki ki zubar da hawaye a gidansa." Nayla ta ce, "Amma Abiy meyasa lokacin ka yanke hukunci bayan na ce na fasa?." Abiy ya yi murmushi ya ce, "Lokacin da ki ka bar falon nan a ranar kika tafi Kano ba kin ce Maman ki ce ta ce ki je ba?." Nayla ta aga kai ta ce, "Mama ce, itace tace na je zan fi samun nutsuwa kafin na dawo, sannan zata saka ka amince da abinda na ce." Abiy ya ce, "Kuma ita ta ce ki yi min text." "Eh Abiy, amma da na je sai na tarar an yi hacking WhatsApp account in dan cewa tayi nayi maka ta whatsapp, sai da muka dawo dashi ni da Salma. Ban kai ga yin message in ba na ajjiye wayar da na duba naga an sake yin hacking insa, sai da na dawo dashi sai na yi maka message in." Abiy ya shafa kanta yana murmushi ya ce, "Yanzu kina farin ciki da auren ko bakya yi?." Nayla ta yi murmushi ta kalli Omar da yake kallonta amma ta asa idanu sai ta sunkuyar da kai. Abiy ya yi murmushi ya ce, "komai ya wuce ki auka daman haka addarar aureki take, Allah ya rubuta a lokacin sai kin zama matar Omar shiyasa komai ya zama a haka. Inda mutuwa ce haka zaki ji ana fa a Nayla ta mutu ba shiri, to haka aure ma indai rabon auren yayi kira ka amsa zance ya are. Ina matu ar alfahari da auren nan na ku, Ina kuma fatan ya ore daga nan har aljanna." Nayla ta sunkuyar da kai tana murmushi cikin jin da i da farin ciki. Ta kalli Abiy da shagwa a ta ce, "Yanzu zan iya zuwa gidan nan ko yaushe?" Kafin ya bata amsa ta cigaba, "Abiy ka ce kar nazo maka gida sai ka neme ni, na da e ban ganka ba" ta fa a cikin rauni. Murmushi yake yana kallon ta, kafin ya girgiza kai ya ce, "Nayla na ce komai ya wuce, ki auka komai bai faru ba, kuma ba gashi yanzu kin ganni ba?." Ta aga kai ya yi dariya ya kalli Omar ya ce, "Omar ya