Sashe 203
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Marmerh, Marmerh? Ko wanne laifi ki ce Marhmerh, ko yaushe itace take yi miki abin duka sauran basa yi. Musliha ko Mufty basa yin laifin dukan ne sai ita?" Ya fa a cikin fa a sosai yana kallon ta. Nayla ta ago ido ta kalle sa suka ha a ido, ta girgiza kai tana binsa da kallo mamaki da ba in ciki fuskarta babu walwala ko ka an, acin rai ya mamaye fuskarta gaba aya ta ce, "Ohhh kana fa a min bana dukan wan anda na haifa sai wacce bani na haifa ko?." Shiru ya yi bai amsa ba yana kallon ta, Nayla ta ce, "ashe akwai ranar da zaka ce ina nuna banbanci tsakanin su? Ashe akwai ranar da zaka nuna min na fifita an da na haifa akan Marmerh? Ashe akwai ranar da zaka ce indai aka yi laifi Marmerh nake cewa tayi saboda ba ni na haifeta ba?. Ashe daman kallon da ka ke yi min kenan, kallona ka ke yi matsayin wacce take nuna banbanci a tsakanin su ko?." "Kinga Jidda, ni ba haka nake nufi ba, kar yi deflecting maganta. Ina...." Ta katse sa a fusace cikin acin rai ta ce, "oh deflecting maganarka ma nayi kenan ko? Cewa ka yi meyasa ko yaushe ita nake duka bana dukan sauran, cewa kayi ko yaushe ita nake cewa tayi min laifi bana cewa sauran sun yi min. Kana nufin ina banbanta Marmerh da ana, ina zaluntarta tunda ba ni na haifeta ba. Kai tsaye kace min bana tausayin ta, daman ta ya za a yi na ji tausayinta tunda ban ji zafi a lokacin haihuwarta ba?......" ta an girgiza kai ta ce, "Haka ka ke nufi, haka maganar ka take nufi babu zancen deflecting" ta fa a tana kallon sa cikin acin ran da taji yana mamaye mata zuciyarta. Zai sake magana ta hana sa, cikin murya mai sauti dake nuna acin ran da take ciki ta ce, "Ka kyauta, na gode sa sakamakon da na samu daga gare ka. Amma ina so ka san abu aya, wallahi Indai baza a saka Marmerh kuka ba, indai duk duk abinda tayi sai dai a yale a zuba mata ido saboda tsoron kar ta yi kuka zaka lalata mata tarbiyya, zata tashi babu kwa a babu wanda zai fa a mata ta ji. Al awarin da ka yiwa mahaifinta akan zaka bata tarbiyya zai bi rariya, sannan Didi baza ta yi alfahari da ri eta da ka yi ba wallahi." "Nima na tashi babu uwa, yadda ake tsawatar min ana saka ni kuka ya saka na tashi da tarbiyyar da har nake bawa ana irinta a yanzu. Indai a haka rayuwar Marmerh zata tafi nan gaba zaka yi danasani, domin har kai in baza ka ta a iya sarrafata ba wallahi. Ice tun yana anye ake tan wara sa, in ya bushe sai dai a saka gatari a sara sa bazai ta a tan waruwa ba. Kuma ka yi ha uri, ni na auka ina ri e Marmerh daidai da yadda nake ri e Musliha, na auka itama kamar ata take zan iya yi mata hukuncin da nake so, hukuncin da nake ganin shine zai taimaki tarbiyyarta yanzu da nan gaba. Ashe ba haka abin yake ba, ashe ita daban su Musliha daban. Na auka yadda take ce min Mummy na zama mahaifiyarta, tunda yanzu ni ta sani matsayin uwa a gareta. Amma tunda kana ganin ina nuna banbanci a tsakaninsu ka yi ha uri, bazan sake yi mata fa a ba balle har na daketa ta zubar da hawayen da zaka ji zafin zubarsu a zuciyarka. Tunda baka so na daina in sha Allah, zan yiwa ana dana haifa hukuncin da nake so, tunda su ni na haifesu ko a wuta na saka su na ona kowa ya san nawa ne, ni na sha wahalar haihuwarsu ba wani ba, babu wandai tuhume akan meyasa nayi hakan. Ita kuma tunda ar Yayarka ce ba Yayata ba bazan sake yin abinda zai sakata kuka ba, fa a akan tayi ba daidai ba bazan sake yi mata ba balle har tayi kuka, in sha Allah bazan kuma ba" tana gama fa ar haka ta tashi ta bar masa wajan ranta a ace sosai. Omar ya bita da kallo har ta ace, sai zuciyarsa ta karye ya ji babu da i ko ka an, shi ba da wani abun ya fa a ba wallahi, itace ta fassara zuwa haka. Ta ya zai ce tana nuna banbanci bayan sai ta hana Musliha abu ta bawa Marmerh? Ai bai yi mata adalci ba, kuma sai Allah ya tsayar dasu ya saka mata indai har ya ce tana nuna banbanci. Duk wanda ya tambaye ta cewa take anta hu u duk ita ta haife su, bata ta a cire Marmerh cikin anta ba, in ta fa a kuma yarda ake yi saboda Marmerh da Didi take kama, Didi kuma jinin Omar ce. Ajiyar zuciya ya yi cikin rashin jin da i, daga yadda take magana ya san ta fusata sosai. Ya mi e a sanyaye ri e da Muhsin ya fita daga falon. Bai shiga inda take ba dan yana so ta huce sai ya bata ha uri, dan yaga ta yi fushi. Nana Haleema 09030398006. P131 Sai gab da lokacin sallar magrib ya shiga kitchen ya same ta a tsaye tana aiki, ya jima a tsaye a bayanta yana kallon ta zuciyarsa babu da i akan abinda ya yi mata. Ya sauke ajiyar zuciya arasa inda take a sanyaye ya ce, "Ashiq!." Juyowa tayi ta kalle sa taga yana takowa inda take. Gefenta ta kalla sai ta auke kai ta cigaba da abinda take yi. Omar ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce, "i'm sorry Jidda." Matsowa yake inda take a hankali yana taku kamar mai san a. Ganin ya kusa tarar da ita sai ta auki wu ar da take gefenta ta nuna sa ta ce, "kar ka matso kusa dani, ka ja baya kar ka zo inda nake." Omar ya zuba mata ido yana kallon ta yana cigaba da matsawa kusa da ita a hankali bai dakata ba. Nayla rai a ace take nuna sa da wu a ta ce, "kar ka zo inda nake, kar ka sake ka araso, wallahi in kazo inda nake zan yanke ka da wu ar nan." Omar ya aga hannu sama alamun surrender, Calmly ya ce, "Indai abinda ki ke so kenan ki yi Jidda, indai shigar wu ar nan jikina ki ke da bu ata ki aikata kawai indai zaki huce" ya fa a yana matsowa kusa da ita sosai. Idonta yana rufe suke gam, da gaske bata son ganin fuskarsa ko ka an, muryar tasa ma a dole take shiga kunnenta ba dan tana so ba. Baya take yi yana matsowa har ta kai arshe ta jingina da cabinet, har lokacin bata daina nuna sa da wu a ba ta ce, "Ka daina matsowa inda nake, wallahi soke ka. Ka bar kitchen in nan, ka fita bana son ganinka!." Omar ya wara idanu ya ce, "bakya son ganina Jidda?..." sai kuma ya ce, "Ni kuma Ina son ganinki Jiddana, ki soke ni kawai indai zaki wuce ki yi, kin ji!" Ya fa a a tausashe yana kallon fuskarta da idanunta suke a rufe. Ganin ta kasa yin komai sai idanunta da suke a rufe gam, sai ya kai hannu zai ri e ta firgita ta kamar wacce wuta zata ta a ta ce, "kar ka ta a ni, kar hannunka yazo jikina." Hannu biyu ya sake agawa sama yana kallonta ya ce, "bazan ta a ki ba, kin ga hannuna yana sama." "Ka fita daga wajan nan bana son jin muryarka, bana so na bu e idona na ganka, kar hannunka yazo inda nake, bana so ka ta a ni, don Allah ka fita." "Ba ta a ki zanyi ba Ashiq, tunda bakya so bazan ta a ki ba" ya furta a cikin sanyi yana kallonta. Nayla ta fashe da kuka mai sauti, ya an yi aramin tsaki cikin sigar rarrashi da kwantar da murya ya ce, "kin ce in na matso kusa dake sai kin soke ni da wu a, kin ce bakya so na ta a ki, kuma gashi kina kuka. Ta ya zan iya jure wannan uhum! Ta ya zan iya jure ina tsaye kina kuka Jidda?. Dole na ta a ki Ashiq, i'm sorry, bazan iya ganin kina kuka na yaleki ba. In caka min wu ar zai saka ki huce ki yi Ashiq....." ya fa a yana saka hannunsa guda aya ya zaga dashi ugunta, ya jawota jikinsa da arfi ya ha a jikinsu waje Kiciniyar wace kanta take yi ya hanata saboda ri eta da ya yi, ya zare wu ar hannunta ya ajjiye ya matse ta sosai a jikinsa ta yarda baza ta iya watar kanta ba. Ya kai bakinsa kusa da kunnenta yana sauke mata numfashia hankali, kafin ya ziea harshensa a kunneta ya an juya ka an, sannan ya yiwa kunnen kiss kana ya ce, "I'm sorry, i'm sorry Ashiq, bazan sake ba, ki yafe min ba haka nake nufi ba. Ki yi ha uri jidda, ki yi ha uri Ashiq!" Ya fa a cikin salon rarrashi yana sake matseta a jikinsa sosai. Kuka take yi sosai a irjinsa cikin zafin kalamansa, tunawa da kalamansa a kanta sai ta cigaba da son wace jikinta shi kuma ya i bata wannan damar. Cikin kuka mai arfi ta ce, "Ka sake ni, ka sake ni!." "A'a bazan iya ba, ina son na jiki a jikina! Ina so ki zubar da hawayen da na zama silar zubarsu a irjina. I'm sorry, bazan sake fa ar abinda nace ba, ki yi ha uri Jidda" ya fa a yana an sassauta ri on da ya yi mata. "Ni bana so! Ka cika ni!" Ta fa a da arfi tana wance jikinta daga nasa tana harararsa. Omar ganin hararar da take aiko masa sai ya sake motsawa zai kamo ta ya ce, "Jid..." ai kafin ya arasa ta fita daga kitchen in tana kuka ta barsa a wajan a tsaye. Kai ya dafe cikin rashin mafita, gaba aya nadamar kalamansa ta kama sa, shi bai fa a da