← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 205

Sashe 82

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ha uri ka yafe min, zan fa a musu kar wanda ya sake yi min waya." Kallon ta ya yi jin abinda ta ce, bata san abinda ta ce in ma sake bashi haushi ya yi ba. Wai zata ce musu, kenan ma sai ta yi musu magana har su ji muryarta, tsaki ya ja ya share ta bai yi magana ba ta ce, "Don Allah YaMar!." "Ki fita ki baki waje bana son hayaniya." "Don Allah ka...." Cikin tsawa ya ce, "ki bar nan na ce!." Firgita tayi ta juya kamar zata tafi, sai ta fasa ta dawo da sauri ta fa a jikinsa ta rungume shi ta zagaya da hannunta ta ri e bayansa gam tana kuka. "Ka yi ha uri, ka yi ha uri YaMar ka yafe min!"abinda take fa a kenan tana kuka akan irjinsa. Kulle ido ya yi ya bu e bai ri eta ba kuma bai janyeta daga jikinsa ba. Kalmar ha uri take ta jera masa tana hawaye yana jinta bai ce komai ba. Ta jima a haka tana kuka tana bashi bashi ha uri, yadda take magana tana kuka a jikinsa ya saka ya runtse ido yana ji kamar ana ura masa kukan da take yi cikin zuciyarsa. A hankali ya an sauka ka an, ya ago ta daga jikinsa yana kallon fuskarta da ta ji e da hawaye gashi ta an yi ja ka Murya a tausashe ya ce "Baki yarda ina sonki ba?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "Meyasa ki ke amsa wayar abokin aikinki a gabana? Ko neman aurenki nake yi in ki ka yi hakan a gabana raina zai aci balle ke matata ce." Nayla ta ce, "wallahi ban sani ba, ban san number ba." Omar ya girgiza kai ya ce, "ya aka yi suke samun number ki? Meyasa suka damu da rashin zuwa aikinki? Sonki suke yi?." Ta girgiza kai da sauri ta ce, "A whatsApp group na tabbatar suke aukar numberta, tunda akwai group na ma'aikatan." Omar ya ce, "sonki suke yi kenan?." Ta girgiza kai alamun a'a kafin ta ce, "A'a." "Meyasa suka damu dake haka?." Nayla ta sunkuyar da kai ganin yana bin fuskarta da kallon da yake kashe mata jiki. Ya an kawar da kai ya ce, "baki fa a musu kina da aure ba ko? Saboda aurena ba aure bane ba ko Jidda?." Cikin kuka da shagwa a ta ce, "Wallahi sun sani, kowa ya san ina da aure, Ka yi ha uri don Allah." Ajiyar zuciya ya yi ya kalli window bai kalle ta ba ya ce, "na yi ha uri ko Nayla? Kin san abinda nake ji da zaki ce nayi ha uri?." Jin ya fara magana a kausashe ya saka ta sake langwa ewa ta ce, "ban sani ba, amma ka yi ha uri wallahi ba halina ba ne, in kana ganin arya nake ka tura har inda nake aiki a tambaya." "Hmmm!" Shine abinda ya furta kawai bai ce komai ba. Barin jikin window ya yi ya araso ya zauna akan sofa ya har e hannayensa waje aya yana kallon wani wajan daban. Nayla ta araso inda yake tana kallonsa bata ce komai ba. Shiru ya ratsa tsakaninsu, ya zubawa waje aya bai ce komai ba ita kuma bata yi magana ba. Ajiyar zuciya ya yi ya kalle ta ya ce, "Tun farko na san da maganar aikinki, iyayenki sun fa a min amma a lokacin na ce ina ruwana, in ma duniya zaki bari ba aiki ba bai dame ni ba. Ashe na yi babban kuskure, ashe na yi kuskuren da ban ta a yin irinsa ba a rayuwata. Barin ki kina aiki kamar a ha a rami ne a binne ni da raina. Amma...." Ya ja numfashi mai tasho kana ya ce, "Bazan hana ba, bani da wannan ikon na hanaki aiki tunda na san dashi, in na hanaki ma na cutar dake. Amma akwai gab ar da za a zo zaki ajjiye aikin matu ar kina son zama dani, bazan juri wannan abubuwan a tare da matata ba. Amma a yanzu zan yi ha uri, na san da batun aikinki tun ba yanzu ba, ban isa na hana ba" ya fa a tana an lumshe idanunsa a hankali yana bu ewa a hankali. Nayla ta ce, "i'm sorry." Ya kafa mata ido irr yana kallon fuskarta, ita kam idanunsa da suka koma ja ya saka ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. "Jidda kin san zan iya tashin garin Kano a kan kishinki? Zan iya fuskantar ko wanne alubale akan hakan. Zan iya aikata komai akan kishinki, zan iya...." maganar ma alewa tayi yana girgiza kai kafin ya ce, "Ki kula!" Ya fa a yana girgiza kai yana cize bakinsa cikin sautin da yake nuna takaicin da zuciyarsa take ciki. "Ka yi ha uri!." "Laifi ki ka yi ki ke bani hakuri!?." Yadda ya yi maganar cikin kaushi ya saka ta an yi baya bata ce komai ba. KRB3P47 Omar ya ja dogon numfashi ya kulle ido ya sake jan numfashi ya ora afa a kan aya ya ce, "laifina ne, ban san abin zai zama haka ba da tun farko bazan amince da aikinki ba. Bazan amince ba!" Ya fa a yana shafa fuskarsa da duka hannayensa. Nayla ta ri e hannunsa kawai ta fashe da kuka ta ce, "I'm sorry YaMar bazan sake ba, kuma in kana so sai na daina zuwa aikin gaba aya. Kuma ni bana kula kowa, bana magana da kowa sai maganar aiki kawai." Yana jinta amma bai san me zai ce mata ba, dan wallahi a yadda yake jin zuciyarsa bai san abinda zai iya aikatawa ba. Ta jima a haka tana ri e da hannunsa kafin ya ce, "ki je." Nayla ta ago ta kalle shi ta ce, "ba ka ce ka ha ura ba ai." "Na ce ki bani waje." Nayla zata yi magana ya ce, "na ce ki bani waje!" Ya fa a yana wara idanunsa da suke matu ar bata tsoro. Sai kawai ta sake fashewa da kuka ta sake shiga jikinsa ta ri e shi tana kuka sosai. Kanta yana shimfi e a irjinsa a daidai saitin zuciyarsa, ta zaga da hannun ta ri e shi sosai tana kuka. Wani irin abu yake ji daga zuciyarsa yana sauka kamar abu yana zubewa a asa, ya lumshe ido yana jin sassauci akan kishin da yake addabar zuciyarsa. Sun jima a haka kuma bata daina kuka ba ya ce, "ya isa, ki bar kuka ki je ki kwanta." Ta girgiza kai ta ce, "ka yi ha uri?." Shiru ya yi bai ce komai ba ta ce, "in baka yi ha uri ba babu inda zan je." Lumshe ido ya yi ya sake bu ewa ya raba ta da jikinsa dan hakan ba aramin canja masa yanayi yake yi ba ya ce, "na yi, ki je." Nayla ta kalle shi har lokacin fuskarsa babu walwala ko ka an ta ce, "a nan zan kwana" ta fa a tana sunkuyar da kai. "Yau me ki ka gani a akin?." "Babu komai, a nan dai zan kwanta." Kawar da kai ya yi tare da yin murmushi ka an ya koma ya zauna bai ce komai ba. Nayla ta wuce ta je ta zauna a gefen gadon tana goge hawaye. Ta jima a zaune shima yana zaune babu wanda yake magana a cikinsu, shi waya ma yake dannawa. Kwanciya ta yi jiki a sanyaye sai da ta jima da kwanciya sannan ya tashi ya kwanta bayan ya kashe hasken akin ya kwanta. Shiru bai motsa ba itama bata motsa ba, ya juya ya kalle ta bai ce komai ba dan ya san idonta biyu kafin ya ga bacci ya auketa. Murmushi ya yi da ya tabbatar tayi bacci ya matso yana kallon fuskarta. Abin mamaki yake bashi, Omar ne da wata a kwance a gado aya sunan matarsa, Omar da son wata a zuciyarsa yana jin kishin ta kamar ya ora hannu a kai ya yi ihu saboda zafin kishin. Bai ta a kawowa hakan zai faru a rayuwarsa ba sai gashi ya faru. Fuskarta ya shafa a hankali ya ja hancinta kafin ya koma ya kwanta dan fushi yake da ita. Tun asuba ta lura da bai bar fushi ba fuskar sa tana nan a yadda suka kwanta, ta dai gaishe shi ya amsa daga nan bai sake cewa komai ba. Da safe ta yi breakfast bai i ci ba ya ci amma bai ce mata komai ba daga nan ya fita. Da wannan damuwar ta yini ranar, Allah ya taimaketa Jidda ta zo, zuwan Jidda ya saka aka kira Salma suka baje suna hira. Sai yamma Jidda ta tafi bayan ta sake bata shawarar da take ganin in tayi amfani da ita zamansu zai sake wuce yadda yake. Salma ma ta wuce gidan Hajja aka bar ta ita ka Girki ta yi an ka an ta ajjiye masa, bai shigo ba sai gab da magriba shima bai jima ba ya fita bai dawo ba sai bayan i'sha. Yana shigowa tana fitowa cikin fitted gown ta lace mai bala'in kyau, lace in pink colour ne hakan ya saka ya kar e ta ya amshi fatar jikinta. are mata kallo yake yi cikin shau i da tsantsar qauna da kuma zallar sha'awarta da ta fara mamaye masa zuciya da gangar jikinsa lokaci aya. Ita kanta ta tsargu da kallon da yake yi mata, domin ba kallo ne na ko yaushe da ya saba ba. Ta an sunkuyar da kai ta ce, "sannu da zuwa." Bai amsa ba kuma bai daina kallon ta ba, ta ago kai a hankali ta kalle shi, ta auka da suka ha a ido zai janye idonsa amma sai ta ga bai yi ba sai ma lumshe idon da ya yi ya sake bu ewa a kanta. Ta ce, "YaMar sannu da zuwa." Sai a sannan ya aga mata kai alamun yauwa tare da yin ajiyar zuciya. Wuce ta ya yi ba tare da ya ce komai ba, Nayla ta bishi da kallo ta ce, "Wannan bawan Allah yana da abin mamaki, yau ya koma fari, gobe ya koma ba i." Tana so ta shiga wajansa kamar yadda Jidda ta ce amma
Chapter 82 · 0% Book details