Sashe 80
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
babban an yatsansa akan kumatu sa biyun farko kuma suna kan goshinsa, ya an motsa su kamar yana sosa saman goshinsa kamar yadda hakan ya zamar masa al'ada. Nayla bata jira cewarsa ba ta tashi ta kawo abincin ta yi serving insa a wani babban plate mai fa i wanda ya auke duk abinda ta zuba masa. Kallon abincin yake yi domin kuwa ya yi matu ar burge shi, ga hamshi da yake yi a ido ma kana gani ka san zai yi da i sosai balle kuma in ka ci. Nayla ta ce, "ka ci." Kallon ta ya yi da shanyayyun idanunsa, ta an jure kallon idanunsa na wani lokaci kafin ta janye idon tana kallon asa. Kallon abincin ya yi ya ce, "A ina ki ka samu kayan girkin nan?." Nayla ta ce, "siyo min aka yi." Omar ya girgiza kai ya ce, "ba nace duk abinda ki ke so ki fa a min ba?." Nayla ta ce, "gani nayi wannan ba wani abun bane." "Wani abu ne, daga yau kome zaki siya ki sanar dani." Nayla ta aga kai alamun to ya saka hannu aljihu ya auko ragowar ku in jikinsa da basu wuce dubu goma ba ya ajjiye mata ya ce, " auki ku inki." Nayla zata yi magana ya zuba mata ido dole ta yi shiru ta auka ya ce, "bana son musu, ki ri e wannan ma." Nayla ta ce, "To." Abincin da ta ajjiye masa ya auka ya jingina da kujera bayan ya ora afa a kan aya. Ya kalle ta ya ce, "ke bakya ci?." Nayla ta ce, "na ka zan ci." Ga mamakin ta sai ya ajjiye ya ce, "bismillah." Murmushi ta yi ta ce, "Wasa nake yi, yanzu zan ci nawa." "Ba ki isa ba, zo mu ci tare." Babu yadda ta iya haka ta dawo kusa dashi ta saka spoon a abincin masa tana ci kamar yadda yake ci. Girgiza kai ya yi ya kalle ta murya a asa ya ce, "Abincin ya yi da i." Farin ciki ya mamaye zuciyar Nayla ta ce, "Na gode." Bai ce komai har suka gama cinye na plate in zata ara ya ce, "ke ka ai." Ta ce, "amma baka ci da yawa ba." "Ya isa haka" ya fa a yana aukar wayarsa jin ana kira. an tsaki ya yi ya ajjiye wayar ya sake mayar da yatsunsa kan goshinsa kamar ko yaushe. "YaMar!." Sai da ya lumshe ido sannan ya kalle ta ta ce, "Shagunanka yanzu nawa ne?." Ya ce, "da bakya nan dan bu e guda hu u, shida kenan." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Allah ya taimaka ya sa ka fi haka." "Amin." "An fara ha a wanda Abiy ya ce zasu kar a?." Ya girgiza kai ya ce, "An fara, saura ka an a kammala." Ta sake yin murmushi ta ce, "Allah ya sa albarka." "amin ya rabbi " ya furta ba tare da ya kalle ta ba. hamshin turarenta ya dame shi, ru a masa tunani yake yi lokaci aya shiyasa ko magana baya son yi dan kar ta fahimci yanayin da yake ciki amma ta kasa ganewa, shi kuma yanzu bazai iya yi mata banza ba, in dai zata ce sai ya tanka. aramin tsaki yayi tunawa da wani abu, a bayyane ya ce, "Na manta." Nayla ta kalle shi ta ce, "'me ka manta?." Omar ya ce, "na so na tashi azumi yau, na manta." "Azumin meye?." "Kaffara." Nayla ta kalle shi da mamaki ta ce, "ta meye?." Omar ya kalli idanunta yana juya nasa idon a cikin nata kafin ya auke kai ya ce, "Na yi rantsuwa bazan kar i abinda ya fito daga hannun wanda suka kar i min aurenki ba, na rantse bazan so abinda suka bani ba, na rantse bazan zauna dake ba, sai gashi komai ya canja sama ta dawo asa. Abinda na rantse a kan bazan so ba yanzu ita nake yiwa son da ban ta a yiwa wata halitta a duniya ba, ina kasa sarrafa kaina saboda yadda nake jin soyayyarta a zuciyata. Kin ga azumin kaffara ya kama ni. Abin mamaki ba a ta a karya min rantuswa ba sai a kan ki, in Omar ya ce eh baya dawowa ya ce a'a, haka in ya ce a'a ba ya cewa eh. Amma a kan ki na ce a'a yanzu na dawo na eh da babbar murya, canji yana ta zuwa ta dalilinki." Nayla tayi murmushin jin da i ta ce, "Naji da i da na zama ta farko in sha Allah kuma ta arshe." Murmushi ya yi bai ce komai ba Nayla ta ce, "Yaushe zaka fara azumin? Sai na ta ya ka." Kallon ta ya yi ya kulle ido ya bu e ya ce, "zan fa a miki." Nayla ta amsa tana murmushi, ta an juyar da fuskarta dimples inta suka bayyana sosai. Omar ya bita da kallo, cikin tsaddiyar murya Omar ya ce, "na fa a miki wani abu?." Nayla ta aga kai tana kallonsa cikin shau aunarsa, in duk da ba wata doguwar hira suke yi ba, amma in yana yi mata magana cikin salon da yake yi da i take ji sosai. Omar ya kalli idanunta ya ce, "Ki cigaba da murmushi, murmushi yana yi miki kyau sosai, ki cigaba da yinsa yana sake awata fuskarki." Bata san lokacin da ta sake fa a murmushinta ba, ta saka hannu ta rufe fuskarta cikin tsananin jin da i da farin ciki. Tashi ya yi ya bata wajan, dan in yana zaune kusa da ita bai san irin arin zancen da zai dinga yi ba, sai yanzu ya amince da maganar Didi da take cewa daga zuciyarsa maganar zata dinga zuwa kan harshensa, a lokacin da ta fa a ya auka fa arta ce, sai gashi kuwa ya ga zahiri. Nayla da walwala ta tashi ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke ta ajjiye sannan ta shiga aki ta shiga ban aki. Ba jimawa ta dawo ta ora ruwan zafi, tana tsaye ya yi zafi ta juye ta kai ban aki ta yi wankan tsarki ta fito tayi sallar azahar da la'asar da suke kanta a lokacin. Babu jimawa aka yi sallar magriba, ta yi sallah ta fito falon dan tana so ta tambaye shi zata je gaishe da Hajja. Ta aga hannu zata yi knocking ofar akinsa sai ta tuna ya hanata, sai ta fasa ta mur a handle in ta shiga da sallama. Yana tsaye ya fito daga wanka yana aure da towel kalar blue, ya tattare towel wajan aurawa dan gaba aya bai wuce cinyarsa ba. Jikin sai igar ruwa yake yi, haka gashin jikinsa ya kwanta ya bi ruwan fatar jikinsa. Kai tsaye ido suka ha a da Nayla ta yi wata irin zabura ta juya da sauri zata koma ya ce, "kar ki fita, shima wannan na hana ki, ki ri e hakan." Nayla ta dakata daga fita daga akin jikinta na rawa sosai. Ashe jiya ba komai ta gani ba, yau ne ta ga cikakkiyar irar da Allah ya yi masa, yadda ruwa ya kwanta a jikinsa ya arawa fatarsa haske da wani irin kyau mai aukar hankali. Nayla bata yi zato ba ta ji ya juyo da ita ya ri e kafa unta yana kallon idanunta da ta kulle da sauri tana kiftawa kamar yadda ta saba. Sakinta ya yayi ya bar wajan, idanunta a rufe ya saka kaya ya zauna akan kujera ya ce, "kin shigo kin rufe ido, baki son ganina ne?." A hankali ta bu e ido, sai taga ya saka doguwar riga mai gajeren hannu ya ora afa kan aya yana gyara wani kamar zare da yake aure a afarsa wanda ya haska afarsa sosai. Ganin ya saka kaya sai ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Daman ina so na je na gaishe da Hajja." Omar ya kalle ta ya ce, "To, in na yi sallah sai mu je tare?" Ya fa a da sigar tambaya. Bata ce komai ba ta juya zata fita ya ce, "Ina zaki je?." aki" ta bashi amsa a tsorace ya ce, "Nan ba aki ba ne?." A sanyaye ta araso ta zauna a kujerar da take facing insa cikin sabon yanayi. Bai mata magana ba ya gama gyara ba in abun da yake afarsa ya sauke afar. Nayla ta bi afar da kallo tana mamakin namiji da abu a afarsa kamar sar afa?. "Meye ya baki tsoro?." Tambayarsa ta ji a sama bata yi tunani ba. Ta daure ta ce, "Babu komai." Bai ce komai ba shima sai ya mi e tsaye ya fita daga akin. Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "abinda baka saba gani ba, namiji da towel a tsaye a gabana, ko a mafarki ban ta a gani ba. dole na ru Sallah tayi kamar yadda ya fita sallah, bayan ta idar ta saka hijjab dogo har asa ya shigo ya kalle ta ya ce, "mu je." Tare suka fito suna tafiya a asa mutane suna ta kallon su wasu suna gulma. Ganin ana kallonsa sai ya ri e hannunta, ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba tayi murmushi suna tafiya hannunsu a sar e har gidan Hajja. Itace ta fara shiga ba jimawa ya bi bayanta ya same ta a zaune kusa da Hajja ya shiga sallama. Sallamar da ya yi ya saka suka kalle shi suka amsa Hajja ta ce, "A'a Ummaru barka da zuwa, lallai yau farar rana ce, Omar ne da kansa ba aike ba?." Fuskarsa a aure take kamar ko yaushe, sai da Hajja ta yi magana ya an saki rai amma ba murmushi ya ke yi ba ya ce, "Barka da dare." "Barka dai Omar, ya gida ya iyali?." "Lafiya" ya amsa cikin muryarsa ta ko yaushe, cikin aji da asaita. Salma da take gefe ta ce, "ina yi Omar in Nayla." Bai san ya yi murmushi ba sai da ya ji Hajja ta ce, "Lallai Ummaru, ni da yake ban saka Hauwa'u a ciki ba shiyasa baka yi murmushi ba." Bai ce mata komai ba ya kalli Salma ya ce, "Lafiya." Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru kamar ko yaushe. Kallon falon yake yi yana tuna ranar da aka sanar