← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 205

Sashe 31

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce, au ashe ma ranar zata zo kenan?. Jidda ta harareta cikin jin haushi ta ce, nufin ki a haka zaki are kenan?. Nayla tana dariya ta ce, ni dai bana wannan tunanin Twiny, ni na san da wa nake tare. Ko waye shi sai dain bamu so kama shi ba wallahi, shi in banza Jidda ta fa a cike da jin haushi. Nayla dai dariya take yi ta bu e misk in ta ce, Kamar kin san nawa na barshi a Kaduna, bani dashi a na ko ka an. Kuma na manta shaf ban siya ba wallahi. Ke dai Allah ya barki da baby, ya fito mana da unborn lafiya. Ta amsa da amin Nayla ta bu e turaren ta ce, Akwai hamshi kam sosai wallahi. Yana da da i gaskiya, shiyasa bana sakawa na fita nima a gida nake amfani dashi. Nayla ta ce, mu kam gwara mu shafa mu fita in, a nan in amfanin uban me zai min?. Jidda ta ce, kedai Allah ya ba mu lafiya. Suka yi dariya a tare suka cigaba da hira har aka yi i sha sannan Jidda ta wuce gida. Ranar juma a su Abiy suka dawo, kamar yadda Mama ta ce Kano in ta shigo ita da Yaya J. Sai da daddare suka zo gidan Nayla. Da zumu i ta bu ofar ta rungume Mama tana murna. A falo suka zauna Mama ta bita da kallo bayan sun gaisa ta ce, Nayla babu wata damuwa dai ko?. Nayla ta ce, Babu komai Mama. Mama ta ce, kar fa ki oye min damuwarki, in kina ganin baza ki iya fa a min a gaban Jawad ba sai ya bamu waje. Nayla ta yi dariya tana kallon Yaya J ta ce, babu komai Mama, in akwai zan fa a miki. Mama ba haka ta so ji ba, bata so ta ji ta ce lafiya lau ko babu komai, damuwa ko tashin hankali kawai take da bu atar ji daga bakin Nayla. Jin abinda Nayla take fa a sai ta sharebata nuna mata ba ta bata tsarabar da ta siyo mata. Jawad ma ya bata tsaraba harda McDonald fried chicken in da suka yi da ita, ai kam ta ji da i sosai sai muryar take yi ta ga babarta da yayanta. Bayan fitar Jawad yana jiran Mama a mota Mama ta kalle ta ta ce, Nayla zo nan. Nayla ta dawo kusa da ita ta zauna ta ri e hannunta ta ce, Kin tabbatar dai babu matsala?. Nayla ta ce, babu Mama. Kina so ki ce ya kar e ki matsayin matar sa? Har ha in da yake kansa na aure yana sauke miki ko ya ya?. Nayla sai ta ji maganar ta yi mata nauyi sosai, ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Mama ta ce, ba kunya zaki ji ba, fa a min zaki yi, ai ba ajiya aka kawo masa ke ba. Nayla a sanyaye ta ce, Mama ki yarda babu wata damuwa. Baki amsa min ba ai, yana sauke miki ha in ki da yake kansa?. A ta aice ma ke da shi kun zama mata da mijin na gaske?. Nayla ta rasa abinda zata ce, ta rasa wacce amsa zata bawa Mama dan wallahi kunya take ji. Baza ta iya ce mata eh ba dan ta san arya take yi, sannan bazata iya cewa a a ba saboda kunyar da take ji. Mama ta ce, bai faru ba, Ina kallon idanunki na san bai faru ba, kuma ki ce min babu matsala Nayla? Gaskiya zan samu Abiy a raba auren nan kawai. Nayla a sanyaye ta ce, a Mama, Abiy har yanzu yana fushi dani, ki bari a kwana biyu ba yanzu ba. Mama daman abinda so kenan sai ta ce, ai shikenan. Allah ya kyauta, ki cigaba da ha uri komai zai wuce. Mama ki gaishe da Abiy, Na yi kewar sa sosai, har yanzu bai bani umarnin zuwa Kaduna ba ko?. Bai bayar ba Nayla. Ki gaishe shi. Bara na kawo sa o ki kai masa Mama ta fa a tana shigowa ciki da sauri amma ta bita da kallo tana ta e baki. Ba jimawa fito ta bawa Mama sa on ta kar a tana cewa, Abiy an gatan Nayla, ya gode sosai. Tare suka fito har mota ta raka Mama sannan ta koma ciki zuciyarta cike da kawar an gidan su. Abiy yana zaune ranar asabar da safe shida Jawad suna duba littafi wanda suke rubuta duk abinda ya shafi kasuwancin su musmaman wanda suka bawa kaya. Mama ce ta shigo da sallama hannunta auke da abinda Nayla ta bata ta araso ta zauna ta ce, barkan ku da aiki. Suka amsa kafin Mama ta ce, Abiy ga sa o jiya Nayla ta ce na baka ta fa a tana ajjiye masa. ewa ya yi ya yi karo da ananun cincin irin wanda yake so har take yi masa da tana gidan. Murmushi ya yi yana kallon cincin in cikin kewarta ya ce, na gode ya fa a yana rufewa ya cigaba da abinda yake yi. Mama ta sauke numfashi ta ce, Abiy haka za a bar Nayla a cikin wannan yanayin da take ciki? Wata biyu da kenan da tarewar ta amma babu cigaba tana nan a rame har yanzu. Dan tana sonsa ai ba hakan yana nufin zamu yaleta a halaka ba. Jawad ya kalli Mama jin abinda ta ce, dan shi kam bai ga alamun damuwa a tare da ita ba. Abiy ya yi shiru bai ce komai ba Mama ta ce, Duk da ta oye min damuwarta ta ce babu komai amma ni uwa ce zan iya fahimtar damuwarta ta ko wacce fuska. Nayla tana cikin damuwa, mijin nan nata bai auke ta a bakin komai ba, itace take dakon sonsa na wahala wanda bazai amfane ta ba. Yarinya gaba aya tayi ashin wuya, ba dan da kayan abinci aka kaita ba da ina jin ko abinci bazai dinga bata ba. Jawad da mamaki ya ce, Mama azumi fa aka gama, ga azumi ga aiki ai dole ta rame. Mama ta kalle shi ta ce, tun kafin azumin ai a rame ta ke, tunda ya shigo rayuwarta shikenan komai ya lalace, farin cikin gidan nan gaba aya ya tarwatse. Ni na gaji kawai a raba auren nan. Abiy ya sauke numfashi ya kalle ta ya ce, Zeenatu meyasa baki ta a fa ar alkhairi akan auren nan na Nayla ba? Ko yaushe cikin kushewa ki ke bayan ke kika bata goyan bayan aurensa?. Gaban Mama ya fa i ta kalli Abiy da yake kallonta ta ce, bana fa ar alkhairi fa ka ce?. Eh haka na ce. In aka ga arna shiru ake yi ba ya ata ake zuwa a yi ba, a matsayin ki na uwa a gareta sai ki cigaba da yi mata addu a tunda kin shaida tana son mijinta. Ni kar ki sake samu na da irin wannan batun, bana so. Mama ta ce, Yanzu inda mahaifiyarta ce ai baza ka ce mata haka. Kullum da tunanin Nayla nake kwana nake tashi, kullum tunanina ya take me yake faruwa da ita wacce irin rayuwa take yi a gidan. Damuwa da ita ne ya saka make yawan maganarta ba dan bana fa ar alkhairi akan aurenta ba. Ka bashi auren ta ba tare da ko sisi ba, ta tare ka ce kar ta zo maka gida sai ka neme ta, ka san yadda Nayla take da ulafucin aunarka ko iya wannan bazai saka ta rama ba?. Ga shi bata da wani matsayi a wajan mijin nata, ya jingine ta a gefe kamar ba matar sunna ba. Ni bazan iya jure ganin Nayla a wannan hali ba gaskiya, sai dai ka ce bana fa ar alkhairi amma bazan iya ba tana fa a ta tashi ta fita daga falon. Abiy ya kalli Jawad ya ce, kai ka ga alamun wani abu a tare da Nayla?. Wallahi Abiy ban gani ba, rayuwarta ke yi da walwala kamar tana cikin gidan nan. Inda tana da damuwa ko a fuska za a gani, damuwar ta bai wuce har yanzu kana fushi da ita ba. Abiy ya ce, magana ta are, cigaba da lissafin. Suka cigaba da abinda suke yi. Mama da ta koma aki ita kanta ta kasa nutsuwa, ba haka taso ta ga Nayla ba, taso ta ganta cikin damuwa sosai amma sai ta ga akasin haka. Taso ta je ta ga Omar ya yi mata dukan tsiya sai taga babu alamun koda cizon sauro a jikinta balle alamun duka, taso ta je ta ga fuskarta a kumubure, fatar jikinta a yayyake amma sai ta ga kyau da yalli ma fatar take yi. Gashi yanzu Abiy ya fara zargin bata fa ar alkhairi, tunda ya fara fa ar hakan kenan ya kar i auren na su hannu biyu. Ba yanzu take so ya amince da auren ba, ko da zai amince tafin so sai Nayla tasha ba ar wahala a hannun Omar, amma yanzu tun ba a je ko ina ba ya fara fa ar haka dole ta damu. Zagaye take yi tana tunanin ya zama dole ta samo mafitar da Nayla zata sha wahala sannan Abiy ya sake tsanar auren, sai ta yi hakan burinta zai cika, a yanzu abinda yake faruwa ba shi take so ba. Mum da Dad da Najwa sun dira Texas saboda yadda hankalin su ya kasa kwanciya a kan Narma. Sun je estate in da suka san suna nan amma basa gidan. Hankalin Mum ya sake tashi da yar Dad ya lalla a suka koma inda suka sauka. Bayan sun koma Mum cike da damuwa ta kalli Dad ta ce, ni wallahi jikina yana bani wani abun ya samu Narma, ka kira Ashraf in mu ji suna ina. Dad bai musa ba ya kira Ashraf whatsApp call, Ashraf bai fahimci Dad yana America ba tunda whatsApp call ne ya saka shi ya auki wayar. Yana auka Dad ya ce, Ashraf kuna ina ne? Ga mu a estate in da ku ke amma gidan babu kowa. irjin Ashraf ya buga ya kalli Narma da take kallon sa ya ce, Eh Dad, mun canja estate ne. Turo min location in yanzu. Okay Dad
Chapter 31 · 0% Book details