Sashe 81
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dashi an aura masa aure da Nayla. Hajja ta ce, "Ashe kun je Kaduna, hakan ya yi kyau Allah ya ara mu ku zaman lafiya." Dukkan su suka amsa da amin kafin ya mi e ya ce, "sai anjima." Hajja ta ce. "To Ummaru na gode sosai." Bai ce komai ba ya fita. Salma ta daki a bayanta Nayla ta ce, "Sai da ke tawan, na rantse da girman Allah gayen nan ya kamu. Ke ni ai ban san haka yake ba sai yanzu, wai daman haka kyaunsa yake fitowa in ya yi murmushi?." Nayla ta harari Salma, sai kuwa ta sake yin dariya ta ce, "Nayla kishi ko?." Murmushi ta yi Hajja ta ce, "Ni wallahi daman na san auren ku da Omar ba mai rabuwa ba ne ba, da aka ce kun je Kaduna sai na ji da i na kuma jinjina hankalin Omar in, dan da ban auka yana da hankali da hangen nesa na yin abinda ya yi ba gaskiya." Nayla ta ce, "Hajja ko ni ban san can zamu je ba sai ganina nayi a gidan, kuma Abiy ya san da zuwan mu." Hajja ta ce, "ya yi ari, yanzu ko babu komai kuna zaune da albarkar mahaifinki. Allah ya ara mu ku zaman lafiya." Suka amsa da amin ita da Salma kafin Hajja ta ce, "tashi ki je ku tafi, naga har yanzu shegen halin na sa dai yana nan." Nayla ta yi murmushi kawai suka yi sallama Salma ta rakota amma baya ofar gidan. Salma ta ce, "na san yana gidansu, ki shiga ni kam na koma. Sai na zo na sha labari, ke wai har yanzu ba a wuce wajan ba? Duk wannan soyayyar ta ido ce babu wani bayani?." Nayla ta harareta ta ce, "akan Jawad." Salma ta ce, "ai ni da shi baza mu auki wannan lokacin muna kallon juna ba, da wuri kowa zai san ya an uwansa yake." "Baki da kunya wallahi." "Eh na ji, Gaskiya zan yiwa Jidda waya mu samo makaman ya in da zamu ya i Omar kawai a wuce wajan." "Ban nema ba, dalla koma gida" ta fa a tana wuce ta tana dariya ita kuma ta koma ciki. KRB3P046 Arewabook@nanahaleema11. Gidan ta shiga da sallama ya amsa yana fitowa daga falon ya ce, "har kin gama?." Nayla ta ce, "eh." Ta fa a tana kallon tsakar gidan abinda ya faru a kwanakin baya yana dawowa zuciyarta. Bangon da ya rits ta da wu a ta kalla tayi murmushi ta ce, "A nan wajan ka ora min wu a a wuyana, na ga tashin hankali a ranar." Abinda bata ta a gani yayi ba yayi, dariya taga yana yi sosai har ta waiwayo tana kallonsa duk da gidan babu haske. Suna ha a ido ya tsayar da dariyar bai ce komai ba sai da ya araso inda take ya ce, "mu je." Mamakin abinda ya bashi dariya haka take yia haka suka fito suka nufi komawa gida kamar azu. Shi ya bu e gidan ta shiga ya biyo bayanta kamar jira ake ta shiga aka kira wayarta. Bata auka ba ta wuce aki ta canja kaya zuwa na bacci ta fito falon aka sake kiran wayar a karo na uku kenan. auka ta yi kawai sai ta saka a speaker ta yi sallama ta ji muryar namiji ya amsa. Bata kowa komai a ranta ba ta ce, "Waye yake magana?." Daga wayar aka ce, "Hawwa Najib ne, your colleague." Gaban Nayla ya fa i ganin Omar a tsaye a kanta, sai ta an ru e ka an, amma gudun kar ya kawo wani abun a zuciyarsa sai ta ce, "Najib ya aiki?" Ta fa a tana kallon Omar da yake tsaye har lokacin. Daga wayar ya ce, "fine. I hope kwana biyu kina lafiya, baki zuwa aiki na tambaya an ce kin auki hutu, i hope everything is going well?." Nayla kasa bashi amsa tayi saboda kallon da Omar yake mata, gashi ya dawo kan kujera ya zauna zuba mata ido yana kallo. Sai ta yanke wayar da sauri ta kashe ta gaba aya, ya zuba mata ido na wani lokaci yana jin zuciyarsa kamar zata fio waje saboda kishi. Shiru ya ratsa falon na wani lokaci kanta yana asa irjinta yana bugawa sosai, kallon da yake mata ka ai ta san ta yi laifi ko bai fa a ba. Kanta yana sunkuye ta ji ya ce," daga ranar da abokin aiki ya sauke ki a mota na fara jin zafi a zuciyata, ban auki abin da mahimamci sosai ba amma na kasa oyewa har sai da na yi miki magana. A lokacin da naji Didi tana yi miki maganar samarinki shima na kasa oyewa sai da nayi magana, wani ya biyo ki ya ce yana sonki na kasa oyewa shima na yi magana. Da na fahimci da jikinki ake yin talla na ji tashin hankali da acin ran da ban ta a jin irin shi ba a duniya, wani abu mai kama da yaji naji yana mamaye idanuna da zuciyata. Duk a lokcin ban san kishi nake ba, ban san haka ake jin kishi ba shiyasa ban fahimta ba sai da aka fa a min. Yanzu da na sani na tabbatar da zafinsa, na tabbatar da ra i da unar da kishi yake dashi. Ban ga laifin masu illata mutane akan kishi ba, ban ga laifin masu raunata kansu akan kishi ba, ban ga laifin ba su kashe kan su akan kishi ba, domin abinda na ji a zuciyata in aka ce zan iya zama sanadin ta uwar lafiyar wani bazan yi musu ba." Shiru ta ji ya yi kafin ta ji ya ce, "Jidda!." Gabanta ya fa i sosai, ta ago a hankali ta ce, "Na'am." "Raina aurena da yake kan ki ka yi ne?. Abokin aikinki ya dawo da ke daga wajan aiki saboda baki da lafiya, na san lokacin zaki ce ai ba sonki nake yi ba amma matata ce ke. Abokin aikinki ya kira ki muna tafiya Kaduna, har kina cewa kin gode da kulawa, abokin aikinki ya kira ki yanzu yana tambayar lafiya bakya zuwa aiki, Jidda auren ne bashi da mahimmaci ko ni ne bani da mahimamcin?." Nayla a sanyaye ta girgiza kai ta ce, "ba haka nake nufi....." a tsawace ya ce, "to ya ki ke nufi? In ba rashin mahimamcin ba meye wannan? Raini ko kuma iyayya ce!?." Yadda ya yi maganar da tsawa ya saka ta zabura sosai,dan ya dawo mata asalin wanda ta sani. Tsawar ta ratsata, domin kwana biyu ta saba da yadda yake yi mata magana babu tsawa balle tsoratarwa. Sanin baya so ayi masa shiru sai ta ce, "Ba haka bane ba wallahi, ba abinda ka ke tunani ba ne." "In ba haka bane meye? Amsa min... meye in ba raini da rashin bawa auren mahimmmaci ba?. Dan kin raina min hankali a gabana ma? Ko dan kin ga ina sonki ne ya saka ki ke tunanin zaki iya komai a gabana?." Shiru ta yi bata amsa ba, a firgice ya ce, "Ina tambayar kin yi min shiru, sa'anki ne ni!?." Nayla ta fara hawaye tana girgiza kai, ya nuna ta da yatsa ya ce, "in ki ka bari hawayen nan ya sake sakkowa mai raba ni dake sai Allah." Cak ta tsayar da kukan tana jan numfashi a hankali, ya runtse idanu yana jin wutar kishi tana ruruwa a zuciyarsa. Wai matarsa ce take amsa kiran wayar wani abokin aikinta a gabansa. Ji yake kamar ana gasa masa zuciya, ji yake ra in gashin yana zaga jininsa yana kaiwa har walwarsa. Nayla ta ce, "Don Allah ka yi ha uri, bazan sake ba." "kenan raina ni in ki ka yi, kin auki aurena bashi da mahimmaci a gare ki shiyasa ki ke aikata hakan a gabana ko nauyi na bakya ji. Waya fa har sau biyu a gaban idanuna, kin kyauta" ya fa a cikin tsantsar acin rai da yanayi na fushi ya tashi ya bar mata wajan. Nayla ta ri e ha a ta ce, "Na shiga uku, ni wallahi ban auka ina sane ba, kuma ban shine ya kira ni ba, naji tsoron kar na auka a gabansa ya yi tunanin wani abun ne. Yanzu ya zan yi?" Ta fa a tana hawaye. Abinda yake aga mata hankali znacensa rainin da ya ce da rashin sanin mahimmacin aurensa da yake fa a, shine bata so. Tsoro zuwa tayi masa magana take yi dan ta san halinsa, yadda ya birkice yana buga mata tsawa ta san in ta je yanzu hargitsewa zai sake yi. Hankalinta ya tashi, gashi bata so ya cigaba da tunanin abinda ya fa a haka ne. Shawarar zuwa ta bashi ha uri ta yi koda zai zane ta, da wannan tunanin ta mi e ta nufi da in a arare ta shiga. Yana tsaye ya bu e taga yana kallo harabar gidan, kai da ka ganshi ka san yana cikin acin rai sosai, dan har fuskarsa ta komaja. Nayla ta taka a hankali ta ce, "Ka yi ha uri YaMar, abinda ka ke fa a ba haka ba ne. Wallahi ban raina ka ba, kuma wallahi ina daraja aurena, ina bashi mahimmaci sosai. Kuma ni ban ta a waya dasu ba sai a cikin kwanakin nan, amma don Allah ka yi ha uri." Kallon ta ya yi da jajayen idanunsa, yadda idanunsa suka yi ja ya bata tsoro dan fuskarsa ma gaba aya ta canja kamar ba shi ba. Nayla ta sake asa da murya cewa, "Ka yi ha uri, ka yi ha uri don Allah. Ban san number waye ba shiyasa na auka a ranar da mu ka je Kaduna, yau ma ban san lambar ba shiyasa na auka. Don Allah ka yafe min ka daina fushi da ni." Nan ma bai ce mata komai ba ko kallon inda take ma bai yi ba. Batu na gaskiya ciwo yake ji a zuciyarsa, zafi da rada i da kuma kishi da tashin hankali yake ji yana mamaye masa ko ina na jikinsa shiyasa ya i kulata, dan shirun shine alkhairi. A hankali ta tako zuwa inda yake a tsorace dan umarnin zuciyarta take bi tazo inda yake. Ta ja numfashi ta ce, "Ka yi