Sashe 101
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saboda kai nake zuwa Kano, saboda kawai na ganka YaMar!" Ta fa a tana kuka sosai. ago ido ya yi yana kallon ta, ganin yadda take kuka sai ya share mata hawaye da hannunsa, kafin ya yi magana ta ce, "Ko lokacin auren mu ni na aureka ne saboda ina so, duk abinda ya dinga faruwa a gidan nan ban ta a jin na daina sonka ba. Ko wacce rana, ko wanne awa, ko wanne minti, ko wanne second, ban ta a jin na daina sonka ba, sonka ko yaushe aruwa yake a zuciyata. Wallahi kalaman Mama ba haka bane, itama ta san ina sonka tamkar raina, ina sonka sosai, akan sonka zan iya mutuwa YaMar, ka yarda dani, kar kalaman Mama su yi tasiri a zuciyarka don Allah!. Itama ban dalilinta na fa ar haka ba, amma itace mai goya min baya akan auren mu. Wata ila tana gwada ka ne dan ta tabbatar kana sona ko baka sona. Amma ka yi ha uri, kar ka ri e maganar da ta fa a a ranka. Mamana ce, tana son duk abinda nake so, ta san ina sonka, itama kuma tana sonka!." Lokaci guda duk wani acin rai da yake damun zuciyarsa ya ji gaba aya ya gushe, ya zuba mata ido yana kallonta, bai gaji da jin yadda take furta tana sonsa ba shiyasa bai ce mata komai ba ya yi shiru yana jira ta cigaba da magana. Nayla ta tsagaita kukan da take yi ta ce, "ban ta a cewa bana jin da in zama da kai ba, ban san a ina Mama ta samo kalaman nan ba, amma ka yi ha uri wata ila wani abun ne ya ata mata rai, dan Mama itace mutum na farko da ta fara bani goyan baya akan aurenka. Uwata ce, haihuwata ce kawai Mama bata yi ba, amma duk wani farin cikin da a yake samu wajan mahaifiya Mama ta bani shi. Ganina da ta ke yi ina yawan shiga damuwa a kanka ta amince ta jure acin ran Abiy saboda farin cikina. Ka yi ha uri, kuma ka daina cewa bana sonka, na so ka tun kafin ka so ni, na tabbatar ina yi maka son da baka yi min shi....." Akan la anta ya ora yatsansa yana kallon cikin idanunta yana hango zallar gaskiya a kalamanta. Ya zuba mata ido yana kallon idanunta da suka canja launi zuwa jajaye saboda kuka, ya lumshe ido ya bu Cikin sanyin murya ya ce, "Shiii! Kar na sake ji kin fa i kalmar kina yi min son da bana yi miki. Kin san adadin son da nake miki kuwa Jidda? Kin san yadda zuciyata take bugawa akanki a ko wanne lokaci?. Hmmm! Da kin sani da baki ce haka ba, son da ki ke min bai taka kara ya karya ba akan wanda nake yi miki, kar ki yi sa o wajan fa ar wannan kalmar......babban zunubi ne Jidda!" Ya arasa fa a muryarsa a can asa yana kallon idonta tare da bu e idonsa a cikin nata. Nayla ta ja numfashi tana kallonsa ta ce, "Na yi ciwo ta sanadin son da nake maka, na kwanta a asibiti saboda tunaninka. Ina ganin ina wahalar da kaina ne saboda na san bazaka so ni ba, sannan a lokacin kana son Narma baza ka ta a kallona ba, sannan kuma ka tsane ni kana jin haushina. Tunanin hakan shine yake haifar min da ciwon da an gidanmu suka kasa gane kaina. Lokacin da ka ke a Abuja na kusa yin accident da mota saboda damuwata a wanne hali ka ke ciki, duk yadda zan fa a maka how much you means to me you will never understand wallahi, abu aya na sani....wallahi ina sonka!" Ta fa a murya na rawa sosai, bakinta sai kar kar kar yake yi saboda rawar da yake yi. Bakinsa ya ora akan nata, ya an yi kissing ka an kafin ya cire yana kallon ta ya zuba mata ido yana kallon ta tana hawaye. Nayla ta ja numfashi jin bai yi magana ba sai take tunanin har lokacin kalaman Mama basu bar zuciyarsa ba. A sanyaye ta ce, "Zan iya sadaukar da komai saboda kai YaMar....a kan sonka zan iya mutuwa Rouhii!." Da zafin nama ya rungumeta, ta shiga jikinsa sosai ta matse shi a jikinta tana ji kamar za a wace mata shi. Jikinta har rawa yake yi ta rasa yadda zata sarrafa shi a jikinta, tana ji kamar runguma bata yi mata ba, ji take kamar ba a jikinsa take ba. Sai da ta auki lokaci a jikinsa tana sauke nunfashi sannan ya ce, "Ni zuwan Mama ma ya yi min amfani, ko babu komai na ji sirrin zuciyar matata, ki fa awa Mama gobe ta dawo, ta dawo ta ga son da Omar yake yiwa arta, zata tabbatar da Omar yana son Nayla soyayyar da zata sakata farin ciki da alfahari" ya furta idanunsa lumshe yana jin yadda ta ri e shi sosai, shima sai ya ri eta da kyau yana jin buguwar zuciyarta a irjinsa. Bata motsa ba sai lumshe ido da tayi tana sake gyara kwanciya a jikinsa. Murya a asan ma ogwaro ya ce, "Wai tsananin auna ce in aka cewa mutum za a iya mutuwa a kan son da ake masa?..." ta ji ya tambaya amma bata amsa ba dan nutsuwa take so ta lalubowa kanta. Ya yi ar dariya sannan ya agota daga jikinsa, ya ri e fuskarta yana kallon idanunta ya ce, "To Jidda in ki ka mutu akan son da ki ke yi min ta ya soyayyar zata amfane mu bayan bakya nan?, kin tafi kin bar ni, wata ila na yi rayuwa da wata sai abin tuna ki ya zo sannan zan tuna duk da tsananin son da ki ke yi min. A ganina ba mutuwarki nake da bu ata soyayyata ta yi miki ba, zan fi bu atar ingantacciyar rayuwarki, mu rayu a inuwa aya, mu yi hira, mu yi fa a, mu shirya, mu ci abinci tare, mu je duk inda mu ke so tare, mu haifi yara, mu basu tarbiyya a tare da ke. Na baki farin ciki na hana ki ba in ciki, na mayar dake gimbiya wacce ta fi sarauniya iya sarauta, na soki, na mayar dake aljannata kuma duniyata. Yin hakan tare dani shine arshen tanadin auna da soyayya a gare ni da samun ta tare dake Jidda! Hakan ne zai amfane mu ni da ke amma ba ta hanyar rasa ki ba Jidda....." "Ya an numfashi mai aukar hankali, ya lumshe ido ya bu e akan idanunta ya ce, "Cikar aunar da nake miki ba mutuwa ba ce Ashiq, tanadar miki da lokacina da kuma soyayyata a gare ki shine cikar soyayyar da nake miki, na sadaukar miki da kaina da rayuwata shine asalin abinda ake kira auna. Mu inganta rayuwar mu dan morar juna shine soyayya ba mutuwa ba. Mutuwa ai sau i ne da ita ta, in Allah ya yi nufinta kamar a bu e ido a rufe ne har an gama. Amma rayuwa itace mai wahala, itace zaka tashi yau ka kuma tashi gobe, ba tare da ka san me zai faru da kai ba. Inganta rayuwarki da baki farin ciki shine asalin auna Ashiq, in ki ka mutu kuma wa zan bawa Jiddana!?" Ya arasa fa a yana kallon idanunta tare da murmushi kamar yadda take kallon kallonsa tunda ya fara magana. Kalamansa sun gama kashe ta, ta zuba masa ido tana kallo dan ita bata auka haka ya iya kalamai masu kyau da saka farin ciki ba sai da suka fara rayuwar farin ciki dashi. Tana yabawa da hikimar da take cikin kalamansa sosai, tana yabawa da azancin da yake dashi musamman a kalaman yanzun nan. Duk da maganar ta sa sai ya ga dama, kalaman sun gama tafiya da ita bata san ta sake komawa jikinsa ta kwanta ba. "I love you so much YaMar!." Ya lumshe idanunsa ya furta, "I love you Jidda!. Oh ashe fa ni bahaushe ne, ina sonki Jida!" ya fa a yana sake mayar da ita jikinsa tana murmushi jin abinda ya ce. "Kar na sake ji kin ce zaki iya mutuwa akan son da ki ke min, ki ce zaki iya rayuwa dani akan son da ki ke yi min Jidda. Kuma ina so ki san ba ke kika fara sona ba ni na fara sonki, na fara sonki tun a ranar da na ku utar dake daga hannun wa annan an iskan, a lokacin naji abinda ban ta a ji ba a zuciyata, amma bazan fahimta ba saboda ina ji da tantiranci da uruciya. Na yi dakon sonki na sama da shekara goma, na rayu da sonki, zan kuma mutu dashi, zan tashi dashi. Ina so na mori soyayyarki har a aljanna Ashiq. A cikin son da nake miki ka an ki ka auka kina yi min, kamar a saka aramin cokali ne a ebi shinkafa a cikin buhunta. Baki san yadda Allah ya saka min ke a zuciyata ba ne shiyasa ki ke tunanin na ki ya fi nawa. Hmmm! Na ki bai wuce ruwa a kan farcen jariri ba." Murmushi take yi cikin farin ciki da jin da i da kuma walwala. Ta kasa oye farin cikinta kamar yadda ya kasa oye nasa sai murmushi suke yiwa junansu. Omar ya an sassauta ri on da ya yi mata, ya saka hannu aljanu ya auko wata aramar jaka ya bu e jakar ya fito da red colour ring cover ya bu e, zoben gold ne a ciki, ya auko ya kama yatsanta na kusa da na arshe ya saka mata. Kiss ya yiwa hannun nata yana murza yatsan ka an ya ce, "komai aka baki kyau yake yi miki Ashiq, ya haska hannunki sosai, sai na rasa gane ke ce kike yi masa kyau ko shi yake miki kyau?......" ya fa a yana kallonta. Gira ya aga mata ya ce, "Kyautar farko daga wajan mijinki kuma masoyinki Omar, ina fatan zaki so ta har cikin ranki" Nayla ta kalli zoben tana shafa shi, bashi da girma sosai amma a ido ka san yana da tsada dan nauyinsa zai kai four to five grams. Nayla ta